Ticker

Mijina Baya Sallah, Ko Zan Iya Neman Ya Sake Ni?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam wata mata ce take son a faɗa mata hukuncin zama da mijinta da bai damu da Sallah ba, ko da kuwa lokacin Ramadana ne, sannan kuma yana tilasta mata ya sadu da ita a lokacin watan Ramadana da rana, bayan haka yana saduwa da ita tana jinin haila, kuma ta faɗa masa haramun ne amma yaƙi ya daina. Shin Malam za ta iya neman saki tunda baya bin dokokin Allah ko taci gaba da zama dashi?

𝐀𝐌𝐒��❗️

To, 'yar'uwa mutukar an yi masa nasiha bai bari ba, to za ki iya neman saki, saboda duk wadda baya Sallah kafiri ne a zance mafi inganci, kamar yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya faɗa a hadisin da Muslim ya rawaito mai lamba (81), gashi kuma aya ta (10) a Suratul Mumtahanah ta tabbatar da rashin halaccin Musulma ga kafiri, kinga ci gaba da zamanku akwai matsala a addinance.

Allah ya hana saduwa da mace mai haila a Suratul Bakara aya ta 222

وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ قُلْ هُوَ أَذًى فَاعْتَزِلُوا النِّسَاءَ فِي الْمَحِيضِ وَلَا تَقْرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطْهُرْنَ فَإِذَا تَطَهَّرْنَ فَأْتُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ أَمَرَكُمُ اللَّهُ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ التَّوَّابِينَ وَيُحِبُّ الْمُتَطَهِّرِينَ 

Kuma suna tambayar ka game da haila Ka ce: Shi cuta ne. Saboda haka ku nisanci mata a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su sai sun yi tsarki. To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku. Lalle ne Allah Yana son masu tuba kuma Yana son masu tsarkakwa. (Suratul Bakara aya ta 222).

Saduwa da mace da rana a Ramadana babban zunubi ne kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba (616) ya tabbatar da hakan. Zunubin barin Sallah shi kaɗai ya isa ya raba aure, mutukar mijin bai tuba ba.

Idan har bai sake ki ba, za ki iya kai shi kotu, Alkali ya raba ku.

 Duba Al-minhajj na Nawawy 2/69.

Allah ne mafi sani.

Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments