Wanene Ya Rawaito Hadisin "Ar-Rahimun, Yarhamahumur Rahman

Tambaya (68)

Shin wanne sahabi ne ya rawaito hadisin: Ar-Rahimun yarhama humurrahman

AMSA

Alhamdulillah

Abdullahi Ibn amr bin al-As shi ne sahabin da ya rawaito hadisin; "Ar-Rahimun". To amman ta yaya zamu tabbatar kuma mu gasgata cewar shi ne ya rawaito wannan hadisin ?

Anan zamuyi duba ne zuwa ga abinda Ahlul Hadis, Muhaddisun (Malaman Hadisi) suke kira da Musalsal Hadis ma'ana hadisin da za'a zayyano sunayen wadanda suka karbo hadisin tun daga wannan zamanin har zuwa shekaru 1,400 can baya da suka wuce, wato tun daga yanzu zuwa zamanin Tabi'ut Tabi'un, zuwa Tabi'ai, zuwa Sahabbai, kai tsaye daga bakin Annabi SAW

Shaikh Muhammad Alyaqoubi, sharif daga kasar Syria, ya kasance jinin Annabi Muhammad SAW ne

Al-Yaqoubi tsatson Mawlay Idris al-Anwar ne, (founder din birnin Fès), jikan Sayyadina Hasan ibn Ali, jikan Annabi SAW. Kamar dai yanda Sarkin kasar Jordan na yanzu (mai shekaru 61) wato Sarki Abdullah II Bin Hussein ya kasance bahashime, jikan Annabi SAW na 41 (Kamar yanda Hashemite Kingdom of Jordan wato Masarautar Bani Hashim ta Jordan kasar Jordan ta fitar a shekarar 2020 a cikin Magazine dinta mai taken: 500 Most Influential Muslims In The World In 2020, ma'ana: Musulmai 500 masu ikon fada a ji a shekarar 2020)

Al-yaqubi ya kasance yana karantawa mutane wannan musalsal hadis din. Wanda shi ne hadisi na farko da a al'adance masana hadisi suke koyarda dalibansu domin fa'idantuwa da sunayen marawaita hadisin. Haka kuma ana kiran hadisin da suna; Musalsal haqiqatan bil awwaliyya

Ga sunayen marawaitansa kamar yanda Shaikh Hamza Yusuf Hanson (Mai Zaytuna College, California, Amurka) ya sanar damu;

Ana haddasani, abul huda Muhammadul yaqubi, al-hasani, al-idrisi, ad-dimishqi, wahuwa awwala hadisi sami'tahu minhu, qala haddasana, bihi shaikuna, al-allama, muhammad al-makki, bin muhammad bin ja'afar al-kattani, al-hasani, al-idrisi, alfasi ad-dimishqi, mufti al-malikiyyati, bi biladish sham, wahuwa awwala hadisin sami'tahu minhu, qala, haddasana, as-said ahmad bin isma'il al- barzanji, al-husaini, mufti shafi'iyyati bil madina almunawwara, wahuwa awwala hadisin sami'tu minhu, qala, haddasana, waridi, isma'il bin zainul abidin albarzanji, mufti shafi'iyyati fil-madinatil munawwara

Wahuwa awwa hadisin sami'tu minhu qal, haddasana, muhaddisil madinatil munawwara ash-shaik saleh bin muhammad al-umari, al-fullani, al-maliki, wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, haddasana shamsuddin muhammad bin muhammad bin abdallah almagribi, al-madani, wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, haddasana musnad al-hijaz al-imamu abdullah bin sal al-basri al-makki, wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, haddasana, alhafiz shamsuddin muhammad bin ala'addin salihal babiri al-masri, wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, haddasana shihabuddin ahmad bin muhammad, ash-shibri al-hanafi, wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, haddasana, jamaluddin yusuf bin shaikhal islam, zakariyya bin muhammad al-ansari

Wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, haddasana, burhanuddin ibrahim bin ali bin ahmad al-qalqashandi, wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, haddasana, shihabuddin ahmad bin muhammad bin abi bakar al-wasati al-maqdasi, wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, haddasana, shadruddin abul fath muhammad bin muhammad bin ibrahim al-maidumi al-hambali, wahuwa awwal sami'tu minhu qal, haddasana, musmilu masra abul-faraj abdallatif bin abdul-mun'im bin saiqal al-harrani al-hambali, wahuwa awwal sami'tu minhu qal, haddasana al-hafiz ash-shahir abul faraj abdurrahman bin ali al-ma'aruf bin aljauzi al-hambali

Wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, haddasana, abu sa'ad isma'il bin hafiz ahmad bin abdulmalik an-naisaburi al-wa'is, wahuwa awwal sami'tu minhu qal, haddasana, al-hafizul musnad abu salih ahmad bin abdulmalik bin ali an-naisaburi ash-shahir bin mu'azzan, wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, haddasana, musnid naisabur abu-dahir, muhammad bin muhammad bin muhammad bin mahnish az-ziyadi, wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, haddasana, abu hamid ahmad bin muhammad bin yahya bin bilal al-bazzaz al-mutawaffas sana salasa mi'atan wasalasina

Wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, haddasana, shaihul fuqaha bi makkata abu muhammad abdurrahman bin bishir bin al-hakam al-abdi wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, haddasani, amirul mu'umin sufyan bin uyaynata mutawafas sanata mi'a wa samaniya wa tas'in wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, anat tabi'iyal jalil abi muhammad amr bin dinar anat'tabi'il jalil abi qabusal mutawaffa ba'ada mi'ati mawla sayyadina abdallah bin amr bin al-as anas sahabiyal jalil, sayyadina abdullahi bin amr bin al-as qala, QALA RASULULLAHI SAW: AR-RAHIMUN, YARHAMAHUMUR-RAHMAN, YARHAMU MAN FIL ARD, YARHAMIKUM MAN FIS-SAMA" wafi riwaya: "YARHAMU MAN FIL-ARD YARHAMKUM BISH-SHARJ, YARHAMKUM MAN FIS-SAMA" Sadaqa Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam. Alhamdulillah

A ruwayar Tirmidhi kuma yazo kamar haka: An karbo daga Abdullahi Bin amr Bin al-As yace: Manzon Allah SAW yace; "Ku nuna rahama a duniya, wanda yake a saman bakwai zai nuna muku Rahama"

Jami' at-Tirmidhi 1924

Haka ma Muhammad Nasiriddin Albany ya ingantashi a cikin; Jami' at-Tirmidhi hadisi mai lamba ta 1924

Jan Hankali; Ya zama wajibi idan har muna son ganin daidai a al'amuranmu to mu fara saka Allah SWT a gaba, muyi komai da ikhlasi mu nesanta daga riya, musamman yan kasuwarmu, la'akari da sauran kasa da kwanaki 50 mu shiga watan azumi mai albarka. Kowa yasan halin da muka tsinci kanmu na tsadar rayuwa kuma la shakka duk hakan na faruwa ne silar munanan bayyanannu da boyayyun ayyukanmu

Taliyar Spaghetti ta gida ta doshi N500, yayinda na tambayi ta kasar waje sai mai kantin yacemin N700, a maimakon kayi raki, to anan kamata yayi ka roqi ar-Razzaqu ya azurta ka da dukiyar da zaka siyawa wasu cartons

Dole sai mun sauya sannan ne Allah SWT zai shigo lamarinmu, mu samu sauqin komai. Da ace yanda muke complain akan tsadar rayuwa, haka muke complain akan zunubbanmu to da munyi qoqarin hobbasa wajen gyarawa. Allah SWT ya fada a cikin Qur'ani mai girma cewar;

( لَهُ مُعَقِّبَاتٌ مِّن بَيْنِ يَدَيْهِ وَمِنْ خَلْفِهِ يَحْفَظُونَهُ مِنْ أَمْرِ اللَّهِ ۗ إِنَّ اللَّهَ لَا يُغَيِّرُ مَا بِقَوْمٍ حَتَّىٰ يُغَيِّرُوا مَا بِأَنفُسِهِمْ ۗ وَإِذَا أَرَادَ اللَّهُ بِقَوْمٍ سُوءًا فَلَا مَرَدَّ لَهُ ۚ وَمَا لَهُم مِّن دُونِهِ مِن وَالٍ )

الرعد (11) Ar-Ra'd

(Kowannenku) Yana da waɗansu mala'iku masu maye wa juna a gaba gare shi da baya gare shi, suna tsare shi daga umurnin Allah. Lalle ne Allah ba Ya canja abin da yake ga, mutane sai sun canja abin da yake ga zukatansu. Kuma idan Allah Ya yi nufin wata azaba game da mutane, to, babu mai mayar da ita, kuma ba su da wani majiɓinci baicin Shi.

Don haka idan har da gaske muna son shiga Aljannah to sharadin shi ne mu koma ga Allah SWT kamar yanda ya fada;

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا تُوبُوا إِلَى اللَّهِ تَوْبَةً نَّصُوحًا عَسَىٰ رَبُّكُمْ أَن يُكَفِّرَ عَنكُمْ سَيِّئَاتِكُمْ وَيُدْخِلَكُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ يَوْمَ لَا يُخْزِي اللَّهُ النَّبِيَّ وَالَّذِينَ آمَنُوا مَعَهُ ۖ نُورُهُمْ يَسْعَىٰ بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَبِأَيْمَانِهِمْ يَقُولُونَ رَبَّنَا أَتْمِمْ لَنَا نُورَنَا وَاغْفِرْ لَنَا ۖ إِنَّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ )

التحريم (8) At-Tahrim

Ya ku waɗanda suka yi ĩmani! Ku koma zuwa ga Allah komawar gaskiya. Mai yiwuwa Ubangjinku Ya kankare muku miyagun ayyukanku kuma Ya shigar da ku a gidajen Aljanna, ƙoramu na gudana daga ƙarƙashinsu a ranar da Allah ba Ya kunyatar da Annabi da wadanda suka yi ĩmani tare da shi. Haskensu yana tafiya a gaba gare su da jihohin damansu, suna cewa, "Ya Ubangijiumu! Ka cika mana haskenmu, kuma Ka yi mana gafara. Lalle Kai, a kan dukkan kome, Ya kai Mai ikon yi ne."

Wallahu ta'ala a'alam

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments