Tambaya (72)❓
Duk sanda na
karanta Qulhuwallahu ahad sau 10 a jere, Allah SWT zai gina min gida a cikin
Aljannah ko zan iya karanta sama da sau 10 don samun gidajen da yawa
AMSA❗
Alhamdulillah
Shahararren
Tabi'in nan Sa'id ibnul Musayyab (Rahimahullah) ya karbo hadisi mursal cewar
Annabi SAW yace: "Duk wanda ya karanta Qulhuwallahu ahad sau 10 a jere,
Allah SWT zai gina masa katafaren gidan bene a cikin Aljannah. Idan ka karanta
20, gidaje 2, ka karanta 30 gidaje 3
Sayyadina Umar RA
yace: "Na rantse da Allah! Indai hakane to zamu samu gidajen bene da yawa
tunda zamu yawaita karantawa
Sai Annabi SAW
yace: "Fallahu akhsar" ma'ana: "Allah shi ne mai yawaitawa"
Abin nufi shi ne
Allah SWT bazai gaji da gina muku gidajen ba matuqar zaku yawaita karantawa
(Sunan Darimi
hadisi mai lambata 3429)
Hafizh Ibn
Khathir (Rahimahullah) yace: wannan hadisi ne mursalin jayyid (mai kyau)
(Duba Suratul
Ikhas a cikin Tafsir na Ibn Khathir)
(Muhammad
Abusoomar ya taba amsa makamanciyar wannan tambayar)
Haka kuma an
karbo hadisi daga Abu Hurairah RA yace: Annabi SAW yaji wani mutum yana karanta
Qulhuwallahu ahad sai yace: "gaskiyar sa ce"
Sahabbai suka ce:
Ya ma'aikin Allah, mene ne gaskiyar ta sa ?
Sai yace (SAW):
"Aljannah ce gaskiyar ta sa"
(Musnad Imam
Ahmad 7669)
Annabi SAW yace:
"Duk wanda ya karanta Qulhuwallahu ahad sau 10 a jere, Allah SWT zai gina
masa katafaren gidan bene a cikin Aljannah"
(Sahih al-Jami'
al-Saghir, 6472 na Muhammad Nasiriddin albany)
A shawarce, duk
wanda ya karanta wannan hadisi to ya dinga aiki dashi - idan kai malami ne to
sai ka tara dalibanka ka ce su dinga karantawa sau 10 a jere, idan mahaifiyace
to sai itama ta tara yayanta waje guda su karanta a tare kuma a jere, hakama
mahaifi. Gidan haya kuke zama a matsayin mata da miji to ku lizamci wannan
bonanza don samun babban rabo, kada ayi biyu babu
Kuma duk wanda ya
koyawa wani to yana da ladan wani gidan daban ba tare da an tauyewa wanda aka
koyawa haqqinsa ba kamar yanda ya tabbata a cikin sahihin hadisi. Allahu Akbar!
Wallahi babu wani Attajiri a duniyarnan da ya isa ya baka wani abu kwatankwacin
wannan
Aljannnah gaskiya
ce. Tananan yanzu haka, an tanade ta ga masu rabo. Mu'ujizozin Qur'ani kadai
sun isa sun tabbatar mana samuwar Aljannah
A shekarun baya akwai wani lokacin damuna muna zaune tare da yan uwa a
makarantar Nurul Hayat Islamiyya dake anguwanmu, ina cikin karatun Qur'ani ina
karanta daidai ayata 26 cikin Suratu Yunus inda Allah SWT yake cewa;
( لِّلَّذِينَ
أَحْسَنُوا الْحُسْنَىٰ وَزِيَادَةٌ ۖ وَلَا يَرْهَقُ وُجُوهَهُمْ قَتَرٌ وَلَا
ذِلَّةٌ ۚ أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ )
يونس (26) Yunus
Waɗanda suka kyautata yi, suna
da abu mai kyawo kuma da ƙari, wata ƙura ba ta rufe
fuskokinsu, kuma haka wani ƙasƙanci. waɗancan ne abokan Aljanna, suna madawwama a cikinta.
Anan take sai
qurar iska ta taso ta lullube fuskokinmu gaba daya, kasa ta shigarwa wasunmu
ido, masu furzar da kasar nayi, tuf! tuf! mutane na ta kakkabe fuskokinsu
Nace Allahu
Akbar! Sadaqallahul Azim
Anan naga
mu'ujizar Qur'ani qarara, na nunawa yan uwa da muke tare daidai wannan ayar,
mukaita fata da roqon Allah Azzawajallah ya sakamu cikin Aljannah gidan dawwama
inda qura ba ta rufe fuskoki wadda fadin Aljannar musulmi daya tak yakai girman
sammai bakwai da kassai bakwai kamar yanda Allah SWT ya fada;
( وَسَارِعُوا
إِلَىٰ مَغْفِرَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا السَّمَاوَاتُ وَالْأَرْضُ
أُعِدَّتْ لِلْمُتَّقِينَ )
آل
عمران (133)
Aal-Imran
Kuma ku yi
gaugawa zuwa ga neman gafara daga Ubangijinku da wata Aljanna wadda faɗinta (dai dai da) sammai da ƙasa ne, an yi tattalinta domin masu taƙawa.
Allahu Akbar! A
dan karamin sanin da Allah SWT ya bani na bangaren ilimin kimiyyar sararin
samaniya (Astronomy) wannan ayar ita ce tafi kowacce dauremin kai la'akari da
ana auna girman sama ne da gudun haske wanda a kowanne second daya haske yana
gudun kilometers 300,000 ne kuma akwai inda kafin haske ya je sai ya share sama
da shekaru trillions, quadrillions, octillions ko zillions ko ma sama da haka
kuma duk magana ake ta lebatun sama ta farko ballantana ta biyu har zuwa ta
bakwai. To indai har fadin gidan mutum daya a Aljannah zai yi daidai da sammai
bakwai da kassai bakwai to ina kuma ga tsayin gidan, tunda a al'adance tsayi
yafi fadi
Wallahu ta'ala
a'alam
Ya Allah ka
sakamu a cikin Aljannatil Firdous don rahamarka ba don halayenmu ba
Subhanakallahumma
wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa;
Usman Danliti
Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi
Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.