Wakar Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Ta Makada Musa Dankwairo

    Wakar Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Ta Makada Musa Dankwairo
    ... Ya ja mani Rabbana Atiina,
    Had da Ƙullan Yasibana yaj jaman...

    Wani É—an WaÆ™a a cikin WaÆ™ar Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Suleja, Malam Ibrahim Dodo Musa wadda MakaÉ—a Musa ÆŠanÆ™wairo Maradun ya rera masa mai amshi 'Mai Ƙasas Suleja É—an Musa, ba a kai maka wargin banza'. 
    Mai wannan hoton ne ya yi ƙarin wannan ɗan Waƙar a tsarinsu na karɓa - karɓa kuma shi ne Marigayi Alhaji Sani Musa Ɗanƙwairo Maradun(wanda ke saye da kaya kalar baƙi) da aka fi sani da laƙabin "Sani Zaƙin Murya" dake da muƙamin Marafan Kiɗi a Tawagar Kiɗa ta Marigayi Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun. Ya rasu a Shekarar 1988 sanadiyar hatsarin /haɗarin Motar da ya yi akan hanyar Gusau Zuwa Sakkwato kafin akai Garin Dange, Ƙaramar Hukumar Mulkin Dange /Shuni dake Jihar Sakkwato. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Daga Taskar:
    Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
    ÆŠanmadamin Birnin Magaji
    Imel: birninbagaji4040@gmail.com
    Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.