Ticker

6/recent/ticker-posts

Samosa, Shawarma, Kuli-Kuli, Kosan Wake, Kosan Rogo, Kosen Doya, Kosen Dankali Da Nama, Soyayyen Dankali

Wannan rubutu ya kawo bayani game da yadda ake yin samosa da shawarma da ƙuli-ƙuli da ƙosen wake da ƙosen rogo da ƙosen doya da ƙosen dankali da nama da kuma soyayyen dankali da ƙwai.

Samosa

Kayan haɗin da za a tanada:

i. Albasa

ii. Attarugu

iii. Fulawa

iv.  Gishiri

v. Kon filebo

vi. Kori

vii. Magi

viii. Nama

ix. Ruwa

Za a daka ɗanyen nama wanda ba shi da kitse, sannan a soya sama-sama tare da kori da magi. A gefe guda kuma, za a yi jajjagen kayan miya , musamman albasa  da attarugu sannan a soya sama-sama a jiye gefe guda. Daga nan za a kwaɓa fulawa tare da gishiri kaɗan da kuma kwan filebo. Da zarar wannan  ya samu sai a aza firayin fan bisa wuta . Za a riƙa shafa wannan kwaɓaɓɓ iyar a fulawa cikin firayin fan ɗin. Da zarar an saka, zai kame jikinsa ya zama lafe-lafe.

Daga nan za a ɗauko kayan miyan da aka soya sama-sama da kuma nama, a riƙa sanyawa cikin wannan  fulawar da aka ɗan gasa. Za a riƙa nannaɗewa daidai irin tsarin da ake so. Bayan an kamala, sai a barbaɗa  filawa a sama. Sai maganar soyawa a cikin mai.

Shawarma

Kayan haɗin da za a tanada:

i. Bota

ii. Fulawa

iii. Kabeji

iv. Karas

v. Naman kaza

vi. Ruwa

vii. Suga

viii. Tumatur

ix. Yis

A haɗa fulawa da bota da yis da kuma suga kaɗan, sai a kwaɓa su da ruwan ɗumi. Ana son kwaɓin ya yi ɗ an ruwa-ruwa. Bayan an kammala kwaɓin, sai a ajiye shi domin ya kumburo. A ɓ angare guda kuma, za a ɗauko kabeji da karas da tumatur a yanka. Fulawar da ke gefe kuwa, za a ɗauko ta a riƙa gutsura ta daidai gwargwado ana faɗaɗawa. Sai a riƙa sanya ta cikin firayin fan kamar yadda aka yi wa ta samosa.

A gefe guda kuwa, za a tafasa nama, sannan a soya shi tare da kayan lambun da aka riga aka yanka. Bayan sun soyu sama-sama, sai a riƙa zubawa a cikin fulawar da aka yi bekin a riƙa naɗewa. Bayan an daɗe, za a sake mayar da shi domin bekin. Idan akwai obun, to za a sanya a ciki. Idan babu kuwa, za a iya amfani da firayin fan wanda ba ya kamawa.

Ƙuli-Ƙuli

Kayan haɗin da za a tanada:

a. Gyaɗa

b. Kayan yaji

c. Man gyaɗa

d. Ruwa

Za a soya gyaɗa  a murje a fece, sannan a saka kayan yaji a ciki a kai markaɗe. Bayan an markaɗo, za a sanya cikin turmi  ko roba sannan a sanya taɓarya ko muciya a yi ta juyawa har sai mai ya fito. Za a riƙa yi ana kwashe man da ya taru. Sannan akan ɗan ƙara ruwa kafin mai ya fara fitowa domin a ji sauƙin juyawa.

Bayan an kammala wannan , sai a ɗora bisa dutsen matsa domin a ƙara matse man da ke cikin tunkuzar. Daga nan ne kuma za a riƙa yanka ana mulmulawa, sai kuma a ri ƙ a gutsuttsurawa ƙanana-ƙanana kuma ana curawa.Waɗannan curarrun ne za a riƙa sanyawa cikin mai domin suya.

Ƙosen Wake

Kayan haɗin da za a tanada:

a. Albasa

b. Gishiri

c. Kayan yaji

d. Magi

e. Mai

f. Ruwa

g. Tarugu

h. Tattasai

i. Wake

Za a jiƙa wake , sannan a surfe  a wanke  a cire hancinsa. Daga nan za a jiƙa shi a ruwa har sai ya jima, sannan a tsane a regaye ƙasar da za ta iya kasancewa a ciki. Daga nan za a gyara tarugu da tattasai da albasa  a yanka a sama. Za a iya sanya tafarnuwa idan ana buƙata.

Daga nan sai a kai shi markaɗe, sai dai ba a son a tsananta ruwa sosai wurin markaɗen. Saboda haka ne ma ake zuwa da ƙaramin kwano (mazubi) domin a tare ruwan wanke  injin. Bayan an dawo da shi, sai a sanya gishiri da magi da sauran kayan ƙamshi da ake buƙatar sawa, ana iya yanka ganyen  albasa  ciki, sannan sai a juya shi ƙwarai. Bayan wannan  ya samu, sai batun aza mai a saman wuta . Za a riƙa ɗiba da ƙaramin ludayi ko wani cokali mai faɗi ana zubawa cikin mai. Idan gefe guda ya soyu, sai a juya zuwa ɗaya gefen.

Ƙosen Rogo

Kayan haɗin da za a tanada:

a. Albasa

b. Gishiri

c. Magi

d. Rogo

e. Ruwa

f. Tarugu

Za a niƙa rogo  a tankaɗe, sannan a kwaɓe shi da ruwan ɗumi, sai a saka gishiri da magi da albasa  da tarugu waɗanda aka jajjaga. Daga nan za a riƙa dunƙulawa daidai yadda ake buƙata ana soyawa da mai.

Ƙosen Doya

Kayan haɗin da za a tanada:

i. Albasa

ii. Doya

iii. Fulawa

iv. Kwai

v. Madarar ruwa

vi. Magi

vii.  Mai

viii. Ruwa

ix. Tarugu

Za a fere  doya a wanke  ta sosai, sai a markaɗa ta da bilanda har sai ta yi laushi. Kada a sanya ruwa sosai yayin wannan  markaɗe. Bayan an kamala, sai a sanya fulawa da madar ruwa da kuma ƙwai. Sannan za a sanya jajjagen tarugu da albasa  a juya su sosai. Idan ya juyu, zai kasance mai kauri. Daga nan sai a a fara soyawa cikin mangyaɗa.

Ƙosan Dankali Da Nama

Kayan haɗin da za a tanada:

i. Albasa

ii. Attarugu

iii. Dankali

iv. Fulawa

v. Gishiri

vi. Magi

vii. Man gyaɗa

viii. Nama

ix. Ƙwai

x. Ruwa

Za a wanke  nama a tafasa, sai a sanya magi da gishiri da albasa  a markaɗe tare da attarugu da albasa sannan a juye a kwano. Sai kuma a ɗauko dankalin turawa a tafasa shi ya yi laushi, sannan a farfasa shi cikin kwano. Daga nan za a zuba naman ciki. Bayan nan sai a zuba fulawa a ciki a saka gishiri da magi a juya sosai har su haɗe. Sai a ɗora mai a kan wuta  a riƙa ɗiba ana soyawa.

Soyayyen Dankali Turbuɗe Cikin Ƙwai

Kayan haɗin da za a tanada:

i. Albasa

ii. Dankalin Turawa

iii. Gishiri

iv. Kayan yaji

v. Magi

vi. Man gyaɗa

vii. Ƙwai

viii. Ruwa

ix. Tarugu

x. Tattasai

Da farko za a samu dankalin a wanke  shi a fere , sai a sake wankewa karo na biyu. Sai a yayyanka shi tsattsaye a aje shi gefe guda. Daga nan za a dafa shi sama-sama, kar a bar shi ya nune sosai. Idan an sauke za a tace da kwando. Daga nan sai a jajjaga tattasai da tarugu a saka kayan yaji a ciki da ɗan magi da gishiri, sai a fashe ƙwai tare da kayan jajjagen a ciki. Kada a saka magi fari ko yaji su yi yawa. Za a sanya su ne daidai gwargwado. Daga nan sai a kawo dankalin nan a zuba a cikin ƙwan, sai a ri ƙ a ɗiba ana soyawa tare da ruwan ƙwan nan a hankali. idan sun soyu, za su ri ƙ a ha ɗ ewa wuri ɗ aya.

Citation (Manazartar Littafin):   Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments