Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarihin Marigayi Injiniya Abdu Gusau (Garkuwan Sakkwato)

An haif Marigayi Injiniya Abdu Gusau Ranar 15 ga watan Yuli na shekarar 1918, ya yi wafati Ranar 6 ga watan Nuwamba na Shekarar 1994, kenan shekarun sa 76 a duniya, Allahu Akbar!

Bayan karatun Addinin Musulunci da ya soma tun ya na yaro har ya zuwa wafatin sa, ya halarci Makarantar Midil ta Sakkwato da Makarantar Fasaha da Ƙere- Ƙere ta London (Woolwich Polytechnic) a cikin shekarar 1947 inda ya samu damar zama ƙwararren Injiniya na gine-gine. Tun a can ne ya soma aiki da  Kamfanin Taylor Woodsrow dake London.

Ya riƙe muƙamai da dama, kaɗan daga cikin su kuwa sune : Babban Jami'in kula da Sashen Gine-gine na Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria, Kwamishinan Kula da Ayyukan Gine-gine a Tsohon Lardin Sakkwato, Daraktan Ayyuka a Babban Bankin Nijeriya, Daraktan Ayyuka a Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto, Shugaban Kamfanin Siminti Na Arewa (CCNN) a Sakkwato, Shugaban Hukumar Gudanarwa ta Kwalejin Fasaha Da Ƙere - Ƙere  ta Jihar Sakkwato da kuma matsayin Jami'i na biyu mai kula da harkokin gudanarwa na Jami'ar Ilorin, Jihar Kwara. Waɗan nan ayyuka basu haɗa da muƙaman da ya riƙe a kamfanona na Gwamnati da masu zaman kan su ba.

Jigo ne a Babban Kwamitin Yaƙin Neman Jihar Zamfara. Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III ya naɗa masa rawani na sarautar gargajiya a Ranar 18 ga watan Maris na shekarar 1973, ya samu lambar yabo daga Sarauniya Elizabez ta Ingila da ake kira MBE (Member Of the Order Of the British Empire) da kuma lambar yabo ta Ƙasa ta Tarayyar Nijeriya OON (Officer Of the Order Of the Niger) saboda ƙwazon sa. 

Ya na ɗaya daga cikin Injiniyoyin da suka gudanar da aikin gina wani sashe na sauka da tashin fasinjoji dake Babban Filin Sauka Da Tashin Jiragen Sama na  biyu mafi girma da daraja a Duniya da ake kira Heathrow Airport a Turance dake London.

Ya rasu ya bar iyalai masu albarka a duniya, an kuma karamma sa ta hanyar sakawa Kwalejin Fasaha Da  Ƙere - Ƙere ta Jihar Zamfara sunan sa.

Wannan Bawan Allah shi ne, Injiniya Alhaji Abdu Gusau, Garkuwan Sakkwato. Allah ya jiƙan sa da rahama shi da sauran magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

www.amsoshi.com
Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments