TAMBAYA (67)❓
Menene hukuncin wanda yake ihu da timuwa a kasa saboda an yi
masa mutusa ?
AMSA❗
Ba mu da abin fada face abinda Annabi SAW yace a lokacin da dan
sa (Ibrahim) ya rasu; "Haqiqa ido yayi wahaye, zuciya ta quntata, ba ma da
abin fada face abinda zai farantawa Ubangiji. Muna baqin cikin rashinka ya
Ibrahim"
Bukhari 1303 da Muslim 2315
Da kuma abinda Abu Dardaa ya fada; "me nake gani yayinda
mutane suke qoshi da abinci amman kuma suna tsananin jin yunwar ilimi"
Da kuma abinda Ayyub as-Sakhtiyaani ya fada; "Haqiqa idan
labarin mutuwar Ahlus Sunnah ya riskeni, sai naji kamar wata gaba ce a cikin
gabobin jikina ta fadi"
Abu Nu'aym al-Hilya Vol. 3 page 9
Da kuma abinda Imam Ibn al-Qayyim ya fada a cikin Miftaah Daar
us Sa'aadah, a page 74 yace; "Kyakkyawar rayuwa ita ce kusantar malamai,
saboda idan babu su to mutane zasu koma ne tamkar shanu a garke ko fiye da
haka"
Wallahu ta'ala a'alam
Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta,
astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa;
Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.