Wakar Mai Batun Yaƙi Da Sabra: MakaDa Amali Sabubu (Daga Ratayen Littafin Cimakar Hausawa)

Gindin Waƙa: Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,

  Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.

 

Jagora: Kada ruwa su ci mai hito,

Yara: Tun da bami bai iya ba. ×2

 

Jagora: Kada ruwa su ci mai hito,

Yara: Tun da bami bai iya ba,

            Ya yi halin maza,

            Ko da rani bai sake ba,

            Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.

 

Jagora:Kada ruwa su ci mai hito,

Yara: Tun da bami bai iya ba.

 

Jagora: Ran da bami ya iya,

Yara: Shi gwani ya gwanshi kai nai. ×3

 

Jagora: Ana ruwa Ɗan Namudi,

Yara: Mijin Hana ceci gayya. ×2

 

Jagora: Ana ruwa roƙi Allah,

            Ya bar ma masu son ka,

Yara: Ɗiyan maƙiyanka su ko,

            Su hude ciki da barho.

 

Jagora: Ana ruwa roƙi Allah,

            Ya bar ma masu son ka,

Yara: Ɗiyan maƙiyanka su ko,

            Su hude ciki da barho.

            Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,

            Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.

 

Jagora: Sarki ya yi doka a bar waƙar manoma,

            In ba mu garza su ba aiki sukai ba,

Yara: Dan nan am mahwarin hatci,

            Ya katce ma gwarza,

            Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,

            Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.

 

Jagora: Ga wasu na hwarin ciki an dwaɗikke roƙo,

            Wannan mai hwarin ciki komi bai daɗa ba,

            Wasu na baƙin ciki roƙo ba a yi nai,

Yara: Wannan mai baƙin ciki ba rowa ya kai ba,

            Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,

            Sauka lahiya mai batun yaƙi da sabra.

 

Jagora: Ga sadda ana kiɗi ba ni kwana ba ta gari,

Yara: Da anka ruhe kiɗi ko kumallo ban ƙarawa,

            Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,

            Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.

 

Jagora: Garba ga ni tsakag gida,

Yara: Ga takaici na ta cin ka.

 

Jagora: Sana ga ni cikin gida,

Yara: Ga takaici na cin ka.

 

Jagora: Labbo ga ni cikin gida,

Yara: Ga takaici na cin ka.

 

Jagora: Ga ni ba kuɗɗin awo,

Yara: Ga ka ba tsabad dakawa. ×2

 

Jagora: Tun da gero ya ɓace,

Yara: Dole sai mu gama da gari,

            Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,

            Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.

 

Jagroa: Mu zo mu ga mai jiƙo,

Yara: Alhajin jama’a Arewa. ×2

 

Jagora: A kai ni ga mai jiƙo,

Yara: Alhajin jama’a Arwa.

 

Jagora: Gari ya hito daz Zanhwara,

            Ya dubi Gobir,

            Garo ya buga gabas,

            Ya kuma ma yamma,

            Na yi abin wata ina taɓa yawon ƙasaisai,

            Ina saitin gidaje ina ta awon manoma,

Yara: Yau duk inda nib biya gari na rigya na,

            Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,

            Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.

 

Jagora: Yau duk ina nib biya,

Yara: Gari na rigya na,

            Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,

            Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.

 

Jagora: Kun gani yunwag ga,

Na sa mutum ya yi zamne jangwam,

Yara: Yana magana cikin zuciya tai,

            Ba a sani ba.

 

Jagora: Sai ka ji zuciya,

            Tanai mai ebe-ebe,

Yara: Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,

            Sauka lahiya mai batun yaƙi da sabra.

 

Jagora: Ashe yunwag na sa mutum ya gaza da mata,

Yara: Ya sa a yi mai jiƙo,

            Ba ya ce mata tashi gashi,

            Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,

            Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.

Jagora: Ka ga yunwag ga na iske ɗan gaye ta shuwai,

Yara: Ta ce mai tashi zaune.

 

Jagora: Ashe yunwag ga na iske ɗan gaye ta marai,

Yara: Ta ce mai ya hakan ga,

            Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,

            Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.

 

Jagora: Na ga ɗan gaye da gayan tuwo ya sa ga baki,

            Kuɗɗin sabulu masu gari anka ba su,

Yara: ‘Yan kuɗɗin ɓula masu bakuru nar riƙe su,

            Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,

            Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.

 

Jagora: Wanga irin baƙin zamani Allah kiyaye,

            Wasu na ta tashi suna tahiyas su Gwambe,

            Mu kam mun tsaya nan muna gyaran gidaje,

            In mun cimman gyaranta ba tashi mukai ba.

 

Yara: In ta ɓaci ko Singa ba ta rigam mu bi ma,

            Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,

            Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.

 

Jagora: Shekarun dandi ne,

Yara: Ba gudun kunya akai ba. ×2

 

Jagora: Yanzu karuwa tai yawa,

Yara: Ga su nan hab ba iyaka.

 

Jagora: Kuma ga ƙattan da an nasu,

            Ba aiki sukai ba. ×2

 

Jagora: Masu noma ‘yan kaɗan,

Yara: Masu ci nai ba iyaka.

 

Jagora: Karuwa ke baro uwaye ke zaɓi dandi,

Yara: Wagga ɗiya uwayenki na da baƙin cikinki,

            Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,

            Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.

 

Jagora: Tashi ba ki da gaskiya,

Yara: Ke baro ɗakin mijinki. ×2

           

Jagora: A a daw wata gaskiya?

Yara: Sai da aure za a yinta.

 

Jagora: Da duk ba a gyara aure ba,

Yara: Ke ma ba a yin ki.

 

Jagora: Dub ba a gyara aure,

Yara: Ke ma ba a yin ki.

 

Jagora: Ke an yo ki,

Yara: Ko ɗa guda ba ki samu yi ba.

 

Jagora: In da kwana duniya ba a kwana lahira.

Yara: Ran da kwana nac cika,

            Ban ga kwana duniya ba.

 

Jagora: A sai nono da mai,

Yara: In ji matan mai bisashe. ×2

 

Jagora: Ku sai tsabat tiya,

Yara: In ji mai mai ɗakin manomi. ×2

 

Jagora: Duk ku kawo in saye,

Yara: In ji matam mai sulalla,

            Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,

            Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabta.

The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology.  Data is collected from interviews with different categories of people including:  i.                    Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets.  ii.                  People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas.  iii.               Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets.  Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas.  The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.).  Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes.  Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food.  7th November 2022
Citation (Manazartar Littafin): Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

abuubaidasani5@gmail.com 

Post a Comment

0 Comments