TAMBAYA (56)❓
Assalamu alaikum wa rahmatullah. Barka da wannan lokaci
Mallam. Ya ayyuka, Allah yayi jagora ya Bada Lada Aamim. Mallam ba tambaya
nikeda ita ba face Neman shawara, ni budurwace ansaka bikina Nanda wata Daya.
Ina bukatan shawarwari zaman aure dareda addu'oin dazan kare aurena na kare
mijina sannan na kare yarana idan Allah ya bani. Nagode Allah ya Kara basira
AMSA❗
Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuhum
To yar uwa, ina roqon Allah yayi miki albarka
Sannan ina roqon Allah ya baki zaman lafiya dangane da zaman
ibadar da zakiyi
Allah SWT yace;
( وَمِنْ
آيَاتِهِ أَنْ خَلَقَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَاجًا لِّتَسْكُنُوا إِلَيْهَا
وَجَعَلَ بَيْنَكُم مَّوَدَّةً وَرَحْمَةً ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ
يَتَفَكَّرُونَ )
الروم
(21) Ar-Room
Kuma akwai daga ãyõyinsa, Ya halitta muku mãtan aure daga
kanku, dõmin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya sõyayya da rahama a
tsakãninku. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin tunãni.
Haqiqa dukkan aure idan babu nutsuwa, soyayya da rahama to
akwai lam'a a tattare da ma'auratan. Ana samun wadannan ababe 3 ne kadai idan
aka yi koyi da yanda Annabi SAW ya mu'amalanci iyalansa
Shawarar da zan baki anan itace; na farko dai ki ji tsoron
Allah SWT, na biyu kuma ki qudurce a ranki cewar wannan aure da za ki yi akwai
daruruwa ko ince dubunnai gwauraye maza da mata wadanda suke ta neman irin
wannan damar amman Allah bai ba su ba, ga shi ke a yau kin samu
Na uku, akwai wasu littattafai na addini guda 3 wadanda zan
so ace kin karanta su a cikin nan da kwanaki 30 dinnan, kafin ki tare a dakin
mijinki
Sanin kanki ne cewar komai da zamu aikata saida musulunci ya
koyar da mu, hatta shiga bandaki to ina kuma ga rayuwar auratayya wanda wallahu
a'alamu a nan ne za'a samu shugaban kasa ko gwamnan gobe wanda zai jagoranci
miliyoyin al'umma. Kinga kenan komai zaki gudanar sai an koma ga hadisai da
suka yi bayani akan yanda Annabi SAW ya koyar da matan gidansa a lokacin
rayuwarsa tare dasu
Littafi na farko shine;
1) Sifatu Salatin Naby PDF (Siffar yanda Annabi SAW yayi
sallah, wallafar Shaikh Muhammad Nasiriddin Albany (Rahimahullah)
Ya suffanta tare da kawo bayanai daki-daki akan yanda Annabi
SAW ya koyar da yanda ake sallah dogaro da hujjar hadisin "Sallu kama
ra'ayta muni usalli" bi ma'ana: "Kuyi sallah kamar yanda kuka ga ina
yi". Don haka ya zama dole ki mallaki wannan littafin kuma ki koyi sallah
irin yanda Annabi SAW ya koyar. Kamar yanda kika sani cewar kowa yana cikin
dayan biyu ne: immadai kana sallah ne a al'adance (kamar yanda ka taso ka ga
ana yi) ko kuma kana sallah ne a addinance (yanda Ma'aiki SAW ya koyar)
2) Guidelines to intimacy in islam (Shiriya akan alaqar
auratayya a musulunce, wallafar Mufti Ahmad Ibn Adam Alkautary)
Yayi bayani sosai kuma daki-daki akan yanda Annabi SAW ya
koyar da al'ummarsa yanda ake rayuwar auratayya. Akwai makarantun da ake
koyarda rayuwar zamantakewar aure a addinance irin makarantar: ZADUZAUJJEN. Ana
koyarda (1) Yadda ake neman Aure a muslinci (2) Sanin Hakkin muji (3) Shagwaba
ga miji ki mayar dashi kamar Jariri (4) Koyan Halayen da miji zai maida ke
madubin sa ya zame miki kamar rakumi da akala (5) A koya Miki Yadda mahaifansa
da Danginsa zasu Soki Babu Boka ba Malam (6) iya Tattalin Miji da Dukiyar sa da
kuma Abubuwa masu matukar Amfani Sannan
ki zama Abin Alfahari mijinki duk bazaki San su ba sai kinje Zaduzaujjen.
Registration: N4,000. Karkashin jagorancin Shaikh Prof. Umar Sani Fagge.
Makarantar MANARU ISLAMIYYA FAGGE SPECIAL PRIMARY SCHOOL IBRAHIM TAIWO ROAD.
