𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Yanzu rabon da mijina ya
kwanta da ni shekara guda da watannin uku kenan, wai saboda ina ‘bleaching’
kuma ina da ƙyasfi, wanda kuma ya ƙi nema mini magani. To shin akwai aure a
tsakaninmu ko babu?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Ƙwarai kuwa, baiwar Allaah! Akwai aure a tsakaninku mana.
Ai duk auren da aka ɗaura
shi a bisa ƙa’idoji
da dokokin Musulunci ba ya mutuwa haka siddan sai in an kashe shi. Ma’ana: Har sai in shi mijinki
da kansa ya fito ƙarara ya ce ya sake ki, ko kuma sai in ke da kanki kin rabu da
shi ta hanyar ba shi khul’i,
ko kuma idan magana ta kai gaban alƙali, kuma ya bincika sannan ya gano akwai
cutarwa a tsakaninku ko a addini idan aka bar ku kuka cigaba da zama. Daga nan
ne shi ma yana iya sanya ƙarfin matsayinsa ya kashe auren ya raba tsakaninku.
Don haka, idan har kina ganin ba za ki iya haƙurin
cigaba da zama da shi ba saboda wannan cutarwar, to Shari’a ta ba ki daman ki kai
maganar gaba: Da farko dai ga iyayensa, in kuma ba a samu biyan buƙata
ba sai ga iyayenki. Idan sun kasa warware matsalar, to kina iya wucewa zuwa
wurin alƙali,
amma tare da izininsu. A nan ne shi alƙali zai yi cikakken bincike mai zurfi a
kan matsalar kuma ya gano gaskiyar da’awarki,
daga nan kuma ya fitar miki da haƙƙinki.
Kodayake ‘bleaching’ saɓon
Allaah ne, amma kuma shari’a ba ta bai wa mijinki daman ya ƙaurace
miki na tsawon shekara saboda kin yi wannan saɓon
ba, haka kuma ko domin kina da ƙyasfi a fatar jikinki ba. Domin iyakan
tsawon lokacin da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ƙaurace
wa iyalansa don ladabtarwa shi ne wata guda kaɗai.
Amma har tsawon shekara, wannan abin da ya yi ya ci karo da maganar Allaah Maɗaukakin Sarki da ya ce
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا
لَا يَحِلُّ لَكُمْ أَن تَرِثُوا النِّسَاءَ كَرْهًا وَلَا تَعْضُلُوهُنَّ لِتَذْهَبُوا
بِبَعْضِ مَا آتَيْتُمُوهُنَّ إِلَّا أَن يَأْتِينَ بِفَاحِشَةٍ مُّبَيِّنَةٍ وَعَاشِرُوهُنَّ
بِالْمَعْرُوفِ فَإِن كَرِهْتُمُوهُنَّ فَعَسَىٰ أَن تَكْرَهُوا شَيْئًا وَيَجْعَلَ
اللَّهُ فِيهِ خَيْرًا كَثِيرًا
Ya Ku waɗanda
suka yi ĩmãni! Bã ya halatta a gare ku, ku gãji mãtã a kan tĩlas kuma kadaku
hana su aure dõmin ku tafi da sãshen abin da kuka ba su, fãce idan suka zo da
wata alfãsha bayyananniya kuma ku yi zamantakẽwa da su da alhẽri sa'an nan idan kun ƙĩ su, to akwai tsammãnin ku ƙi
wani abu alhãli kuwa
Allah Ya sanya wani alhẽri mai yawa a cikinsa. (Surah An-Nisaa’: 19).
Don haka, abin ya ke wajibi a kan mai irin wannan abin shi
ne ya tuba ga Allaah Ubangijin Halittu kuma ya komo ga sauke haƙƙoƙinsa
dangane da matar aurensa.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.