Wakokin soyayya a karni na 21: Kallon kwakwaf a faifan Al'ada

 Takardar ƙara wa juna sani da aka gabatar a ajin ALH 400: Seminars, a Sashen Nazarin Harsuna Da Aladu, Jamiar Tarayya Gusau, Nijeriya, (2022/2023 Academic Session).

Federal University Gusau (FUG) Nigeria

Wakokin soyayya a karni na 21: Kallon kwakwaf a faifan Al'ada

Na

Name: Nafisa Aliyu

Admission no:1810104016

Department: Languages and Culture

Federal University Gusau

Gmail: nafisaaliyu173@gmail.com

Tsaƙure

Wannan aikin ya shafi waƙoƙin soyayya a ƙarni na 21, wato a wannan aikin an yi kallon ƙwaƙwaf ne a faifan Al'ada. Aikin ya mayar da hankali ne a kan gano matsayi ko gurbin waƙa a Al'ada da duba wasu waƙoƙin na Soyayya a yau domin gani irin kalaman da su mawaƙan suke saƙawa a wakoƙin nasu. A inda a wannan nazarin an gano kurakurai da mawaƙan ke tafkawa ta inda suke nuna halin ko in kula wajen tsara waƙoƙinsu. Yayin gudanar da wannan Bincike an yi amfani da ingantattun hanyoyin tattaro bayanai da suka haɗa da waiwaye a kan ayyukan da suka gabata da ziyartar ɗakunan karatu da bincike a yanar gizo da kallon bidiyo da sauraron wasu waƙoƙi, da ma yin la'akari da abubuwan da matasa suka mai da hankali a kai, ta haka an gano yadda al'umma na da da na yanzu suka bai wa waƙa matukar muhimmancin da har ya tasirantu da yadda suke gudanar da al'amurran rayuwa a yau da kullum. kana kuma duba da irin yadda waƙa ta samu gindin zama a rayuwar Hausawa da kasancewarta cikin rashe na Adabin al'ummar Hausawa. kamar yadda za a gani a wannan muƙala. Ana bada shawarar cewa marubuta waƙoƙin soyayya a wannan ƙarni na 21 yana da muhimmanci su mai da hankali a kan irin kalmomin da za su rikka amfani da su don gudun gurɓata wa matasa tunani.

1.0 Gabatarwa

Kafin mu nutsa cikin bayani, ya kyauta mu yi waiwaye a kan ma'anar waƙa: kamar yadda masana suka bayyana waƙa ta kasu kashi biyu, wato waƙar baka da kuma rubutacciyar waƙa. Duba da cewa wannan aikin zai yi nazari ne a kan waƙoƙin ƙarni na 21, wato ana Maganar zamani kenan, don haka wannan aiki ya shafi rubutattun waƙoƙi ne. Bari mu duba ma'anar waƙa Rubutacciya kamar yadda masana suka kawo.

Bunguɗu, H.U da Maikwari, H.U (2019) sun kawo a littafinsu cewa "Rubutacciyar waƙa wani saƙo ne da ake gina shi a kan tsararriyar ƙa'ida da baiti da ɗango da kari da amsa-amo da sauran ƙa'idojin da suka danganci daidaita kalmomi, da zaɓar su, tare da yin anfani da su, a rubuce sannan a rera lokacin da ake buƙata.

Gusau, (2001) ya ce "waƙa ta bambanta da taɗi na yau da kullum, aba ce da ake shirya maganganu daki daki cikin azanci da nuna ƙwarewar harshe. Harshen waƙa cikakke ne, duk da yakan kauce wa wasu ƙa'idojin nahawu, wannan kenan.

Duba da cewa wannan aikin yana nazari ne a kan waƙoƙin soyayya na Zamani wato ƙarni na 21, sannan kamar yadda yake wakokin zamani suna tafiya ne tare da kiɗa musamman na Soyayya, an samu taƙaddama a kan shin waƙoƙin zamani za su shiga cikin wani rukuni ne? Shin cikin waƙoƙin baka za a sa su ko kuwa na zamani? Za a bayyana hakan a nan gaba kaɗan cikin wannan muƙalar.

1.1 Ra'in Bincike

An daura wannan Binciken ne a kan ra'in 'ƙwakƙwafi'(close reading) bisa la'akari da taken wato "........ Ƙallon ƙwaƙwaf a faifan Al'ada" domin irin bin diddigin da aka yi na gano gurbin waƙa a Al'ada da kuma yadda a kai wa wasu waƙoƙin soyayya na ƙarni na 21 kallon ƙwaƙwaf domin fitar da wasu ƙalmomi ko manufofin da mawakan yanzu suke saƙawa a waƙarsu, saɓanin wadda aka saba da shi a al'adance. Farfesa Ivor Armstrong Richards, (1893-1979) wani masani daga Ingila ne ya assasa mazhabar nazarin ƙwaƙƙwafi. Ya gina mazhabar nazarin ayyukansa waɗanɗa suka haɗa da;

a. The meaning of Meaning.

b. Principles of Literary Critici

c. Practice of Retoric.

d. Philosophy of Retoric.

Yawancin ɗaliban wannan mazhabar sun fito ne daga Ingila da Chicago da kuma sauran sassa na U.S.A. Daga cikin mabiyan wannan mazhabar akwai;

1. William Empso.

2. Franco Moretti.

3. Lesvis, F.R.

4. Clenth Brooks.

5. Blackmur, R.P.

6. Crame, R.S.

7. Murry Krieger.

8. Wimsert, W.K da sauransu.

1.2 Dabarun Bincike

Don tabbatar da inganci da kuma Sahihancin wannan bincike an bi wasu ingantattun hanyoyin tattaro bayanai kamar haka;

a. Ziyartar ɗakunan karatu na jami'a da kwaleji.

b. Bitar ayyukan da suka gabata.

c. Bincike a yanar Gizo.

d. Sauraron Odiyo da kallon bidiyo na waƙoƙi.

e. Duba muƙalu.

2.0 Waiwaye a kan Ma'anar Al'ada

Al'ada kalma ce da ake ara daga larabci, aka mayar da ita 'yar gida a Hausa. Ma'anarta ita ce sababben abu.Wato abin da aka saba da shi kenan. Shi kuwa Farfesa Ɗangambo (1984). Cewa ya yi "Al'ada ita ce abin da aka saba yi yau da gobe". Saboda haka, idan aka ce al'ada, ana nufin tsurar ko zallar ko gundarin abubuwan da aka saba yi a ƙasar Hausa. Idan wata hidima ta tashi kamar aure da suna da sauransu.

Al'ada ta shafi kusan dukkanin rayuwar Bahaushe. Idan aka lura sosai da hidindimun da ake yi a ƙasar Hausa, za a tarar cewa kowane akwai yadda ake yin sa, da kuma lokacin da ake yin sa. To wannan shi ne. Kenan, a taƙaice ana iya cewa al'ada Ita ce abin da aka saba yi yau da kullum wajen gudanarwa ko yin abubuwa. Kuma ta shafi abubuwan da ake yi yau da kullum. A ƙasar Hausa akwai al'adu iri iri da suka haɗa da Aure, Zanen suna da sauransu.

2.1 Gurbin waƙa a Al'ada

Waƙa dai ta jima tana tashe a al'adar Bahaushe. Duba da cewa duk wata al'ada ta Bahaushe tana tafiya ne tare da waƙa a cikinta. Misali kamar aure da zanen suna da muka ambata a sama, za a tarar cewa a duk waɗannan shagulgulan a kan samu mawaƙa da makaɗa, hasali ma akwai waƙoƙin da aka tanada don aure da zanen suna.

Haka ma lokutan gudanar da shagulgula a ƙasar Hausa, kaman su bukin naɗin sarauta ko ranar salla ko ma lokacin azumi (tashe) lokacin wasannin yara da samari da 'yan mata da yayin gabatar wa da yara da tatsuniya ( a kan samu waƙoƙi a ciki wato ƙodago) da yayin gudanar da aikace aikace na cikin gida ( ga mata) ko a waje ko a daji ga (maza) haka kuma kowace sana'a da ake da ita a ƙasar Hausa tana da irin tata waƙar da ake yi domin ta, don a rikka kurzanta wannan sana'ar da masu yin ta.

Haka ma ko a da can ana samun Samari na yi wa Masoyiyarsu waƙa ko budurwa ta waƙe gwaninta musamman a wurin gaɗa (wata wasa ce da 'yan matan Hausawa kan yi da dare kafin dare ya tsala) haka ma ana samun waƙoƙi da almajirai suke yi yayin da suka fita Bara da waƙoƙin yabo na madahu da dai makamantansu.

Don haka za mu fahimci cewa waƙa tana da babban gurbi a al'ada kwarai! Domin idan aka duba bayanan da aka kawo a sama za a ga cewa kusan dukkanin matakan rayuwar Bahaushe akwai waƙa a cikinsu. Hatta da mutuwa idan aka yi akan yi waƙa ta ta'azziya. Misalin wakar Rasuwar Murtala, wanda aka kashe shi a juyin mulkin da connel Dimka ya yi sai kuma waƙar da Shaihu Alƙanci ya rubuta na haɗarin jirgin sama da aka yi da Alhazai a (1973) a Kano sunan waƙar ta'azziyar haɗarin jirgin sama (1973) haka ma da ta'azziyar Sarkin Kano Abdullahi Bayero (naƙaltar Malama Halima Kurawa) tana cewa " Galibi mutanen da suka shahara bayan sun rasu a kan rubuta waƙoƙin ta'azziya, a wakoƙin baka". Kawo yanzu ma a kan samu mawaƙan zamani suna yin waƙoƙin ta'azziya musamman ga 'yan uwansu mawaƙa ko 'yan Fim, Misali waƙar ta'azziyar S.Nuhu da Balaraba Musa waɗanda suka yi hatsarin mota, da Rabilu Musa wanda aka fi sani da Ibro wani shahararren ɗan wasan barkwanci ne a masana'antar fim ta kannywood, ko ma wani Sanannen mutum ko 'yan siyasa waɗanda suka riga mu gidan gaskiya. Kenan tun asalin inda aka fito tun da can, al'ummar Hausawa ta sadu da waƙa. Don haka tsayawa bada tarihin asalin samuwar waƙa ga Bahaushe Labari ne mai tsawo! Zahirin abun shi ne waƙa dai karɓaɓɓiyar lamari ne a al'ada domin kuwa idan aka duba fannin adabin Hausa za a ga cewa waƙa na ɗaya daga cikin reshen adabi. Sauran su ne; Zuɓe da Wasan ƙwaiƙwayo. Wannan kenan.

3.0 Waƙoƙin ƙarni na 21

Bunguɗu, H.U da Maikwari, H.U ( 2019:64-65) sun kawo cewa" Masu iya magana sun ce 'zamani baƙo ne'. Don haka sai mu gani shin ko mutanen da suke yi wallafe wallafe a wancan zamanin su ne ke yi har yanzu koko akwai wasu da ke yi a yanzu haka?

Amsar tambayar kenan da za a amsa a wannan sashe. Amsar ita ce a'a, a yau ma muna da marubuta da suke yi mana rubutun waƙoƙinmu daidai da na Zamaninmu na yau. Babu shakka wannan lokaci shi ne ƙarni na 21 kuma akwai marubuta da dama ba mu iya cewa ga adadinsu amma ga kaɗan daga cikinsu; Shaihin Malami Aliyu Muhammadu Bunza, Kaftin Suru Ummaru (RTD) da Shaihin Malami Haruna Abdullahi Birniwa, Shaihin Malami Abdullahi Bayero Yahya, Malam Musa Maidawa (surus) da dai sauransu. Su waɗannan malamai marubuta waƙoƙin Hausa ne kuma su kan samu jigo na musamman su rubuta waƙoƙin don shi. Sukan rubuta waƙoƙinsu ne tare da yin amfani da salon da waɗanda suka gabace su suke amfani da shi.

An faɗa a baya cikin ƙarni na 20 cewa mawallafan wannan ƙarnin suna amfani da Bahaushen kari ne ko ma wani lokacin su kwaikwayi muryar indiya su yi waƙa da ita kuma waƙar ta yi daɗi. A wannan ƙarni ma akan yi haka kuma kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Da yake zamanin yau ya canza wasu mutane da suka dauki waƙar sana'a, su ma su kan rubuta kuma su yi amfani da kayan kiɗan zamani su rera. Amma galibin waɗannan mawaƙan sun fi yin waƙoƙin ga jigogin Siyasa da Aure da yabo da soyayya da dai sauran abubuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum.

3.1 Waƙoƙin Zamani

Kamar yadda aka tattaro bayanai daga manhajar 'manhajar blueprint.ng'. an samo bayanai kamar haka " Waƙoƙin zamani waƙoƙi ne da suka fara daga tsakiyar ƙarni na 20 zuwa ƙarni na 21 har zuwa wannan lokaci da nake gudanar da wannan nazari. An kira su da waƙoƙin zamani ne saboda sun saɓa da al'adar tsara waƙa a Hausa, kadayake tarihin samuwarsu ya nuna mana cewa sun faro ne daga waƙoƙin bege ko waƙoƙin yabon Annabi Muhammadu (S.A.W) waɗanda aka fi sani da waƙoƙin Mandiri. Fitattun marubuta irinsu Ɗan'azumi Baba da Alƙasim Bature da Sani Yusuf Ayagi da sauransu suka buɗe wannan fagen ta shirya waƙoƙin Zamani. A inda suka fara buɗe fagen da shirya waƙoƙin finafinai amma bisa tsarin rubutacciyar waƙar Hausa. Mandawari (2004) da Hauwa ( 2014).

Kenan za a iya cewa haɗa kiɗa da waƙa ya faro ne a wannan lokacin a ƙoƙarin masu shirya finafinai na samar da waƙa a cikin fim da nufin ƙayatar da finafinan Hausa da bunƙasa su da kuma yunƙuri daƙushe finafinai indiya waɗanda suka cika kasuwanni a ƙasar Hausa, musamman a tsakiyar ƙarni na 20. An fara tsara waƙoƙin fim da dora musu kiɗa a tsakanin Shekarar 1997 da 1998, misalin fitacciyar nan ta fim ɗin 'Daskin da Riɗi' da fim ɗin 'Badaƙala'.

4.0 Waiwaye A kan Ma'anar Soyayya

A wata muƙala da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani wanda Cibiyar Nazarin Hausa ta shirya. A cikinta marubucin ya kawo ma'anar Soyayya, " Soyayya ita ce ƙawa-zucci ko tsananin kaunar wani abu. (Bello Sa'id, 1982:1)

Marubucin ya sake kawo wata take wato 'Dangogin Soyayyar Bahaushe', ya kawo cewa "Soyayya tana da dangogi, a inda ya kawo kamar yadda Bello Sa'id, (1982: 1-2) ya kawo su kamar haka;

a. Son da ke tsakanin mutum da Ubangijinsa Mahalicci.

b. Son da ake yi wa Annabawa musamman Annabi Muhammadu (S.A.W) da Sahabbansa da sufaye da waliyai da Malamai da wasu Shugabanni na Addinin Musulunci.

c. Kaunar da ke tsakanin uwa ko uba da 'ya'yansa ko kuma irin ta zumuntar jini. Kamar ɗan uwa na wajen uwa ko uba.

d. Son da mace ke yi wa namiji, ko wanda namiji ke yi wa mace. Irin wannan so idan an yi musanyarsa tsakanin bangarorin biyu, yana iya zama Soyayyar ƙawance, idan Soyayyar ta yi ƙarfi akan kai matsayin yin aure. To irin wannan soyayya ce Allah Madaukakin Sarki ya ambata a Cikin Alkur'ani Mai Girma, cikin Suratur Rum aya ta 21, " Ɗaya daga cikin ayoyinSa ita ce, " Ya halitta muku matanku daga jikinki, domin ku rayu tare da su cikin natsuwa. Ya kuma sanya Soyayya da jinƙai a tsakaninku........"

4.1 Kallon ƙwaƙwaf daga wasu waƙoƙin soyayya na Zamani

Waƙoƙin soyayya a yau sun zama ruwan dare leƙa gidan kowa, Musamman ga matasa. Mawaƙan wannan zamani na Soyayya, su kan tsara waƙa ne ga masoyiyarsu ko kuma labarin wata kalubale da suka ci karo da shi a soyayya musamman na yaudara. suna tsara waɗannan waƙoƙin ne domin nuna tsananin kaunarsu ga abar kaunar tasu domin ƙara samun gurbi a zuciyarta da nuna bajinta a Soyayyar tasa.

Waƙoƙin soyayya waƙoƙi ne da sauraronsu ke sanya nishaɗi da shauƙi da natsuwa ga ma'abocin sauraronsu. A cikin waƙar akan ambaci kalamai masu kwantar da hankali da kurzanta kyawun masoyi ko Masoyiya ta hanyar Kambamawa ko ma zuzuwata kyawunta fiye da ƙima ma, da irin matsayin da Masoyiya ko masoyi suke da shi a zuciyar mai raira waƙar. Kana da nuna irin gararin da mutum zai shiga idan ya rasa abar kaunar nan tasa.

Waƙoƙin soyayya a yau sun sha bamban da irin waƙoƙin soyayya na baya, irin su;

a. Lisanul Hali' Na Muhammadu Kwanni Boɗinga.

b. Soyayya Ruwan Zuma Na Halliru Wurno.

c. Sahibi ta Hawwa'u kullu.

Binciken zai kutsa wasu waƙoƙin soyayya a yau don ganin wata irin waina ake tuyawa a cikinsu;

1:Waƙar so na amana ta Garzali Miko

Duk wanda yai ƙudurin za ya raba ni da

Hubbina,

Zan sa wuƙa in yanka shi koko

Almakashi.

A wannan waƙar an ci karo da kalmar Ta'addanci.

2: Waƙar Shagwaɓa wadda Abba El Mustapha da Asiya Chairlady suka hau;

Duk inda ka je Rwbbana ya kare ka,

Ka dawo mini lafiya ka zo mu kasance,

Ba na son mata su kalli fuskarsa,

Duk wacce ta kalli ka Allah sa ta makance.

A wannan waƙar an ci karo da kalmar Mugun fata.

3: Waƙar Buraubu ta Mr 442;

 Ka matso ni za ka ga Buraubu,

 Arewa na buƙatar Buraubu,

 Bidiyo kuma sun yi leaking,

 Ina son Maryam Booth.

A wannan waƙar ba komai sai tsantsar Zagi.

4: Waƙar Taɓara ta Mr 442 tare da Safara'u;

 Kowa na yin taɓara,

 In ba ka yi a waje,

 Ai kana yi a gida kai da 'yar matarka.

A wannan waƙar an samu kalmomin Rashin kunya.

5: Waƙar taɓara ta Mr 442 tare da Safara'u;

 Ke amarya ki koyi rawa x2

 In kin iya rawar taɓara ango kullum

sai yai jaraba.

A wannan waƙar an bayyanar da kalaman Batsa.

6: Waƙar Warr ta Ado Gwanja;

 Iye haka za su gan mu

Haka za su bar mu,

In Kun ƙi ku bar mu, sai na ci

Buhun ubanmu.