(Kamar yanda naga sanarwan a group di na cewar program din na tsawon watanni 3
ne)
3) Newborn baby guide (Shiriya ga Jarirai, wallafar Ibn
al-Qayyim Aljauziyya (Rahimahullah)
Ya rubuta littafinne a matsayin kyauta ga qanwarsa a lokacin
da ba shi da ko da riga daya da zai bata a matsayin tukwici a lokacin da ta
haihu, sai gashi Allah SWT ya albarka littafin ga shi muna amfana dashi. Yayi
bayanai akan yiwa jariri kiran sallah, sakawa jariri suna, yin aski, kaciya,
yanka da sauran bayanai dai da hujja a Qur'ani da sahihan hadisai, kai abin sai
wanda ya karanta dai
Sai kuma ki bawa angonnaki shawarar ya dafa goshinki da
hannun dama sannan ya karanta addu'ar nan da Annabi SAW yace: Idan dayanku ya
auri mace, ko ya sayi bawa mai hidima, sai ya ce;
اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا، وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا
عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا، وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ.
Allahumma innee as-aluka khayraha wakhayra ma jabaltaha
'alayh, wa-a'oothu bika min sharriha washarri ma jabaltaha 'alayh.
"Ya Allah ina rokon Ka laherinta da alhrin da Ka
dabi'antar da ita a kansa, kuma ina neman sarinka daga sharrinta da shaarrin Da
ka dabi'antar da ita a kansa"
Sai kuma addu'ar da kike bida game da yaya idan Allah SWT ya
azurtaki da samu anan gaba
Amman abinda ya tabbata shine; an rawaito cewar Annabi SAW
yana yiwa jikokinsa wato Hassan da Hussaini bin Ali (Allah ya kara musu yarda
baki daya) wadda ta tabbata a cikin sahihan hadisai, kamar yanda Shaikh Sa'id
Alqataani (Rahimahullah) ya kawo a cikin littafinsa na Hisnul Muslim (Asaka
mawallafin littafin a addu'a domin kuwa a watanni baya ya koma ga MahaliccinSa)
Inda yace: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi, ya kasance yana nema wa Hassan da Husain tsari da wannan addu'ar
(Harma yace babanku {Annabi Ibrahim AS} yana yiwa yayansa {Annabi Ismail da
Ishaq} ga addu'ar kamar haka
أُعِيذُكُمَا
بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّة، مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ، وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ
لاَمَّةٍ.
"O'eezukuma bikalimatil-lahit-tammah, min kulli
shaytanin wahammah, wamin kulli 'aynin lammah"
Bi ma'ana: "Ina neman muku tsari da kalmomin Allah
cikakku daga dukkan shaidan da wata dabba mai dafi, da kuma dukkan wani mai
kambun baka, mai cutarwa"
(Duba Sahihul Bukhari hadisi mai lambata 3371)
Sannan kuma kamar dai yanda na fada kwanaki tun ran gini tun
ran zance, akan yi tuya a manta da albasa ma'ana mutane sukan manta da addu'ar
da Annabi SAW ya koyar kafin tarawa da iyali, wadda rashin yinta kan iya kawo
yiwuwar a haifi yaro kangararre ya zo ya dameku ya dami al'umma da shaidanci
domin kuwa sakacin rashin neman tsarin Allah ne daman yasa shaidan kan shafi
abinda Allah ya azurta ma'aurata tunma kafin a haifi yaron, (ananma kamata yayi
ki shawarci angon ya haddace ta) addu'ar itace kamar haka
بِسْمِ
اللهِ اللّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا.
"Bismil-lah, allahumma jannibnash-shaytan,
wajannibish-shaytana ma razaqtana"
Ma'anarta: "Da sunan Allah. Ya Allah! Ka nisantar da
shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da shaidan daga abin da Ka azurta mu da
shi"
Addu'ar tana cikin Sahihul Bukhari tareda Fathul Bari 4/181,
harma Shaykh Pantami yace ba abin mamaki bane idan kaga shaidanin yaro a wannan
zamanin, kana bin salsala zakagano iyayensa basuyi waccan addu'ar bane
Don haka wadannan sune wasu daga cikin sahihan addu'u'o'in
da suka inganta daga Ma'aiki SAW. Kuma naga ya dace na baki shawarar domin kuwa
Annabi SAW yace: addu'a itace takobin mumini (Kamar yanda hakan ya zo a Sahihul
Bukhari)
Ina roqon Allah ya bamu ikon fahimtar addini dakuma aiwatar
dashi, ya Allah ka tabbatardamu bisa tafarkin magabata na qwarai (Salafus
salih)
Allah ya baki zaman lafiya a gidan mijinki, Allah ya kauda
fitina, Allah yasa zamanki dashi ya zamo alkhairi tun anan duniyar har zuwa can
lahira. Allah yasa ya shayar dake Zanjabeel daga tafkin Salsalbeel a Aljannatil
Firdous
Wadanda suke singles (gwauraye), Allah ya basu abokan zama
nagari
Wallahu ta'ala aalam
Subhanakallahumma, wabi hamdika, ash-hadu anla'ilaha illa
anta, astaghfiruka, wa'atubi ilayk
Amsawa;
Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.