TAMBAYA (64)❓
Menene gaskiya dangane da batun da ake cewa mu yan Nigeria
ba Ka'aba kai tsaye muke kallo ba yayin sallah ?
AMSA❗
Alhamdulillah
A binciken da Shaikh Bashir Sani Sokoto yayi ya ce: Wadanda
suke kasar China idan aka ce su dubi alqibla to zasu kalli Yamma maso kudu
Wadanda suke a Amurka zasu kalli Gabas maso kudu. Wadanda
suke a Madina zasu kalli arewa
Mu kuma yan Nigeria ba zamu dubi Gabas kai tsaye ba, domin
kuwa idan mukai hakan, to ganinmu zai doshi Sudan ya wuce Ethiopia har zuwa
Tekun Maliya (Kogin Euphrates, wanda yabi ta bayan gidan Fir'aunan zamanin
Annabi Musa AS), maimakon mu kalli Gabas santal saidai mu dubi Gabas maso Arewa
(wato North-East)
A kissafin Latitude na jihar Sokoto yana daidai da
13.02°North. Yayinda garin Makkah suke da 21.25°North. Banbancinmu da su shi ne:
8.24°North-East. Kenan sai mun dan karkata kadan zuwa ga 8.24°N-E (wato Gabas
amman a dan kalli Arewa kadan) sannan ne zamu iya kallon dakin Ka'abah kai
tsaye, cikakken dubi
A bangaren Longitude kuwa, muna bangaren 5.15°East, su kuma
Makkah suna da Longitude 39.49°East, banbancin dake tsakaninmu dasu shi ne;
Longitude 34.34°. Kamar yanda muka sani Longitude ana amfani da shi ne wajen
auna lokaci (wato Time wanda ya fara daga 0 tun daga lokacin da Allah SWT ya
fara halitta)
Idan muka ce 34.34 ÷ 15 zai ba da awanni 2.289. Idan kuma
aka yi converting into HMS system zai koma awanni 2 da mintuna 18 da second 22
(2hrs, 17mins, 22secs, wannan shi ne dalilin da zaka ji ance banbancinmu da
Makkah awanni 2 ne. Ku duba ku gani mana lokacin azumin Ramadan da muke jiran
kiran sallar Magriba mu sha ruwa su kuma tuni ma sun dade da kammala Isha'i har
ma sun fara sallar Asham)
To ananfa wanda ya dubi gabas dodar bashi da laifi, saboda
Allah SWT bai sa mana cewar dole sai mun kalli Gabas kai tsaye ba, saidai mu
kwatanta saboda hujjar ayar;
لَا يُكَلِّفُ
اللَّهُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا ۚ
البقرة
(286) Al-Baqara
"Allah ba Ya kallafa wa rai face ikon yinsa,"
Abin lura anan shi ne, da yawan masallatai zakaga ba Gabas
din kai tsaye muke kallo ba, zaka ga idan an tashi gina masallachi musamman a
kusa da titi kawai sai kaga an yi masallachi, sai yazamo yayi mudabaqa da titi,
ba Gabas din yake kallo ba. Shi yasa ake son indai za'a gina masallachi to a
samo wadanda suka san alqibla su ginashi akan 8.24° saboda da yawan masallatai
titi suke kallo idan an tashi ginasu bawai alqiblar ake bawa muhimmanci ba.
Sauran aiki kuma ya rage ga Geographers. Kuma kallon alqibla wajibine in banda
wasu wurare qalilan da ba dole bane sai an kalli alqibla din ba kamar irin wanda
ya tsinci kansa a daji kuma ya kasa gane alqiblar
A binciken da nayi kwanaki akan Mu'ujizar dakin Ka'abah
(Miracles of The Holy Ka'abah via Rational Believers Channel) na gano wani abin
mamaki dangane da shi wancan Latitude din na Ka'abah wato 21.25°North kamar
haka;
A cikin Qur'ani tun daga Suratul Fatiha har zuwa Suratun
Nas, Surar da ta fara magana akan Ka'aba ita ce Suratul Baqara (wato Sura ta
2), kuma abin mamakin shi ne sunan Ka'abah din ya fito ne a cikin aya ta 125;
( وَإِذْ
جَعَلْنَا الْبَيْتَ مَثَابَةً لِّلنَّاسِ وَأَمْنًا وَاتَّخِذُوا مِن مَّقَامِ إِبْرَاهِيمَ
مُصَلًّى ۖ وَعَهِدْنَا إِلَىٰ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْمَاعِيلَ أَن طَهِّرَا بَيْتِيَ
لِلطَّائِفِينَ وَالْعَاكِفِينَ وَالرُّكَّعِ السُّجُودِ )
البقرة
(125) Al-Baqara
Kuma a lokacin da Muka sanya dakin ya zama makoma ga mutane,
da aminci, kuma ku riƙi wurin salla daga Maƙami
Ibrahim, kuma Muka yi alƙawari
zuwa ga Ibrahim, da Isma'ila da cẽwa:
"Ku tsarkake ¦akiNa domin masu ɗawafi
da masu lizimta da masu ruku'i, masu sujada."
Kenan idan ka dauko Latitude na coordinates din Ka'aba shi
ne 21° da kuma 25', idan muka canza percentage ratios din zai koma 21:25, ita
kuma ma'anar mu'ujizar zata zama; 2:125 (wato Baqara aya ta 125). Allahu Akbar!
Sannan kuma ayata 142 ta tabbatar da cewar akwai wadansu
wawaye (wato Yahudawa) da zasu yi mamakin me yasa musulmai da suna kallon
Masallachin Baitul Muqaddis (Masjid al-Aqsa) dake Palestine amman yanzu kuma
sun koma kallon Masallachin Ka'abah (Masjid Haram) kamar yanda Allah SWT ya
fada;
( سَيَقُولُ
السُّفَهَاءُ مِنَ النَّاسِ مَا وَلَّاهُمْ عَن قِبْلَتِهِمُ الَّتِي كَانُوا عَلَيْهَا
ۚ قُل لِّلَّهِ الْمَشْرِقُ وَالْمَغْرِبُ ۚ يَهْدِي مَن يَشَاءُ إِلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ
)
البقرة
(142) Al-Baqara
Wawaye daga mutane za su ce: Mẽne ne ya juyar da su daga alƙiblarsu
wadda suka kasance a kanta? Ka ce: "Allah dai ne Yake da gabas da yamma,
Yana shiryar da wanda Yake so zuwa ga hanya madaidaiciya."
Wannan ayar ta saukane tun kafinma a juyar da Alqibla daga
Masjid al-Aqsa zuwa Ka'abah don Allah SWT ya sanar da Annabi SAW ilimin gaibu
cewar ga abinda Yahudawa da munafukai zasu ce idan aka canza alqiblar, kuma
wannan canzawar shi ne zai tabbatar da shi wancan location din na Ka'abah wato
21.25° (degree), iya wannan hujjar kadai ta isa ta tabbatar maka cewar Allah
SWT shi ne Ubangijin mafadan rana guda 2. Kuma abin mamakin shi ne; a zamanin
Annabi SAW babu Telescope ballantana a harba shi sama ya iya gano wannan
lissafin, amsar daya ce anan, wato Ubangiji Allah SWT ya sanar da wannan ilimi
wanda kwanannan (20th century) wato cikin qarni na 20 aka gano hakan. Allahu
Akbar!
Wallahu ta'ala a'alam
Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa
anta, astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa;
Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.