Abubuwan Da Za A Iya Fasa Aure Saboda Su.

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, ina rokon Malam bayani kan hukuncin wanda aka sanya ma ranar aure kafin lokacin ya ce ya fasa.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, in har akwai hujjar da Shari'a ta yarda da ita, ba shi da laifi in ya fasa. Kamar ya bayyana cewa budurwar tasa ba ta da tarbiyya ko mazinaciya ce, ko kuma ba ta son shi, ko tana da cutar da za ta hana a sadu da ita, kamar toshewar farji ko hadewarsa da dubura, ko ya zama su duka suna da jinin da in sun haɗu za su haifi sikila, yana iya fasa auren idan ya zama ba shi da halin da zai iya ciyar da ita, ko kuma likita ya tabbatar masa ba shi da mazakutar da zai iya saduwa da mace, haka ma idan yaji ya tsaneta. Dukkan abin da ake iya saki saboda shi, ana iya fasa aure in aka same shi.

Allah ne mafi sani.

Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments