Ayyukan Da Suka Kamata a Yi Domin Samun Falalar Goman Karshen Ramadan

TAMBAYA (85)

Wanne aiki ya kamata mu dinga yi don samun falalar goman karshe ?

AMSA

Alhamdulillah

Uwar Muminai, Nana Aisha (Radiyallahu anha) ta tambayi Annabi Sallallahu alaihi wasallam: "Ya Ma'aikin Allah, shin me zan fada idan naga daren Lailatul Qadri ?" Sai yace: "Kice

اللّٰهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّيْ

Ma'ana: "Ya Allah kai Mai Afuwa ne, kuma kana son yin afuwa. To kayi afuwa gareni"

Imam Abu Dawud ne ya rawaito shi, da Tirmidhi da Ibn Majah

Dangane da aiki kuma. Ga bonanza kamar haka;

A shawarce anso mutum ya dinga ciyarwa idan kana da iko. Ko kuma ka dinga siyan dabino ko da na Naira 100 ne a kowacce rana a cikin goman karshennan. Domin kuwa indai har aka dace a ranar Daren Lailatul Qadri ka bayar to wannan ladan dabinon zai zamo kamar kayi kyauta ne ta tsawon shekaru 84 da watanni 6

Babbar garabasa kuma itace ka gina gidaje a cikin Aljannah

Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace: "Duk mutumin da ya karanta Suratul ikhlas (Qulhuwallahu ahad) sau 10 a jere, Allah Azzawajallah zai gina masa katafaren gidan bene a cikin gidan Aljannah" Sai Sayyadina Umar yace: Ya Rasulullah gidan bene, aikam zamu yawaita karantawa. Sai Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace: "Fallahu aksar" Ma'ana: Allah shine mai yawaitawa

Duba hadisin a cikin Sahih al-Jami' as-Saghir lamba ta 6,472 na Shaikh Muhammad Nasiriddin al-Albany (Rahimahullah)

Kenan indai muka dage da karanta Qulhuwallahu ahad sau 10 a jere, kuma muka dace da wannan daren to Allah (Subhanahu wata'ala) zai gina mana gidaje dayawa sau adadin kwanakin dake cikin shekaru 84 da watanni 6 dinnan. Ba fa a kasar Dubai ba, a'a gidajen bene na alfarma a Aljannah ake magana. Allahu Akbar ! Me yafi wannan ?

Muna roqon Allah ya bamu ikon aiwatarwa. Sannan kuma kada mu manta mu dinga saka yan uwanmu musulman Gaza dake kasar Palestine da ma sauran musulmai a cikin addu'o'inmu akan Allah ya kawo musu daukin kashe-kashen da Banu Isra'ela suke musu. Sama da mutane 20,000, musulmai musamman yara, wadanda aka kashe, tsawon watanni 6 kenan, muna roqon Allah ya karbi shahadarsu. Mu kuma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da imani

Muma kuma a ci gaba da sakamu a addu'a musamman ma Malam Khamis da yake aiki tuquru ba dare ba rana, Allah ya biyashi da Aljannatil Firdous, Allah ya tabbatar damu akan wannan da'awa da mukeyi yasa mu dinga yi da ikhlasi ya rabamu da riya

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments