Ticker

    Loading......

Shin Maniyyi Yana Iya Fitowa Silar Tunanin Saurayi

TAMBAYA (90)

Aslm. Malam don Allah misali kamar ace inyi tunani cewa cikin mazan da ke Sona wanga Zan aure bani auren wanga sai inyi tayin tunani azucciyata Tom misali maniyyi 🙈🙈Yana iya zubomin innayyi wannan tunani, sai nayi wanka

AMSA

To yar uwa banda abinki ai daman sha'awa ce kinsan kowa da irin karfin sha'awar sa

Zata iya yiwuwa idan kikai wannan tunanin a samu fitar, maniyyi ko kuma maziyyi

Kinsan kowa da irin halittarsa akan hakan

Idan kinga Maniyyi to wanka ya wajabta akanki. Dole zakiyi wanka, ko zubar sa silar tunani ne, ko aiki (saduwar aure ko wasa da gaba) ko kuma ma a mafarki

Wankan janaba kawai zakiyi ko Sifatu Kamala ko Sifatu Jaza'. Idan kuma maziyyi ne to anan wanke gabanki zakiyi gaba daya

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments