𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mace ce tana cikin iddan
saki guda da mijinta ya yi mata shi ne ta yi wasa da namiji amma bai kai ga
zina turmi da taɓarya ba! Shi ne take tambaya hukuncinta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.
Abu ne sananne cewa wasan banza da maza haram ne ko mace
tana da aure ko ba ta da aure. Haka ma idan auren ya mutu ta hanyar saki na
ƙarshe wanda babu kome a cikinsa. Namiji ɗaya ne ya halatta mace ta saki jiki
da shi su yi wasa ko da ma zai kai ga saduwa, shi ne: Mijin da aka ɗaura musu
sahihin aure a ƙarƙashin dokokin Shari’ar Musulunci.
A bayan saki, ko shi mijin ma ba a yarda ta bari ya kusance
ta ba a lokacin da take cikin iddar da ta ke akwai kome a cikinta, watau saki
na-ɗaya ko na-biyu. Sai dai idan hakan da manufar yin kome ne, to wannan daidai
ne, babu laifin komai. Yin hakan ma dalili ne a kan cewa ya dawo da ita, kamar
yadda malamai suka faɗa.
Matar da take cikin iddar saki na-ɗaya ko na-biyu bai
halatta wani ya nemi aurenta da kalmomin neman aure a fili ƙarara ba. Haka ma a
ɓoye ta amfani da kalmomin jirwaye-da-kamar-wanka. Saboda akwai sauran haƙƙin
mijinta a kanta, watau na yin kome a duk sadda ya ga dama.
Don haka bai halatta ba macen da take cikin irin wannan
halin ta saki jiki har wani ya yi wasan jin daɗi da ita. Ko ba komai, idan da
mijinta zai mutu a wannan lokacin to da kuwa iddar ta juye ta koma ta mutuwa,
kuma da takaba ta hau kanta.
Wajibi ne ga macen da ta yi hakan ta tuba ga Allaah
Ubangijin Halittu a kan hakan da sharuɗɗan da malamai suka shimfiɗa.
Amma idan a wannan halin saduwa ta auku a tsakaninta da
abokin wasan da ba mijinta ba, ko da kuwa maniyyi bai fita wa ɗayansu ba, to ta
lalata iddar tata kenan. Kuma sai ta faro ta daga farko bayan ta yi istibra’in
da ya wajaba a saboda wannan saduwar. Waɗansu malaman su yarda wannan ce mafita
gare ta a bayan tuba da istigfari.
Allaah ya ƙara mana shiriya. Ya sa mu iya kafewa a kan
dokokinsa.
WALLAHU A'ALAM
Shiekh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.