Ticker

Tsafe Garin 'Yandoto

Shin ko ka san/ke san  laƙabin Sarautar Tsafe (Masarauta mai daraja ta ɗaya  a Jihar Zamfara a halin yanzu) shi ne "Yandoto", ko  ka san /ke san dalilin kiran Sarautar da Yandoton Tsafe?

Malam Ummaru Ɗan Ƙauran Katsina Mayaƙi Gemun Dodo ne ya fita daga Kwatarkwashi inda ya bar Ɗan Uwanshi Malam Abu Kwatashi /Kwatashi Abu/Kwatarkwashi Abu/Abubakar Kwatashi Ɗan Ƙauran Katsina Mayaƙi Gemun Dodo, shi kuma ya miƙa sai zuwa Yandoto dake Kudu da Kwatarkwashi, ya tarad da Manyan Malaman dake jibge a Yandoto akasarinsu masu zuhudu ne, basu buƙatar sha'anin mulki, saboda haka sai su ka gabatar dashi Malam Ummaru a matsayin jagoransu a sarauce.

Ya ci gaba da mulki har zuwa wafatinshi, 'yayansa suka gade/gaje shi suka ci gaba da mulki anan Yandoto gabanin bayyanar Yaƙin Jaddada Addinin Musulunci Na Daular Usmaniya da Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ya Jagoranta a farkon ƙarni na 19.

Daga cikin zuriyarshi wasu suka fita daga Yandoto, suka ƙara nusawa zuwa Kudu har sai da suka iso wurin da Tsafe take a halin yanzu, suka tarad da wasu gungun jama'a da suka Ƙaurace /Tsafe daga cikin sauran yan uwa (wannan shi ne dalilin kiran Masarautar da sunan Tcahe, daga baya aka canza sunan zuwa  Tsafe). Bayan sun samar da tsarin sarauta a wannan wurin ne sai suka kira Jagoran nasu da suka amince ya yi Sarauta /ya zamo Sarkin su da sunan garin da mahaifinsu Malam Ummaru Ɗan Ƙauran Katsina Mayaƙi Gemun ya yi sarauta kuma inda suka baro, wato Yandoto. Tun daga lokacin ne ya zuwa yanzu ake kiran laƙabin Sarautar wannan wuri/gari/masarauta ta Tsafe da Yandoton Tsafe. Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.
www.amsoshi.com
Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments