Ya Ƙaro Wani Aure Alhali Matarsa Ta 4 Da Ya Saka Tana Cikin Idda

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Menene hukuncin wanda ya saki daya daga cikin Matansa guda-4 amma kafin tagama idda sai yakara auro wata Matar dabam??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Idan ya kasance Matar da ya saka ɗin dama Sakine irin na Kōme, to dukkan Malamai Sunyi Ijma'i akan-cewa duk Matar da aka Saketa irin Sakin-Kōme to tana nan a matsayin Matar-Mutum har zuwa lokacin da zata ƙare Iddarta, danhaka kenan idan Mutum yana da Mata-4 sai ya Saki ɗaya daga cikinsu kuma irin Sakin-Kōme, to  ananma Malamai Sunyi Ittifaƙin cewa bai Halattaba yaje yaƙaro wani auren alhali Matarsa ta-4 da yasaka tana cikin idda bata ​ƙareba, domin idan ya yi haka tamkar yahaɗa Matan-Aurene guda-5 alokaci ɗaya, wanda yin hakan kuma dukkan Malamai sunyi Ijma'i akan cewa haramunne

An naƙalto cewa Babban Tabi'in nan Mai Suna (عبيدة السلماني) yana cewa, Babu wani Ittifaƙi Mai-Ƙarfi da Sahabban Mαnzon Aʟʟaн(Sallallahu alaihi Wasallam) sukayi akan wata Mas'ala ta Addini da yakai Ittifaƙin da sukayi akan cewa Bai Halattaba Mutum ya auro Mace ta biyar alhali Matarsa ta huɗu da ya Saki bata gama iddaba, kokuma Mutum ya auro ​Ƴar'uwar Matarsa (Yayarta ko Ƙanwarta) da yasaka kafin taƙare idda, Dukkan Mutumin dayayi haka kuwa, to ko Shakka Babu Cewa ya Saɓawa Littafin Aʟʟaн() dakuma Sunnar Mαnzon Aʟʟaн(Sallallahu alaihi Wasallam) danhaka idan har anriga anɗaura wannan aure to Hukuncinsa a Shari'a sunansa ​Ɓataccen aure kawai akayi, danhaka wajibine yarabu da wannan Mata (tabiyar) harsai Matarsa (tahuɗu) ta gama iddarta, idan kuma yariga yasadu da'ita to shikenan Zai bata Sadaƙinta Cikakke, Sannan kuma zataje tayi idda, bayan tagama kuma sai asake Sabon Ɗaurin AuAur.

Amma idan yakasance Sakin da ya yiwa Matarsa (tahuɗu) dama Sakine (Ba'ini) Manisanci wanda ba irin na komeba kamar saki uku, to anan sai Malamai sukayi Saɓani akai, Mazhabin Hanabila da  Hanafiyya sukatafi akan-cewa ai koda Saki ukune Miji ya yiwa Matarsa (tahuɗu) to bai halatta ya auro Mace (ta biyarba) dole sai in Matarsa (tahuɗu) tagama idda, amma inda ace Mutuwace Matar tayi to ya halatta nantake yasake auro wata Matar, Saidai kuma Mazhabin Malikiyya da Shafi'iyya sukace indai  Sakine manisanci (Ba'ini) ya yi mata wanda ba sakin komeba, to ya halatta agareshi ya auro Mace tabiyar koda kuwa ta huɗun batagama iiddartaba.

Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:​​

"مواهب الجليل" (4/140)

"المغني لإبن قدامة" (7/104)

"فتاوي اللجنة الدائمة" (2/641)

​​шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαм

​​

              ​​AMSAWA

           Mυѕтαρнα Uѕмαn

              08032531505

​​

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇 https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments