Ticker

Sha'awa Ta Zo Min Alhalin Ina Da Alwala

TAMBAYA (69)

Dan ALLAH ya ingancin alwalar wanda yake da alwala sai yaji sha,awa?

AMSA

Sha'awa halittace wadda tana zuwa silar gani, ji ko tunanin wani abu wanda ido, kunne ko qwaqwalwa suke so. Yayinda gabobi suke taimaka musu wajen cimma muradinsu. Tsoron Allah SWT ko biyewa Qarin (Aljanin da kowa yake tare dashi) sune suke sa; ko dai ka aiwatarda aikin sha'awar ta hanyar da ta dace a shari'ance (aure) ko kuma ka bi son zuciyarka (nafs) tareda taimakon hudubar shaidan (hawa) wajen aikata zina da dangoginta

Silar hakanne Allah SWT yace kada ku kusanci zina;

( وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا )

الإسراء (32) Al-Israa

"Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfasha ce kuma ta munana ga zama hanya"

Bawai ma aikatawa ba, kusantar ta, saboda Allah SWT ne ya halicci sha'awa wanda tana bayyanuwane silar halittun adrenaline don bani Adam suyi aiki da ita a shari'ance bawai a dabi'ance ba

Mafita akan hakan shi ne koyi da hadisin da Annabi SAW ya ce: "Yaku taron matasa kuyi aure, wanda bai samu damar hakan ba sai yayi azumi"

(Bukhari da Muslim)

Don haka hukuncin wanda yake da alwala kuma sai yaji sha'awa ta baibayeshi, zaiyi isti'adha ne (Auzubillahi Minash Shaidanir Rajim), domin kuwa daga shaidan ne, idan wani abu ya fita a jikinsa kamar irinsu; maniy, maziy ko wadiy, to anan alwalarsa ta baci amman idan ba abinda ya fita a jikinsa to alwalarsa tana nan kuma zaiyi sallah da ita, in sha Allahu

A karkashin haka ga wasu shawarwari guda 3;

1) Idan zaka fara kabbarar harama (takbir) sai ka karanta azkar dinnan;

"Allahu Akbar kabira, walhamdulillahi khasira, wa subhanallahi bukratan wa asila"

(Duba littafin Sifatu Salatin Naby na Shaikh Muhammad Nasiriddin Albany, Rahimahullah)

2) Ka dinga karanta addu'ar da Annabi SAW ya shawarci wani sahabi; "Allahummagfir zambi, wadahhir qalbi, wa hassin farji"

Ma'ana: "Ya Allah ka yafemin zunubbaina, ka tsarkake zuciyata, ka kiyaye farji na"

(Hisnul Muslim)

3) Sannan kuma a shawarce idan kana da dama sai kayi aure. Kamar yanda yazo a hadisin da ya gabata

Wallahu ta'ala a'alam

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments