Shi: "Malam za a iya ɗaura mini aure ta Zoom online a kan intanet daga wata ƙasa?"
Barkwanci...
Musa: "Mutumin, ga ni fa na shigo Katsina. Na ga snow na sauƙa."🌧️💦
Audu: "Baabaa, hayaƙin sigari ne."🚬🚬
Kina cikin kallon LABARINA🎬 sai mijinki ya ɗauki remote ya kamo tashar kallon ƙwallo.⚽ Yana zama sai aka ɗauke NEPA.💡 Baitin wace waƙa za ki rera? 😂
Barkwanci...
Da a saka ka kula da mai suna Maryam,🧕 gwara a ba ka kiwon 'ya'yan aljanu uku.😈👹🤡
Barkwanci...
Abin alfahari ne a gare ki 'yan mata su nuna suna son auren mijinki. Hakan na nuni da cewa kin auri mijin ƙwarai. 👳♂️
Barkwanci...
Idan aka lura, ayyukan gida na yi wa mace yawa. Duk namiji mai tausayi zai yi ƙoƙarin samo wa matarsa abokiyar zama 🧕🧕domin tausayawa. 👨🦯
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.