TAMBAYA (73)❓
Don Allah mene ne alaqar dake tsakanin hadisin fitowar rana
daga yamma da binciken da masana ilimin kimiyya sukai akan abinda ke faruwa a
tsakiyar kasan duniyarmu
AMSA❗
Alhmdulillah
Hadisin yana cikin Sahih Muslim wanda aka karbo daga Abu
Hurairah RA ya ce: Annabi SAW ya ce: "Duk wanda ya tuba ga Allah kafin
rana ta fito daga mafadarta (yamma) to Allah zai karbi tubansa"
Hadisin yana bayyana cewar duk bawan da yayi taubatun nasuha
ya koma ga Allah kafin rana ta fito daga yamma ta fadi a gabas to Allah SWT zai
karbi tubansa saboda idan har ranar ta fito daga mafadarta to tabbas wannan
ranar itace ranar karshe wato ranar tashin alqiyama
Hadisin, kamar yanda malamai suka ce yanada alaqa da
binciken da kungiyar da take da alhakin tura masana zuwa sararin samaniya
(space) mai suna National Aeronautic and Space Administration (NASA), gidan TV
na CNN, Geographers (masana taswirar kasashe), Geologists (masana dutsuna),
Oceanographers (masana teku) Geophysicist (masana dabi'un kasa) sukayi akan
abinda ke faruwa acan karkashin kasa (earth's core) kimanin tafiyar kilometers
2,900 kacal
Abune sananne a cikin Qur'ani mai girma cewar sammai guda 7
ne hakama kassai guda 7 ne
(أَلَمْ
تَرَ أَنَّ اللَّهَ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ بِالْحَقِّ ۚ إِن يَشَأْ يُذْهِبْكُمْ
وَيَأْتِ بِخَلْقٍ جَدِيدٍ )
إبراهيم
(19) Ibrahim
Shin, ba ka gani ba cẽwa lalle ne Allah Ya halicci sammai
bakwai da ƙasa
da mallakarSa. Idan Ya
so zai tafiyar da ku, kuma Ya zo da wata halitta sabuwa.
Kuma komai a cikinsu tasbihi yake ga Allah Mdaukakin Sarki
(تُسَبِّحُ
لَهُ السَّمَاوَاتُ السَّبْعُ وَالْأَرْضُ وَمَن فِيهِنَّ ۚ وَإِن مِّن شَيْءٍ إِلَّا
يُسَبِّحُ بِحَمْدِهِ وَلَٰكِن لَّا تَفْقَهُونَ تَسْبِيحَهُمْ ۗ إِنَّهُ كَانَ حَلِيمًا
غَفُورًا )
الإسراء
(44) Al-Israa
Sammai bakwai da ƙasa da wanda yake a cikinsu suna yi Masa tasbĩhi. Kuma babu wani abu face yana tasbĩhi game da gode Masa, kuma amma ba ku
fahimtar tasbĩhinsu.
Lalle ne shĩ, Ya
kasance Mai haƙuri ne, Mai gafara.
Akwai kuma wasu sammai guda bakwai da suke a saman duniyarmu
wadanda ake kira da; Exosphere, Mesosphere, Stratosphere, Troposphere,
Thermosphere, Ionosphere da kuma Atmosphere dukkansu suna bada gudunmawa gameda
rayuwar dan Adam da tsirrai da dabbobi. Kwanannan National Geographic suka
fitar da bayanai na ilimi akan cewar akwai wasu layers a kasan duniyarmu guda 4
wato; crust, mantle, solid outer core sai kuma Inner core
Shi wancan Inner core (tsakiyar duniya) din shi ne wanda
Prof. Michau Kaku ya ce: "Oh my God ! Core din duniyarmu ya tsaya cak kuma
zai fara juyawa da baya da baya sabanin yanda ya saba"
Stephen Hawkins a cikin littafinsa mai suna: "The Brief
History Of Time" (Taqaitaccen tarihin lokaci) yayi tsokaci akan abinda ya
shafi juyawar earth's core wanda ake kira da retrograde motion wato juyawar
duniya anticlockwise
Abinda ya basu mamaki shi ne, a yanzu haka duniyoyin da suke
a anguwar rana (as-Shams) sun fara juyawa sabanin yanda suka saba ma'ana
duniyar Neptune, Uranus, Saturn, Jupiter, Mars dukkansu rana tana bullowa ne
daga Yammaci sannan ta fadi a Gabashi kuma yanzu haka duniyarmu ta Earth itace
makociyar Mars ke nan (Duniyar da turawa suke son komawa da zama nan da
shekarar 2026) nan da wani lokaci kadan muma zamu wayi gari mu ga bullowar rana
daga mafadarta, tashin alqiyama ke nan !
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un !
Kwanakin baya jaridar "The Guardian" ta wallafa
maganar wani Geophysicist daga British Geological Survey mai suna Ciaran
Beggan, ya ce: "Duniya ta sauya tafiyarta daga matakin kilometers 10 (6
miles) zuwa kilometers 50 ko 60 a duk shekara. A yanzu haka tana gudu ne tana
dosar yankin (direction) din kasar Siberia"
A yanzu haka ba kowa bane yasan da wannan bincike da akayi
duk da cewar a zahiri mu kanmu mukance kalli fa yanda shekara take sauri, wata
yake hanzarin karewa, sati yake gudu, mun manta da cewar duk wannan fa kananan
alamomi ne na tashin alqiyama kuma mu musulmai a wajenmu ba abin mamaki bane ba
domin kuwa sama da shekaru 1,400 baya Annabinmu SAW ya sanar da mu cewar
shekara za ta koma kamar wata, yayinda wata zai koma kamar sati, satin kuma
kamar kwana daya, sannan kuma rana za ta hudo ta mafadarta ma'ana daga Yamma za
ta fadi a Gabas, daganan kuma shike nan rana ta daina aikinta na samar da haske
ga halittun Allah SWT
Me na shiryawa zuwan wannan ranar?
Me ka shirya?
Me kika tanada?
Sai yaushe zamu koma ga Allah ne?
Amsar ta rage ga mai karatu
A yanzu ne tunanin canzawa zai amfani bawa, bawai sanda yaga
Jahannama a zahiri ba kamar yanda Allah SWT ya fada;
(وَجِيءَ
يَوْمَئِذٍ بِجَهَنَّمَ ۚ يَوْمَئِذٍ يَتَذَكَّرُ الْإِنسَانُ وَأَنَّىٰ لَهُ الذِّكْرَىٰ
)
الفجر
(23) Al-Fajr
Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai
yi tunani. To, ina fa tunani yake a gare shi!
Fatana shi ne wancan hadisi da kuma wannan bincike da masana
ilimi sukai ya kara nusar damu akan yawaita Istighfari kafin a rufe kofar tuba
(lokacin da za a ga fitowar rana daga mafadarta)
A maimakon mu dinga yawan cece-kuce akan yanayin da muka
tsinci kanmu na tsadar rayuwa, kamata yayi mu koma ga Allah SWT ta hanyar yin
taubatun nasuha tunda wadanda suka gabacemu ma sai da Allah SWT ya jarabcesu
kamar yanda ya fada a cikin Qur'ani mai girma;
(أَمْ
حَسِبْتُمْ أَن تَدْخُلُوا الْجَنَّةَ وَلَمَّا يَأْتِكُم مَّثَلُ الَّذِينَ خَلَوْا
مِن قَبْلِكُم ۖ مَّسَّتْهُمُ الْبَأْسَاءُ وَالضَّرَّاءُ وَزُلْزِلُوا حَتَّىٰ يَقُولَ
الرَّسُولُ وَالَّذِينَ آمَنُوا مَعَهُ مَتَىٰ نَصْرُ اللَّهِ ۗ أَلَا إِنَّ نَصْرَ
اللَّهِ قَرِيبٌ )
البقرة
(214) Al-Baqara
Ko kuna zaton ku shiga Aljanna kuma tun misalin waɗanda suka shige daga gabaninku
bai zo muku ba? Wahaloli da cũta sun shafe su, kuma aka tsoratar da su har
manzonsu da waɗanda
suka yi ĩmani tare da shi su ce: "Yaushe taimakon Allah zai zo?" To!
Lalle ne, taimakon Allah yana kusa!
Kamata yayi mu hanzarta neman yafiyar wadanda muka sabawa
kuma muyi gaggawar aikata ayyukan alkhairi da neman tuba kamar yanda Allah
Azzawajallah ya fada;
(وَسَارِعُوا إِلَىٰ مَغْفِرَةٍ
مِّن رَّبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا السَّمَاوَاتُ وَالْأَرْضُ أُعِدَّتْ لِلْمُتَّقِينَ
)
آل عمران
(133) Aal-Imran
Kuma ku yi gaugawa zuwa ga nẽman gafara daga Ubangijinku da wata
Aljanna wadda faɗinta
(dai dai da) sammai da ƙasa ne, an yi tattalinta domin masu
taƙawa.
Masu aikata alfashi a gaggauta tuba a tuno da matan Hurul
Ayn wadanda Allah SWT zai aurar ga duk mai imani kamar yanda ya fada;
(وَالَّذِينَ
آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ سَنُدْخِلُهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ
خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ۖ لَّهُمْ فِيهَا أَزْوَاجٌ مُّطَهَّرَةٌ ۖ وَنُدْخِلُهُمْ
ظِلًّا ظَلِيلًا )
النساء
(57) An-Nisaa
Kuma waɗanda
suka yi imani, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, za Mu shigar da su gidajen Aljanna, (waɗanda)
ƙoramu suna gudana daga ƙarƙashinsu, suna dawwamammu a cikinsu har abada suna da, a cikinsu, matan aure masu tsarki, Kuma Muna shigar da su a wata inuwa
matabbaciyar lumshi.
(وَلَقَدْ
ذَرَأْنَا لِجَهَنَّمَ كَثِيرًا مِّنَ الْجِنِّ وَالْإِنسِ ۖ لَهُمْ قُلُوبٌ لَّا يَفْقَهُونَ
بِهَا وَلَهُمْ أَعْيُنٌ لَّا يُبْصِرُونَ بِهَا وَلَهُمْ آذَانٌ لَّا يَسْمَعُونَ
بِهَا ۚ أُولَٰئِكَ كَالْأَنْعَامِ بَلْ هُمْ أَضَلُّ ۚ أُولَٰئِكَ هُمُ الْغَافِلُونَ
)
الأعراف
(179) Al-A'raaf
Kada mu fada tarkon shaidan mu yanke Rahamar Allah kamar
yanda Elon Musk (Mai kamfanin Twitter da SpaceX, kuma mutum na 2 wanda yafi
kowa kudi a duniya) wanda Shaikh Muhammad yayi masa tayin karbar addinin
musulunci saboda yanda yake ganin ayoyin Allah a sararin samaniya a matsayinsa
na masanin kimiyya, amman Elon Musk da ya tashi sai yayi masa reply da cewar ya
gode da tayin da yayi masa amman ya zabi ya shiga wutar Jahannama da ya karbi
musulunci wai saboda yaji cewar ma ai mutane sunfi yawa a wutar, hujjarsa itace
ayarnan;
(وَلَقَدْ
ذَرَأْنَا لِجَهَنَّمَ كَثِيرًا مِّنَ الْجِنِّ وَالْإِنسِ ۖ لَهُمْ قُلُوبٌ لَّا يَفْقَهُونَ
بِهَا وَلَهُمْ أَعْيُنٌ لَّا يُبْصِرُونَ بِهَا وَلَهُمْ آذَانٌ لَّا يَسْمَعُونَ
بِهَا ۚ أُولَٰئِكَ كَالْأَنْعَامِ بَلْ هُمْ أَضَلُّ ۚ أُولَٰئِكَ هُمُ الْغَافِلُونَ
)
الأعراف
(179) Al-A'raaf
Kuma lalle ne, haƙĩƙa,
Mun halitta saboda
Jahannama, masu yawa
daga aljannu da mutane,
suna da zukata, ba su fahimta da su,
kuma suna da idanu, ba su gani da su, kuma suna da kunnuwa, ba su ji da
su; waɗancan kamar
bisashe suke. A'a, sũ ne mafi ɓacẽwa;
Waɗancan sũ ne
gafalallu.
To anan gabar ne fa yakamata mu tuno da wannan sahihin
hadisin da Annabi SAW ya ce: "Da ace duniyarnan tana da darajar fiffiken
sauro a wajen Allah SWT da kafiri bai sha ruwa a cikinta ba"
Haka siddan zakaga mutane ba sa son musulunci, kamardai wani
Christian wanda mukai karatu a department din Microbiology dake Jami'ar Bayero
ta Kano wanda nayi masa tayin shiga musulunci yacemin ko da ace mutanen duniya
gaba daya zasu shiga musulunci to shi ba zai musulunta ba. Sai na tuno da
"Wanda Allah ya batar ba wanda ya isa ya shiryar dashi hakama wanda ya
shiryar ba wanda ya isa ya batar dashi. Fatana shi ne Allah ya shiryar da
wancan Trinitarian din
Kagadai Elon Musk shi ne na 2 a kudi a duk duniya kamar
yanda Forbes suka wallafa to ammanfa kaga bashi da imani kai kuma ga ka kana
karanta wannan saqon amman ko Naira miliyan daya bakada ita a cikin aljihunka
ko account dinki to indai kina yin sallah akan lokaci kuma kina kiyaye dokokin
Allah mastada' to hakan na nufin kin fi Elon Musk a wajen Allah Al-Azizu
Wallahu ta'ala a'alam
Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa
anta, astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa;
Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.