Ticker

Yadda Ake Awara (Kwai-Da-Kwai) Da Tubani Da Danwake

Yadda Ake Awaran Waken Suya / Ƙ wai-Da- Ƙ wai

Kayan haɗin da za a tanada su ne:

i. Albasa

ii. Attarugu

iii. Kabeji

iv. Karas

v. Nama

vi. Ruwan Tsami

vii. Waken soya

Za a jiƙa waken suya, idan ya jiƙu sai a kai niƙa. Bayan an dawo da shi daga niƙa, za a ɗan ɗiga manja a ciki a ɗan ƙara ruwa sai a tace. Za a zuba ruwa a tukunya  a ɗora a wuta , ana kula da ruwan awarar da aka ɗora kan wuta. Yayin da ya fara tafasa, sai a ɗauko ruwan tsami  a zuba a ciki. A nan za a ga duk ya haɗe ya riƙa tasowa sama. To ƙullun da ke tasowa shi ne awara. Za a riƙa kwashewa ana zubawa a ƙyallen tata. Bugu da ƙ ari, za a riƙa kwashewa ana zuba ruwan sanyi a ciki.

A gefe guda kuwa, za a jajjaga tarugu da albasa  da kayan yaji a aza tukunya  saman wuta  a zuba mai da albasa tare da jajjagen da kuma ɗan magi, sai soyawa sama-sama. Daga nan sai a yanka kabeji da karas ƙanana, a aje gefe sai a sake zuba mai. A kuma samu magi da gishiri a zuba a cikin awara a murje ciki kafin a soya. Idan an soya, sai a ɗauko soyayyen jajjagen da man da ke ciki da kabeji da karas a zuba. In da hali za a tafasa nama da albasa da magi a soya su a haɗa da awara a ci tare.

Yadda Ake Tubani

Kayan haɗin da za a tanada su ne:

a. Wake

b. Kanwa

c. Rogo

d. Kuka

e. Ganyen rogo ko na masara

Za a niƙa wake  a tankaɗe a saka garin kuka  kaɗan a kwaɓa da ruwan kanwa. Sannan za a wanke  ganyen , idan ganyen ya bushe, sai a riƙa zuba wannan  kwaɓin da aka yi bisa ganyen ana naɗewa. Bayan an kamala, sai maganar sanyawa cikin tukunya  bisa wuta .

Yadda Ake Ɗanwake

Kayan haɗin da za a tanada su ne:

i. Fulawa ko alabo da wake da dawa

ii. Kanwa

iii. Kayan lambu

iv. Kayan ɗanɗano

v. Kuka

vi. Mai

vii. Ruwa

Akwai ɗanwaken da ake yi ta hanyar haɗa wake  da dawa  da alabo, [1] wanda amfanin da ake yi da wake ne ma ya sa ake ce masa ɗanwake. Bayan an haɗa waɗannan kayayyaki, za a sanya musu kuka  kaɗan sannan a kai niƙa. Za a tankaɗe su bayan an dawo daga niƙa. Za a iya kai niƙa ba tare da an sanya kuka ba. Idan haka ta faru, to za a sanya tankaɗaɗɗen garin kuka bayan an dawo daga niƙa. Daga nan kuma za a kwaɓa wannan  gari  tare da ruwan jiƙaƙƙiyar kanwa ba mai yawa ba. kwaɓaɓɓen garin zai kasance mai danƙo.

A gefe guda kuwa, za a ɗora ruwa bisa wuta . Bayan ya tafasa, za a riƙa ɗiban wannnan kwaɓaɓɓen garin ɗanwake ana sanyawa ƙanana- ƙanana a cikin ruwan. Ana amfani da hanu ko cokali domin yin hakan. Bayan an saka daidai adadin da tukunyar za ta iya ɗauka, sai a bar ta haka nan. Ɗanwaken zai riƙa samar da wani kumfa yayin da ruwan ke tafasa. Za a riƙa amfani da ludayi da ruwan sanyi kaɗan domin mayar da wannan  kumfa da ke tasowa.

Yadda ake gane ɗanwake ya nuna shi ne, idan aka ɗauka aka sanya cikin ruwan sanyi, to zai koma ƙasa. Wanda bai nuna ba kuwa, zai zauna a saman ruwa.

Ana cin ɗan wake  da mai da kayan ɗanɗano. Sannan ana iya yanka kayan lambu a sama. Wani lokaci ma akan ci shi da jar miya  ko miyar gyaɗa . A zamanin yau kuwa, ana amfani da fulawa a maimakon waɗannan.

 



[1] Rogo  da aka yayyanka aka shanya ya bushe. 

Citation (Manazartar Littafin):   Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments