Wanda Yayi Soyayya Da Matar Aure, Shin Ya Halatta Ya Aureta Bayan Mutuwar Auren Farko?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Don Allah inaso malam yayi Mani cikakken bayani akan mutumin da yayi soyayya da matar aure, kuma auren ta ya rabu amma ba shine dalilin rabuwar ta da mijinta ba, sai shi kuma ya nuna yanaso ya aureta bayan da auren nata ya mutu, shin ko akwai aure tsakanin shi da ita ta la'akari da cewa dama yayi soyayya da ita tun tanada aure? Allah ya qara ma malam lafiya.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Soyayyar da kayi da ita alokacin da take da aure, tabbas babban kuskure ne kamar yadda kai kanka ka sani. Kuma ba lallai ne ya zamto akwai hujjah ko dalilin dake tabbatar da cewa ba wannan soyayyar ce ta janyo mutuwar aurenta na farko ba.

Kasan su mata tunaninsu ba kamar na maza bane. Kuma zasu iya yin komai domin su samu su auri duk wanda zuciyarsu take kauna. Kuma Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya tsawatar sosai game da duk wanda ya zuga Matar wani ko kuyangar wani har ta bijire wa mijinta ko ubangidanta, to kamshin Aljannah ya haramta gareshi (ko kuma wani zance mai ma'ana irin wannan).

Amma idan mun dawo bisa doron tambayarka, wannan matar bata haramta gareka ba. Zaka iya aurarta. Sai dai zaifi kyawu gareka da kuma ita kanta, ku tuba zuwa ga Allah bisa wancan laifin farkon da kukayi. Tabbas cin amana ne, kuma yana daga cikin Kaba'irori. Ku tuba zuwa ga Allah ku nemi gafararsa domin ya sanya wa auren naku albarka, kuma ya kiyaye zuriyarku daga sharrin abinda kuka aikata.

Wannan fa idan baku taɓa yin zina ba kenan. Amma idan ka taɓa yin zina da ita, to wasu Malamai da yawa suna ganin cewa bai halatta kuyi aure ba. Acikin Maluman dake kan wannan fatawar akwai Sahabbai irin su : Sayyiduna Abubakr, Umar bn Khattab, Abdullahi bn Umar, Abdullahi bn Abbas, Jabir (yardar Allah ta tabbata garesu).

Duk Waɗannan suna ganin cewar bai halatta ga wani musulmi mai imani ya auri mazinaciya ba, har sai tayi cikakkiyar tuba daga abinda ta aikata abaya. Idan kuma shine yayi zinar da ita, babu aure atsakaninsu har sai sun tuba dashi da ita.

Kuma wannan ita ce fatawar magabata na kwarai irin su Dawus, Ata'u, Hasanul Basariy, Ibnul Musayyab, Jabir bn Zaid, Ibnu Shihab Azzuhriy, Sufyanus Sauriy, da sauransu.

Don Qarin bayani aduba Almughnee na Hafiz ibnu Qudamah Almaqdisiy (juzu'i na 7 shafi na 108).

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam


Post a Comment

0 Comments