7: Waƙar Sambisa;

 Na je gida gida ina nemanka

 Liya liyana shirye kawai mu je Sambisa,

 Subhana ga baƙin labari wai kun ji an

Takura ni wai in je Sambisa,

 Jiji tsoho mai wanke goɗiyar kakanmu

ai shekaran jiya shazumamu ya cije shi

 Kuma ni nake zama gun jinyar......

A wannan waƙar an yi ƙarya ƙiri kiri, domin kuwa an san cewa shazumamu bai ciwo balle har ya saka mutum jinya, Ƙarya.

8: Waƙar da aka yi a fim mai suna wuff, a inda Lilin Baba da Ummi Rahab suka hau waƙar;

Kai ne zuciya take ta yabo,

 Kai ne nawa in da rai da rabo,

 Wuff da ke zan yi kar su ce

Sonki ba na yi har zuciya.

A wannan waƙar an ci karo da sabon kalma da babu ita a Hausa.

4.0 Sakamakon bincike

Sakamakon wannan Binciken ya bayyana mana cewa waƙa tana da babban gurbi a al'ada sannan tana taka rawa matuƙa, sannan an gano cewa waƙoƙin Soyayya a da da na yanzu suna da bambanci, duk da dai jigoginsu duk abu ɗaya ne, wato suna nishanɗarwa ne da kuma bayyana Soyayya ga abar kaunar ko abun kauna.

Amma a bincike an gano cewa idan aka kwatanta waƙoƙin soyayya a yau da na da za a tarar cewa waƙoƙin a yau suna dauke da wasu manufofi wanda sam al'ada ba ta aminta da ita ba kuma babu shi a cikin Koyarwa zamantakewar Rayuwar Hausawa. Don haka ana iya cewa 'haƙarmu ta cin ma ruwa' don ko a wannan bincike an yi nasarar bankaɗo wasu korakurai da mawaƙan soyayya a yau suke tafkawa, sanadiyyar wannan suna juya wa matasa akalar yadda ya kamata su fuskance rayuwa ba tare da yin watsi da koyarwar al'ada ba. Sakamakon yawancin matasa a yau suna kallon waɗannan mawaƙan a matsayin Madubi da za su yi koyi da su.

Don haka mawaƙa, musamman na Soyayya, su yi hattara da irin kalmomin da za su rikka jefawa a waƙoƙinsu. Don cewa a dena yin waƙoƙin soyayya abu ne mai wuyan gaske! Domin kuwa an ce "rai dangin goro ne sai da ban iska" amma su kula matuƙa da irin kalmomin da za su rukka amfani da su don kuwa matasa su ne manyanmu na gobe, domin kuwa idan suka gurɓata musu tunani da irin waƙoƙinsu wace irin al'umma za a yi a nan gaba. Don haka su kula.

Don haka matsalolin da ake ci karo da su a wakoƙin Soyayya na yau su ne;

a. Koyar da ƙarya ga matasa.

b. Yin mugun fata a cikin waƙoƙinsu.

c. Ambaton kalaman Batsa.

d. Rashin Kunya da rashin ta ido.

e. Yin zagi, wanda ba Koyarwa al'ada ba ce

f. Sabbin kalmomi: duk da ita wannan ba matsala ba ce, hasali ma sun samar wa da Harshen Hausa sabbin kalmomi.

4.1 Kammalawa

Kamar yadda aka kawo bayanai a wannan muƙala an yi ƙoƙari an kawo ma'anar waƙa, da Soyayya da kuma duba ra'ayoyin Masana dangane da ma'anar al'ada da wakoƙin zamani, Sannan an yi ƙoƙari an kawo wasu waƙoƙin soyayya tare da fitar da wasu kalmomi da furta su ya saɓa wa al'ada da ma dabi'u masu nagarta.

Daga ƙarshe an bada shawara ga mawaƙan soyayya a yau da su rikka hattara da irin kalmomin da za su rikka amfani da su a waƙoƙinsu don guje wa gurɓata tunani da tarbiyyar matasa a yau.

Post a Comment

0 Comments