Aro Da Kwaskwarima a Wasu Sunayen ‘Yan Ta’adda a Arewa Maso Yammacin Nijeriya

Citation: Sarkin Fada, I. & Abdullahi, M. (2024). Aro Da Kwaskwarima a Wasu Sunayen ‘yanta’adda a Arewa Maso Yammacin Nijeriya. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 249-256. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.028.

Aro Da Kwaskwarima a Wasu Sunayen Yan Ta’adda a Arewa Maso Yammacin Nijeriya

Daga

Isah Sarkin Fada
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau
PHONE NO: 08039165872
isahsarkinfada@gmail.com

Da

Musa Abdullahi
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau
PHONE NO: 08037765415

Tsakure

Harshe yana samun sauye-sauye ta hanyar bun ƙ asa da fa ɗ a ɗ a da kuma samun ba ƙ in al’amurra cikinsa da sukan faru lokaci-lokaci. Wannan ma ƙ ala mai taken Nazarin Ƙ ir ƙ ira da Ma anar Wasu Sunayen ‘Yan Ta’adda ta Hanyar Aro da Kwaskwarima a Arewa Maso Yammacin Nijeriya’ ma ƙ ala ce da ta yi nazarin bun ƙ asar harshen Hausa da aka samu dalilin ayyukan masu ta addanci a wasu yankunan Arewa maso Yammacin Nijeriya. Ma ƙ alar ta yi ƙ o ƙ arin fitowa da wasu sababbin sunayen da yan ta adda suke kiran kansu da su wa ɗ anda suka ƙ ir ƙ ira wa kansu domin amfani da su wajen sadarwarsu ta yau da kullum da kuma wasu sunaye da mutane suke kiran su da su. Manufar ma ƙ alar ita ce, tabbatar da bun ƙ asar da harshen Hausa ya samu a dalilin ayyukan yan ta adda ta hanyar samar da ƙ ir ƙ irarrin sunaye na gama-gari da ake kiran su da su da kuma sunayen da suke la ƙ aba wa kansu da kuma sunayen da ake yi masu. An yi amfani da ra’in ‘Dangantakar Harshe da Rikici’ (Language of Violence) na Smith, Alison G. da wasu (2008), wajen gudanar da wannan bincike wanda yake magana a kan sadarwa tsakanin ‘yan ta’adda da wa ɗ anda ke ya ƙ ar su. Ra in ya nuna cewa, idan aka yi la akari da kalmomin da ɓ angarorin biyu ke furtawa, to akwai abubuwan da ake samarwa dangane da harshe da bun ƙ asarsa. Daga cikin dabarun da aka yi amfani da su wajen tattara bayanan da aka rubuta wannan ma ƙ alar akwai; tattaunawa da yan ta adda da suka tuba da mutanen da aka yi garkuwa da su domin neman ku ɗ in fansa, amma daga baya suka samu ‘yanci, da ‘yan jarida da wasu ɗ ai ɗ aikun mutane da ayyukan ta’addanci suke aukawa a cikin yankunansu. Haka kuma, an yi amfani da sunayen da ake ji na ‘yan ta’adda a kafafen sadarwa da kuma kafafen rediyo da talabijin da jaridu da mujallu na intanet.

1.0 Gabatarwa

Harshe wata kafa ce ta ƙ ulla dangantaka tsakanin mutane musamman wajen mu amala da zamantakewa. Harshe yana amfani wajen isar da sa ƙ o daga wani mutum zuwa wani, da kuma gudanar da wasu muhimman abubuwa. Har wa yau, harshe ya kasance wata makaranta domin hani da horo ga al’umma a kan wasu al’amurra. Galadanci da wasu (2005, p. 6) sana cewa, ‘harshe yana nufin hanyar sadar da manufa tsakanin al’umma. Wato harshen kowace al’umma shi ne hanyar hul ɗ arsu ta wajen sadarwa’. Bugu da ƙ ari, harshe yana ƙ unshe da wa ɗ ansu siffofi wa ɗ anda ake iya gane shi da su, . Wa ɗ annan siffofi kuwa sun ha ɗ a da: Ƙ ir ƙ ira domin samar da sababbin kalmomi da tsari da koyo da yalwa da ƙ warewa da kuma daidaito. Babban aikin harshe ga al umma shi ne sadarwa tsakanin al umma.

A ɓ angaren al’umma kuwa, Yakasai (2020, p. 51) ya bayyana cewa: ‘Al’umma ita ce, tarin ɗ ai ɗ aikun mutane da suke zaune a gari guda, ko yanki ko lardi ko jiha ko ƙ asa . Al umma tana iya kasancewa ha ɗ akar ƙ abilu daban-daban. Wannan yana nuna cewa duk lokacin da aka sami fiye da mutum guda, to lalurar hul ɗ a da mu’amala takan kama. Hul ɗ a da mu’amala kuwa ba su cika, ba tare da al’umma ba. Amfani da harshe tilas ne, a wajen hul ɗ a, kuma lalura ce. Saboda haka, harshe ya zama kanwa uwar gami ga dukkan al’amurran rayuwar ɗ an-Adam.

Haka kuma, rukunin jama’a ya ƙ unshi mutane da suka yi tarayyar ala ƙ a ta fuskar zamantakewa wuri guda. Duk da yake ɗ ai ɗ aikun mutane kan bambanta da juna ta hanyar magana, amma ana iya samun Hausar rukuni dalilin tarayyar aiki ko matsayi ko jinsi ko jama’a ko addini ko samun matakin ilmi iri ɗ aya. Nazarin harshen ta’addanci wani fanni ne da ke ƙ ar ƙ ashin ilmin walwalar harshe, amma kuma wanda bai samu ranar shanya daga wajen masana ba. Harshen ta addanci wani ɓ angare ne da yake bayar da gudummuwa sosai wajen bun ƙ asa harshen Hausa. Yan ta adda fan ɗ ararrun mutane ne da suka killace kansu wuri ɗ aya a daji, ba su son mu’amala a cikin al’umma. Saboda haka, kasancewa sun yi gungu wuri ɗ aya, kuma suna gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum, to a mahangar masana ilmin walwalar harshe babu mamaki su samar da wata Hausa ta daban wadda ta ke ɓ anta da su da ta sha bamban da sauran rukunin jama’a.

Ma ƙ alar za ta mayar da hankali ne ga yadda ake ƙ era kalmomin sunayen masu ayyukan ta addanci a harshen Hausa da kuma ma anar sunayen a nahawu. Har wa yau kuma, ma ƙ alar ta yi ƙ o ƙ arin kawo ma anar ƙ irar kalma a fahimtar masana. Bugu da ƙ ari, an kuma kawo hanyoyin ƙ irar kalma.

2.0 Dabarun Bincike

Ayyukan ta’addanci abu ne da al’umma suke ƙ yama, amma duk da haka a ɓ angaren harshe ya taimaka wajen bun ƙ asa harshe matu ƙ a. Dalili kuwa shi ne, an sami ƙ aruwar sababbin kalmomi da sassan jimla da jimloli a cikin harshen Hausa ta dalilin hakan. Saboda haka, an yi amfani da dabaru da dama domin tattara bayanan wannan bincike. Daga cikin dabarun da aka yi amfani da su akwai:

a.      Tattaunawa da ‘yan ta’addan da suka tuba domin samun sahihan bayanai.

b.      Tattaro bayanai daga kafafen ya ɗ a labarai na jaridu da mujallu da kuma kafar sadarwa ta intanet.

c.       Hira da wasu daga cikin wa ɗ anda aka yi garkuwa da su, suka samu ‘yanci.

d.     Tattaunawa da wasu mutanen da ayyukan ta’addanci suke gudana a yankunansu.

3.0 Ra’in Bincike

R a’in da aka yi amfani da shi wajen gudanar da wannan bincike shi ne , ra’in ‘Dangantakar Harshe da Rikici’ (Language of Violence) na Smith, Alison G. da wasu (2008), wanda Randall (2010) ya fa ɗ a ɗ a. Wannan ra’i ya yi magana a kan sadarwa tsakanin ‘yan ta’adda da wa ɗ anda ke ya ƙ ar su. Ra’in ya bayyana cewa harshe shi ne kanwa uwar gami ga dukkan al’amurra, domin babu abin da za a aiwatar ba tare da an yi amfani da shi ba. Har wa yau, da harshe ne ake iya gane mutum ko waye da halinsa da aikinsa? Ra’in ya nuna cewa, da harshe ake am fani wajen dabarun ya ƙ i domin isar da sa ƙ o da tunkarar abokan gaba. Wa ɗ anda suka yi aiki wajen ɗ abba ƙ a wannan ra in akwai: Antonio Sanfilippo da wasu (2013) da Shannon C. Houck (2013) da Lucian Gideon Corway (2017) da Richard Frank (2021) duk sun yi amfani da ra in. Harley Mc Cullough (2022) ya yi wa ra in kwaskwarima ta ɓ angaren ta’addanci da ramuwar gayya inda ya dubi ayyukan ta’addancin da ke faruwa a sassa daban-daban na duniya, musamman yankin ƙ asashen Larabawa.

Bugu da ƙ ari, ra in ya yi ƙ o ƙ arin nazartar sadarwar ‘yan ta’adda ta ɓ angarori daban-daban da sukan yi domin cimma bu ƙ atunsu na yau da kullum. Ta la’akari da halayensu da ɗ abi’unsu da kuma lura da yadda suke gudanar da lamurransu da yanayin zamantakewarsu. Haka kuma, da yadda suke sarrafa harshe. Ra’in ya bayyana cewa, masana ba su mayar da hankali a kan abin da ya shafi harshen ta’addanci ba, wannan kuwa shi ne dalilin da ya sa aka samar da wannan ra’i. Baya ga haka kuma, ra’in ya yi ƙ o ƙ arin fito da wasu ƙ udurori guda uku da mai nazarin harshen ta’addanci ya kamata ya kula da su kamar haka:

a.      La’akari da yanayi da halayyar ‘yan ta’adda a lokacin da suke sadarwa. Wannan dabara tana taimakawa ƙ warai wajen gano ma anar abubuwan da suke furtawa.

b.      Nazarin kalmomi da jimlolin da aka samu daga ‘yan ta’adda, domin fito da ma’anarsu ta asali da kuma sabuwar ma’ana.

c.       Kalmomin da suke furtawa su dace da nazarin da ake a kai, domin shi zai ba mai nazari damar bin diddigin kowace kalma ta fuskar ma’ana.

Daga ƙ arshe, binciken ya ɗ auki wannan ra’in ne domin amfani da shi wajen gudanar da wannan ma ƙ ala.

4.0 Ma’anar Ta’addanci?

Ta’addanci aiki ne da yake iya haifar da ayyuka masu illa da lahani da ha ɗ ari da ke iya haifar da rauni a sashen jikin mutum ko ya yi sanadiyar rasa rayuwarsa da dukiyarsa. Kasancewar ta’addanci ba sabon abu ba ne a Arewa maso yammacin Nijeriya da ma Arewacin Niyeriya baki ɗ aya, malamai da yawa sun bayar da ma’anar ta’addanci a cikin ayyukansu. Wasu daga cikin ma’anonin da suka bayar sun ha ɗ a da:

Abraham (1947, p. 397) ya bayyana ta’addanci a harshen Ingilishi da:

 ‘Bad manner that serious misdemeanour.’

Fassarar mai bincike: ‘ Ta’addanci yana nufin aikata wani mummunan hali da al’umma suke ƙ yama.

Wannan ma’ana ta yi daidai da fahimtar abin da wannan ma ƙ ala take bu ƙ atar fitowa da shi a kan ta’addanci, saboda a nan ana son a fahimci mene ne ta’addanci, kafin a kai ga nazarin ƙ ir ƙ irarrin sunayen da suka samu ta dalilin ayyukan ta’addanci a wasu yankunan Arewa maso Yammacin Nijeriya.

Ƙ amusun Hausa na Jami’ar Bayaro (2006, p. 416) ya bayyana cewa, ‘Ta’addanci yana nufin mugun aiki, musamman na haddasa ɓ arna kamar lalata abubuwa ko kisa da sauransu, don bambancin siyasa ko addini.’

Dunfawa (2009, p. 140) yana cewa, ‘ta’addanci ga Bahaushe na nufin aikata wani abu na rashin imani da ke iya salwantar da rayuwar wanda aka aikata abin a kansa, wani lokaci ma har da mai aikatawa’.

Haka kuma, Atuwo (2009, P. 136) ya ce, ‘ta’addanci na nufin manyan miyagun ɗ abi’u ko aikata miyagun ayyuka.’

Idan aka yi la’akari da wa ɗ annan ma’anoni a kan ta’addanci, za a fahimci cewa ta’addanci abu ne maras kyau a cikin al’umma. Bugu da ƙ ari, babu wata al umma mai tin ƙ aho da shi. A ɓ angaren nazarin harshe kawai ta’addanci ke da amfani ta hanyar samar da sababbin kalmomi a cikin harshe. Dukkan ma’anonin da aka bayar na ta’addanci suna da ala ƙ a da tunanin wannan takarda, saboda binciken na son ya fito da sunayen da suka samu a dalilin ayyukan masu ta addanci a wasu yankunan Arewa maso Yammacin Nijeriya. Wannan kuwa, zai fito da yadda harshen Hausa ya samu bun ƙ asa ta hanyar samar da ƙ ir ƙ irarrun sunayen da ke da ma anoni masu tayar da hankali da firgita da ban tsoro ga jama a.

A fahimtar wannan ma ƙ alar, ta’addanci shi ne aikata wani abu na assha da gangan da ke iya haifar da rasa rayuka da dukiyoyin al’umma.

5.0 Ƙ irar Kalma

Ƙ irar kalma ba sabon abu ba ne ga harshe, domin shi ke nuna bun ƙ asa da fa ɗ a ɗ a da yalwar da harshe ke samu ta hanyar samar da sababbin kalmomi. Harshen Hausa yakan ƙ ir ƙ iri kalmomin da sukan saje da wa ɗ anda da yake da su domin amfanin yau da kullum. Dalilin haka, masana sun bayyana ƙ ir ƙ ira da cewa:

Crystal (2008, p. 340) ‘Morphology: The branch of grammar which studies the structure or forms of words, primary through the use of morphemes construct.’

Fassarar mai bincike: Ƙ irar kalma wani yanki ne na nahawu da ya ƙ unshi yadda ake samar da kalmomi ta hanyar amfani da ƙ wayar ma ana .

Muhimman abubuwa daga cikin hanyoyin ƙ irar kalma su ne: Ɗ afi da ninki da har ɗ antawa da kwaskwarima (Abubakar 2000, p. 5).

Har wa yau, Ndimele (2007, p. 94) ya bayyana wasu daga cikin hanyoyin ƙ irar kalma kamar haka: (a) (Compounding) har ɗ antawa (b) (Borrowing) aro (c) (Clipping) gutsirewa (d) (Coinage or Neologism) kwaskwarima (e) (Conversion) sauya ajin kalma da kuma ha ɗ e sassan kalmomi biyu su ba da ɗ aya. Wannan ma ƙ ala ta dubi wa ɗ annan hanyoyin ne wa ɗ anda ake bi a Hausa wajen samar da sunayen ‘yan ta’adda, kamar yadda ta gudanar da bincike a kai.

Fagge (2013) ya bayyana, tsira da kumbura da har ɗ antawa da cewa su ne ginshi ƙ an ilmin ƙ irar kalma. Shi kuwa Sani (2011, p. 5) cewa ya yi hanyoyin samar da kalma su ne ɗ afi da har ɗ antawa da ninki.

Bun ƙ asar harshe shi ke sa ya sauya, saboda ya ɗ uwa da yake yi a sanadiyyar yawan masu magana da shi, a sakamakon wannan sai a sami sauyi da ke samar da sababbin kalmomi da sassan jimloli da jimloli a cikin harshe. Bugu da ƙ ari kuma, ya samar da kalmomin da ake yi wa kwaskwarima da ƙ ir ƙ ira da kwaikwaya da aro daga wasu harsuna domin su dace da harshen Hausa.

6.0 Ƙ ir ƙ ira da Ma anar Sunayen Wasu Yan ta adda

Ilmin ƙ irar kalma yana taka rawa matu ƙ a wajen samar da kalmomi a cikin harshen Hausa. Daga cikin kalmomin da aka samu akwai sunaye da ke da sigogi daban-daban da kuma ma anoni mabambanta. Haka kuma sunayen sun bambanta wajen yanayin ƙ irarsu da kuma inda suka fi dacewa su zo a wajen ginin jimla. Ga ka ɗ an daga cikin ma’anar suna:

Abraham (1947, p. 826) ya bayyana suna da cewa: ‘Suna wani la ƙ abi ne da ake ba wa abu mai rai ko maras rai, wanda ake gani da ido ko wanda ba iyawa .

Abbas (2012, p. 31) ya ce, ‘suna kalma ce da ake amfani da ita domin ambaton mutum ko dabba ko tsiro ko wani abu mai rai ko maras rai, ta yadda za a iya bambanta shi da wani’.

A fahimtar wannan ma ƙ ala, suna abu ne da ake la ƙ aba wa mutum ko dabba ko wuri ko abubuwa domin bambancewa tsakanin wani abu da wani.

Harshen Hausa ya samu amfana da kalmomi da dama, musamman wajen sadarwa ta yau da kullum. A ɓ angaren kalmomin da ‘yan ta’adda suke amfani da su akwai kalmomi da suka danganci ƙ ir ƙ ira, a dalilin haka masana suka kawo ma anoni daban-daban. Ga wasu daga cikinsu.

Yakasai (2005, p. 5) ya bayyana cewa, ‘ ƙ ir ƙ ira wata hanya ce da harshe ke bi wajen samar da kalmomi a cikinsa.

Bature (1995, p. 135) yana cewa, ‘ ƙ ir ƙ ira na nufin idan Bahaushe ya samu ba ƙ on abu da yake son ya ba shi sabon suna, in ya duba cikin kalmomin Hausa na asali babu wani abu da ya dace ya fa ɗ a ɗ a ma’anarsa sai ya duba cikin kalmomin Hausa ya ƙ ir ƙ ira wata sabuwar ma ana ya ba wannan abun.

Saboda haka, ƙ ir ƙ ira wata hanya ce da harshen Hausa ke bi wajen samar da sababbin kalmomi a cikin rumbun kalmominsa.

A ɓ angaren ma’ana ta sunayen ‘yan ta’adda za mu kalli ma’ana ta kimiyar harshe. Ana nazarin ma’ana a kimiyar harshe ne ta bisa kyakkyawan tsarin da harsuna suke kallon tsarin ma’anar kalmomi da kuma jimloli. A bisa irin wannan ne Finegan (2004, p. 188-217) yake cewa, ana iya nazarin ma’anar kalmomi ta fuskoki uku: (a) ma’ana ta kimiyar harshe (linguistic meaning) wadda ta ƙ unshi ma anar da kalma take nufi kai tsaye a zahiri (referential meaning) da kuma dukkan ma’anonin da ke tattare cikin kalma idan aka fa ɗ e ta (sense meaning). Haka kuma akwai (b) ma’anar da ke tattare da yanayin zamantakewa (social meaning) da kuma ma’anar da ke ƙ unshe da manufar mai magana da abin da mai sauraro zai fahimta (affective meaning).

A wannan ma ƙ ala an mayar da hankali ga ma ana ta kimiyar harshe ta wa ɗ annan sunaye wadda ta ƙ unshi ma ana ta kai tsaye (referential meaning) da kuma ma anar da duk mai sauraro zai iya bijirowa a ransa idan an ambaci kowane ɗ aya daga cikin sunayen. Wannan yana nufin duk sunan da aka ambata, ma’anarsa ta kai tsaye ake nufi da shi da kuma abin da masu saurare suka fahimta.

7.0 Sunayen ‘Yan Ta’adda da Aka Samar ta Hanyar Aro da Kwaskwarima

Aro wata hanya ce mai sau ƙ i da harshe ke amfani da ita domin samar da sababbin kalmomi. Babu wani harshe da ya tsaya ko ya dogara ga kansa kawai, ba tare da aro ba. Kowane harshe a duniya yana aron kalmomi ga wa ɗ ansu harsuna. Saboda haka kafin mu shiga cikin aron da harshen Hausa ya yi daga wasu harsuna za a san ma’anar aro.

Ndimele (2007, p. 85) ya bayyana aro da cewa:

‘One of the commonest ways of creating new words in the human language is borrowing. Borrowing simply means the process of taking words from one or more languages to fit into the vocabulary of another’.

Fassara: Aro hanya ce mafi sau ƙ i wajen samar da sababbin kalmomi a cikin harshe. Aro na nufin wata dabara ta ɗ auko wasu kalmomi daga harshe ɗ aya ko fiye da zimmar mayar da su a cikin rumbun kalmomin wannan harshe da ya ɗ auko.

Ƙ amusun Hausa na Jami’ar CNHN (2006, P. 268) ya bayyana kwaskwarima da cewa, ‘yi wa abu ado domin ƙ ara masa kyau .

Saboda haka harshen Hausa ya yi aron kalmomi daga wasu harsuna kama daga Ingilishi da Larabci da Fulfulde da Kanuri da Faransanci da sauransu. A nan ma ƙ alar ta yi nazarin sunayen ‘yan ta’adda da al’umma ke kiran su da su, da kuma wa ɗ anda suke la ƙ aba wa kansu da aka aro daga wasu harsuna.

S/N

Ƙ ir ƙ irarren suna

Ƙ irara kalma

Aji

Asalin kalma

Ma’ana ta asali

Sabuwar ma’ana

1.

Simolii

Aro

Suna

Ingilishi

‘Small’

Ƙ aramin yaron da bai balaga ba.

Ƙ aramin yaro da ke cikin ayyukan ta’addanci.

2.

Saajan

Aro

Suna

Ingilishi

‘Sergent’

Mu ƙ amin kayan sarki da ke da igiya uku. Ya wuce kofaral amma bai kai insifekta ba.

Ɗ an ta’adda da ke hukunta wa ɗ anda suka yi laifi.

3.

Oga

Aro

Suna

Ingilishi

‘Oga’

Shugaba mai ba da umurni.

Shugaban tawaga idan aka fita aiki.

4.

No-rawun

Aro

Suna

Ingilishi

‘No-round’

Kalma ce ta Ingilishi mai nufin babu kwana.

Suna ne na ɗ an ta’adda da ke nuni da ba ya gudu ba ya ja da baya idan an fita aiki.

5.

Yalo-emiya

Aro

Suna

Ingilishi

‘Yellow’ ‘Emir’

Sunaye ne biyu duka na aro. Na farko yana nuna mutum mai jar fata. Na biyu kuwa suna ne mai nuna shugabanci.

Ɗ an ta’adda mai jar fata, kuma yana da la ƙ abin emiya da ke nufin shugaba.

6.

Jummo-bulak

Aro/kwaskwarima

Suna

Yoruba/

Iingilishi

‘Jami’u’

‘Black’

Har ɗ a ɗɗ en suna ne da aka aro daga Yoruba da Ingilishi.

Ƙ asaitaccen ɗ an ta’adda da ya yi fice wajen garkuwa da mutane.

7.

Albaniya

Aro

Suna

Turawa

‘Albania’

Suna ne na wata Ƙ asa.

La ƙ abi ne na wani ɗ an ta’adda da ya shahara wajen sata.

8.

Manjagara

Ƙ ir ƙ ira

Suna

Ingilishi

‘Rack’

Suna ne da aka aro daga Ingilishi mai nufin abin yaye ƙ azanta.

Ɗ an ta’adda ne da ke kwashe komai idan ya je sata.

9.

Jambros

Aro

Suna

Ingilishi

Front Clipping

Babu ma’ana ɗ aya dun ƙ ulalliya.

 Matashin ɓ arawo mai son nuna fele ƙ e da gwaninta.

10.

Kwamanda

Aro

Suna

Ingilishi

‘Commander’

Shugaban wata runduna da ke ba da umurni.

Shugaban ‘yan ta’adda da ke ba su umurni a yayin aiki.

11.

Kachalla

Aro na kai tsaye

Suna

Kanuri

‘Shugaba’

Kalma ce da aka aro daga Barebari da ke nufin shugaba.

Shugaban daba da ke da yawan mambobi da kayan aiki.

12.

Gayu

Aro/kwaskwarima

Suna

Ingilishi ‘guys’

Mutane musamman matasa masu son ado da fele ƙ e irin na zamani.

Suna ne da ‘yan ta’adda ke kiran kansu da shi. Dalili kuwa, domin suna ke ɓ e a wuri na musamman da ba su son kowa ya riske su ba tare da izininsu ba.

13.

Gwamnati

Aro/kwaskwarima

Suna

Ingilishi

‘Government’

Hukumar ƙ asa ko ta jiha, mai gindaya dokoki ga ‘yan ƙ asa.

Ana kiran ‘yan ta’adda gwamnati domin sun buwayi hukuma, kuma ana tsoronsu sukan ba da umurni ga talakawa kuma dole a bi.

14.

Bubaji

Kwaskwarima

Suna

Fulatanci’Abubakar’

Suna ne da aka yi ha ɗ a-ha ɗ a aka gina shi. A Fulatanci yana nufin ‘Abubakar’

Suna ne na wani ɗ an ta’adda da ya addabi mutane.

15.

Bulaki

Kwaskwarima

Suna

Ingilishi

‘Black’

Kalma ce ta aro daga Ingilishi, aka yi mata kwaskwarima zuwa Hausa ta koma ba ƙ i.

Ƙ asurgumin ɗ an ta’adda ba ƙ i da ya addabi al’umma ta hanyar garkuwa da mutane da fya ɗ e da sace dukiyoyinsu..

 

Simolii: ‘small’ /smol/ suna ne na aro daga harshen Ingilishi. Yana cikin ajin sunaye. Sunan yana zuwa a farkon jimla wani lokaci a yankin aikatau na jimla. ‘Simoli ya a je ɗ ibar ruwa’. ‘Kachalla ya a aiki simoli.’ Ma’ana ta asali ƙ aramin yaro da bai balaga ba. Sabuwar ma ana kuwa, ƙ aramin yaro da ya shiga ayyukan ta addanci. Dangantakar ma ana ta asali da sabuwar ma ana ita ce ƙ aramin yaron da bai balaga ba.

Saajan: ‘sergeant’ /saá:jàn/ sunan aro ne daga harshen Ingilishi, yana cikin ajin sunaye. An fi amfani da sunan a mahallin yankin suna na jimla. ‘Saajan ya a yi masu bulala.’ Ma’ana ta asali mu ƙ amin kayan sarki da ke da igiya uku a rigarsa, ya wuce kofaral amma bai kai insifekta ba. Sabuwar ma ana ɗ an ta’adda da ke hukunta masu laifi. Dangantaka tsakanin ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce mu ƙ ami ne na wanda ke shugabantar wasu mutane..

Oga: /ou.ga/ kalma ce ta aro daga Ingilishi, tana cikin ajin sunaye. Mafi yawa ta fi zuwa a mahallin yankin suna a jimla. ‘Oga ya a san ƙ amo su . Ma’ana ta asali shugaba mai ba da umurni. Sabuwar ma’ana shugaban tawaga idan aka fita aiki da ke ba da umurni. Dangantaka tsakanin ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce ba da umurni.

No-rawun, kalma ce ta aro. Tana cikin ajin sunaye. Bugu da ƙ ari, a tsarin jimlar Hausa an fi amfani da sunan a mahallin yankin suna. ‘No-rawun ya a kai farmaki.’ Ma’ana ta asali kalma ce ta Ingilishi mai nufin babu kwana. Suna ne na ɗ an ta’adda da ke nuni da ba ya gudu ba ya ja da baya, idan an fita aiki. Dangantaka tsakanin ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce idan an tafi, ba ja da baya.

Yalo-Emiya, kalmomi ne na aro daga harshen Ingilishi. Suna cikin ajin sunaye. Haka kuma an fi amfani da sunan a mahallin yankin suna na jimla. ‘Yalo-Emiya ya a ba su wuta.’ Ma’ana ta asali sunaye ne biyu duka na aro daga harshen Ingilishi. Na farko na nufin mutum mai jar fata. Na biyu kuwa, yana nuni da shugaba. Sabuwar ma’ana wani ƙ asurgumin ɗ an ta’adda mai launin fata ja, haka ma yana da la ƙ abi mai nuna shugaba. Dangantaka tsakanin ma ana ta asali da sabuwar ma ana ita ce shugabanci.

Jummo-Bulak, ‘black’ /blaek/ suna ne har ɗ a ɗɗ e na aro daga Ingilishi da Fulatanci, amma Bulak an yi mashi kwaskwarima bayan an aro sunan. Yana cikin ajin sunaye. Sunan ya fi fitowa a yankin suna na jimla. ‘Jummo-Bulak ya a feshe su.’ Ma’ana ta asali sunaye ne na aro biyu daga Yoruba da Ingilishi aka ha ɗ a suka ba da suna ɗ aya. “Jummo suna ne na Yarbawa da ke nufin ‘Jami’u’, da Hausa kuwa ‘Jamilu’. ‘Bulaki kalma ce mai nufin launin ba ƙ i. An aro ta ne daga harshen Ingilishi. Sabuwar ma’ana wani shahararren ɗ an ta’adda ba ƙ i mai ban tsoro da firgita. Dangantaka tsakanin ma anonin biyu ita ce ba ƙ i.

Albaniya, suna ne na aro. Yana cikin ajin sunaye, haka kuma a tsarin jimla ta fi zuwa a mahallin yankin suna. ‘Albaniya ya a iso daba.’ Ma’ana ta asali suna ne na wata ƙ asa. Sabuwar ma ana la ƙ abi ne na wani ɗ an ta’adda da ya addabi al’umma. Dangantaka tsakanin ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce ɗ an ta’addan ba ɗ an ƙ asa ba ne.

Manjagara, ‘rack’ /raek’/ kalma ce ta aro daga Ingilishi amma aka yi mata kwaskwarima. Tana cikin ajin suna. A tsarin jimla, sunan ya fi zuwa a yankin aikatau, duk da cewa wani lokaci yakan zo a yankin suna. ‘Manjagara ya a isa garin.’ Ma’ana ta asali abin share ƙ azanta. Sabuwar ma ana wani ɓ arawo da ke kwashe duk abin da ya tarar a yayin da ya je sata. Danagantaka da ke tsakanin ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce kwashe komai da aka tarar.

Jam-bros, suna ne har ɗ a ɗɗ e na aro daga Ingilishi, yana cikin ajin sunaye. A tsarin jimla sunan ya fi zuwa a mahallin yankin suna. ‘Jam-bros ya a fita aiki.’ Ma’ana ta asali ba ta ci karo da ma’ana ɗ aya dun ƙ ulalliya ba. Sabuwar ma’ana matashin ɗ an ta’adda mai son nuna fele ƙ e da gwaninta. Babu dangantaka tsakanin ma ana ta asali da sabuwar ma ana.

Kwamanda, ‘commander’ /ka’maeder/ suna ne na aro daga Ingilishi, yana cikin ajin sunaye. Sunan ya fi zuwa a mahallin yankin suna a tsarin jimlar Hausa. ‘Kwamanda ya a ba da umurni.’ Ma’ana ta asali shugaba mai ba da umurni musamman a tsarin kayan sarki. Sabuwar ma’ana suna ne da ‘yan ta’adda ke kiran kansu da shi mai nufin shugaba mai ba da umurni idan aka fita aiki. Dangantaka ita ce hani da ba da umurni.

8.0 Sakamakon Bincike

A bincike na ilimi, ana sa ran daga ƙ arshe a fito da sakamakon da aka gano domin ganin an cimma burin manufar bincike ko akasin haka. Saboda haka, a wannan ma ƙ ala an gano abubuwa kamar haka:

Tabbatar da sunayen da ‘yan ta’adda suka samu, a dalilin ayyukan ‘yan ta’adda a bakunan wa ɗ anda ake yi wa ayyukan ta’addanci, domin sanya su a matsayin ƙ ari ga wa ɗ anda ake da su a cikin harshen Hausa.

Haka kuma, ma ƙ alar ta fito da wasu sunayen da ‘yan ta’adda suka samu ta hanyar aro da kwaskwarima tare da bayanin hanyoyin ƙ irarsu da ajinsu na nahawu da kuma inda suka fi dacewa su zo a cikin jimla.

Bugu da ƙ ari, ma ƙ alar ta yi ƙ o ƙ arin fito da ma anar suna na asali da kuma sabuwar ma’ana da ‘yan ta’adda suka ba shi, da dangantakar da ke tsakanin su. Haka ma, an yi ƙ o ƙ arin fitowa da wasu sunayen da ‘yan ta’adda suka samu ta hanyar aro da kwaskwarima.

9.0 Kammalawa

A wannan ma ƙ ala an tattauna abubuwa da dama da suka ha ɗ a da: Ma’anar ta’addanci da bayanin sunayen da aka samu ta hanyar aro da kwaskwarima. Haka kuma an yi bayanin hanyoyin ƙ irar wa ɗ annan sunaye da ajinsu na nahawu da kuma inda suka fi dacewa su zo a tsarin jimla. Bugu da ƙ ari, ma ƙ alar ta fito da ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana da kuma dangantakar da ke tsakaninsu. Daga ƙ arshe, an fito da sakamakon bincike.

 Manazarta

Abbas, N. I. (2012). Nahawun Sunayen Hausawa. M. A. Hausa Studies. Department of

 Nigerian Languages. Usmanu Ɗ anfodiyo University, Sokoto.

Abraham, R. C . ( 1947 ) . Dictionary of Hausa Langauge. London: Hodder and Soughton.

Abubakar, A. (2000). An Intrductory Hausa Morphology. Maiduguri: University of Maiduguri Press.

Amfani, A. H. (2007). Hausa Morphology: In Basic Linguistics for Nigerian Langauges Teachers, (ed) Ore Yusuf. Pp137.

Atuwo, A. A . ( 2009 ). Ta’addanci a Idon Bahaushe: Ya ɗ uwarsa da Tasirinsa a Wasu Ƙ agaggun Rubutattun Labaran Hausa. Kundin Digiri na Uku. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Usmanu Danfodiyo University, Sakkwato.

CNHN, ( 2006 ). Ƙ amusun Hausa Na Jami’ar Bayero Kano. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nigeria.

Crystal, D. (2008). A Dictionary of Linguistics and Phonetics Seven Edition. U. S. A. Blackwell Puplishing. ISBN: 978-1-405-15296-9

Dunfawa, A. A. (2009). Maka ɗ i a Mahangar Manazarta . Kano: Gidan Dabino Publishers. ISBN: 978-8082-02-5

Fagge, U. U. (2013). Ƙ irar Kalma a Hausa . Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

Ministry for Security and Home Affairs. (2011). Report On Armed Banditry, Recovery And Other Related Operation in the State. Zamfara State Government.

Mohammad, I. A. (2019). Ginshi ƙ in Bayanin Ilmin Ƙ irar Kalma a Hausa: Ta ƙ aitaccen Tsokaci. Ma ƙ alar da aka Gabatar a Taron Ƙ ara wa Juna Sani a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami ar Usmanu Ɗ anfodiyo, Sakkwato.

Ndimele, O. N. (2007). Readings on Language. Port-Harcourt: M & J Grand Orbit Communication Ltd.

Rufa’i, M. A . ( 2021 ). I am a Bandits: A Decade of Research on Armed Banditry in Zamfara State. 15th University Seminar Presented at Usmanu Danfodiyo University, Sokoto. Auditorium, Main Campus.

Sani, M. A. Z. (2011). Gamayyar Tasrifi da Tsarin Sautin Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited. ISBN: 978-125-833-0

Yakasai, S. A. ( 2020 ). Jagoran Ilmin Walwalar Harshe. Kaduna: Amal Printing Press.

Jibril, S. N. (2017). Language, Literature, Culture and Conflict Resolution: Language and    Conflict Resolution in the 21st Century. A Paper Presented at the 30th Annual       Conference of the Linguistic Association of Nigeria (CLAN). Ignatius Ajuru University   of Education, Port Harcourt. Rivers State, Nigeria.

 

Post a Comment

0 Comments