𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mace ce ta ke da miji, yana son yin sallar dare, da azumin
nafila, kuma mutane suna mutunta shi, amma matsalarshi dai: Idan ya samu ’yar
walwala yana shan giya kuma yana kallon fina-finan batsa. Ta sha yi masa magana
a kan haka, wani lokaci ma har kuka yake yi, amma duk da haka ya kasa dainawa,
musamman in ya shiga ban-ɗaki.
Matar har addu’a take yi kar Allaah ya ba shi arziƙi don ba ta san abin da
zai yi ba a gaba.
Wace shawara malam zai bai wa wannan matar da kuma mazaje
masu ƙuntata
wa matansu a kan irin wannan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Idan dai haka maganar ta ke, cewa: Mijin yana sallar dare
kuma yana azumin nafila, amma kuma yana shan giya da kallon fina-finan batsa
idan ya samu hali, to a nan abin da zan ce shi ne: A cigaba da yi masa addu’a
da roƙon
Allaah Ta’aala ya
shirye shi, ya sa ya fi ƙarfin zuciyarsa da shaiɗaninsa.
Matar ta cigaba da yi masa bayani cikin hikima da kyakkyawar
wa’azi, kar ta gaji. Ta jawo hankalinsa ga ya daina barin irin waɗanan fina-finan a cikin
wayarsa da komfutarsa, kuma ya daina abota da masu wannan harkar ta kallon irin
wannan hoton ko mashaya giyar, ya daina bi ta layi ko wurin da ake sayar da
fana-finan da giyar, kuma ya daina ajiye duk wani abin da zai tuna masa
al’amarinta, kamar kwalabenta da hotunata da fina-finan da ke nuna yadda ake
shan giyar da masu nuna hotunan tsairaicin da sauransu.
Yanzu zai ji daɗi
’ya’yansa su tashi su gan shi yana aikata irin wannan aikin, kuma zai so a ce
sun yi koyi da shi a kan haka? Sannan kuma yaya zai ji idan aka fara yi musu
gori cewa: Ubansu mashayi ne, ko mazinaci ko dai wani abu irin wannan?
Ta yi haƙuri ta cigaba da zama da shi tana yi masa
wa’azi. Na lura: Akwai
alamar alkhairi a tare da shi, tun da har kuka yakan yi in tana yi masa
maganar.
Addu’ar: Kar Allaah ya ba shi arziƙi, ba daidai ba ne.
Maimakon haka ta yi addu’ar:
Allaah ya ba shi arziƙi mai amfani a duniya da lahira. Annabi (Sallal Laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam) yana yawaita yin wannan addu’ar:
رَبَّنَآ
ءَاتِنَا فِي الدُّنْيَا حَسَنَةً ، وَفِي ألْآخِرَةِ حَسَنَةً ، وَقِنَا عَذَابَ النَّارِ
Ya Ubangijinmu! Ka ba mu kyakkyawa a duniya, kuma kyakkyawa
a lahira, kuma ka tsare mu daga azabar wuta.
Ta yawaita yi wa kanta da shi kansa wannan addu’ar.
Allaah ya taimake mu.
WALLAHU A'ALAM
Shaikh Muhammad Abdullah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.