Ticker

Zan Iya Rokon Allah Ya Ba Ni Mahassada, Amma Ya Yi Min Maganinsu ?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmtullahi. Malam zan iya addu'a kamar haka : "Allah Ka ba ni mahassada ka raba mu da sharrinsu?"

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam Ka yi wata addu'ar  daban zai fi. A aya ta karshe a Suratul Falak Allah Ya umarci masoyinsa da neman tsari daga sharrin Mai hassada

وَمِن شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ

Da sharrin mai hasada idan ya yi hasada. (Suratul Falak aya 5)

Wani mai hassadar in ya kalleka za ka iya lalacewa ko kuma lamuranka su tabarbare, ko ya tunkudaka kabari kafin ka shirya, saboda wata hassadar kunshe take da kambun baka, Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) yana cewa a hadisin da Muslim ya rawaito (2188) "Kambun baka gaskiya ne, inda akwai abin da zai riga kaddara, da kambun baka ya sha gabanta.

A hadisin da Munawi ya ambata a Faidhul kadir, Albani kuma ya inganta a Sahiha (1249), Manzon Tsira yana cewa; "Kambun baka yana shigar da rakumi tukunya a cinye shi, yana kai mutum cikin kabari, saboda ya kwanta dama" .

Ibnul kayyim yana cewa a littafinsa Igasatul lahfaan: "Duk Mai kambun baka mahassadi ne, amma ba duk mahassadi ba ne yake da kambun baka"

Allah Ne Mafi sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/K7RkQRMf2b57l3UENoJ1Or

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments