Nau'ukan Kunu Da Yadda Ake Sarrafa Su (Kunun Koko, Kunun Zogale, Kunun Alkama, Kunun Acca, Kunun Gyada)

    Gabatarwa

    A babi na goma sha biyar (15) an kawo bayanai kan kunun gargajiya da nau’o’insa. Akwai nau’o’in kunu da dama da ba su sauya ba har ya zuwa yau; sakamakon ‘yan bambance-bambancen da ake samu ba su taka kara sun karya ba. Misali, kunun gero da ake kira kunun tsaki, yana nan yadda aka san shi a gargajiyance. Sai dai a yau ana iya sanya masa wasu nau’ukan kayan Æ™amshi da babu su a gargajiyance. A wannan babi, za a iya lura da cewa, ba a kawo wasu daga cikin nau’o’in kunun da ake samu yau a Æ™asar Hausa ba. An yi haka ne domin guje wa maimaicin nau’o’in kunun da aka tattauna a Æ™arÆ™ashin babi na goma sha biyar.

    Kunun Kamu (Kunun Koko)

    i. Barkono (tonka) 

    ii. Citta  

    iii. Gero 

     iv. Kanunfari

    v. Kimba   

    vi. Madara 

    vii. Ruwa  

    viii. Suga

    Yayin samar da kunun kamu (kunun koko), akan surfe gero a bushe a wanke (wani lokaci ma akan haÉ—a geron da masara kaÉ—an). Za a jiÆ™a wannan gero kuma a bar shi har sai ya kwana, sannan sai a kai markaÉ—e bayan an sanya masa kayan yaji nau’in barkono da citta da kanamfari da sauransu. Bayan an dawo da shi daga markaÉ—e, za a Æ™ara masa ruwa, sannan a yi amfani da matata a tace shi sarai, sannan sai a ajiye shi domin ya kwanta.

    Bayan ya kwanta, za a samu abin da ake kira kamu; fari mai laushi. Da wannan kamu ne ake dama kunu. Hanyar da ake bi domin dama shi daidai yake da wanda aka yi bayani a sama.

     Kunun Zogale

    i. Gero

    ii. Kayan yaji

    iii. Ruwa

    iv. Zogale

    Wannan kunun yana kama da sauran kunu da aka yi bayanin su sama. Bambancin shi ne, yayin tafasa ruwan kunun, ana sanya zogale a tafasa su tare. Sannan ana iya sanya zogalen cikin gero yayin da za a kai niÆ™an gumba, wato dai a niÆ™o su tare. Wannan nau’i na kunu na kasancewa É—auke da Æ™amshi da kuma É—anÉ—anon zogale. Masana na ba da shawarar amfani da shi domin taimakon da zogale ke yi ga lafiyar É—an Adam.

    Kunun Alkama

    i. Alkama  

    ii. Aya  

    iii. Citta

    iv. Kanamfari  

    v. Madara 

    vi. Masoro

    vii. Nono  

    viii. Ruwa  

    ix. Suga 

    x. Zuma

    Da farko, za a surfe alkama a wanke ta sannan a shanya. Kafin a kai niƙa, za a ɗebi wani adadi na alkamar a jiye gefe guda (amma ajiyewar ba dole ba ne). A ɓangare ɗaya kuma, za a ɗauko aya a wanke a shanya. Bayan duka sun bushe, sai a haɗa alkamar da ayar sannan a kai niƙa. Bayan an dawo da su daga niƙa, za a tankaɗe, sannan a ƙwaɓa garin da ruwan sanyi. Daga nan za a tafasa ruwa sai a sanya cikin wannan gumba. Za a iya sanya masa lemon tsami da suga da madara.

    Idan har an ajiye ragowar alkama kafin a kai niƙa, to za a sanya ruwa cikin tukunya daidai gwargwado sai a sanya tsakin tankaɗen da aka yi. Za a yi ta gaurayawa bisa wuta har sai ya haɗe ya yi kauri. Bayan an sauƙe sai a sanya ragowar alkama da aka adana ciki sannan a mayar da su cikin tukunya a yi ta juyawa. Akan zuba shi cikin kunun bayan an dama.

    Kunun Zaki

    i. Dankali  

    ii. Gero   

    iii. Kayan ƙamshi

    iv. Kwakwa 

     v. Lemon tsami 

    vi. Ruwa   

    vii. Suga

    Kunun zaƙi na kama da kunun koko ta fuskar yadda ake sarrafa su, sai dai sun ɗan bambanta. Yayin samar da kunun zaƙi, ba a ajiye tataccen markaɗe domin ya zama kamu. A maimakon haka, da zarar an tace, sai a ɗebi wani adadi a matsayin gasara a ajiye gefe guda. Sauran kuwa za a zuba musu ruwan zafi kamar dai yadda ake kunun koko. Yanayinsa zai kasance da ruwa-ruwa amma ba kamar na kunun koko ba. Yayin da aka zuba wannan gasara a ciki (wadda ita ma tana da yawa), sai ya dawo ruwa-ruwa sosai.

    Kunun Acca

    i. Acca

    ii. Ruwa

    iii. Suga

    iv. Tsamiya

    Shi ma kunun acca na kama da sauran nau’o’in kunu da aka yi bayani a sama. Bambancin kawai shi ne, bayan an dawo da niÆ™an accar an tankaÉ—e, to ana Æ™waÉ“a garin ne da ruwan tsamiya. Da ma dai ita acca ba a surfe ta. Ana wanke ta ne kawai a shanya kafin a kai niÆ™a.

    Kunun GyaÉ—a

    i. GyaÉ—

    ii. Kayan Æ™amshi 

    iii. Lemon tsami

    iv. Madara 

    v. Ruwa  

    vi. Shinkafa  

    vii. Suga

    Da farko, akan gyara gyaÉ—a sannan a jiÆ™a ta. A gefe guda kuma, za a wanke shinkafa kaÉ—an (amma za a yi la’akari da adadin gyaÉ—ar da yawan kunun da ake son yi) ita ma sai a jiÆ™a ta. Bayan sun jiÆ™a, za a haÉ—a su a kai markaÉ—e. Za a sanya kayan Æ™amshi kafin a kai niÆ™a. Da zarar an dawo da shi daga markaÉ—en, sai a yi amfani da matata domin tacewa. Bayan an tace, sai batun damawa da ruwan zafi. Ba dole ne a tanadi gasara ba a wannan nau’i na kunu. Idan an kammala dama kunun, ana iya sanya masa lemon tsami da madara. Suga kuwa da ma, “farilla ne tusar mai bacci.”

    Kammalawa

    Duk da cewa Bahaushe na da salon maganar da ya gina labari da shi da ke faÉ—in: “Kunu abincin mutane uku ne; da tsoho da yaro da marar lafiya,” a nan za mu ce wannan labarin Æ™anzon kurege ne. Dalili kuwa shi ne, kunu nau’i ne na abin sha da ake ta’ammuli da shi sosai a Æ™asar Hausa. Za a tabbatar da haka ko ta la’akari da nau’o’in kunu daban-daban da aka tattauna a sama, waÉ—anda kuma duka akan same su a Æ™asar Hausa. 

    Citation (Manazartar Littafin):  Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

    Get a copy:
    To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
    +2348133529736

    You can also write an email to:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.