Gabatarwa
An gina babi na bakwai sukutum kan kwaɗo. A cikin ƙarƙashin 7.1 an kawo ma’anar kwaɗo. A ƙarƙashin 7.2 kuwa, an zayyano nau’o’in kwaɗo na gargajiya da yadda ake sarrafa su. Wannan babi kuwa yana ɗauke ne da nau’o’in kwaɗon da suka samu a zamanance. Yana da kyau a fahimci cewa, kusan dukkanin nau’ukan kwaɗon da ake da su a gargajiyance akan same su a zamanance. Duk da haka akan samu ‘yan bambance-bambance ta ɓangaren sarrafawa, musamman da yake zamani ya zo da kayan haɗi iri-iri dangin ɗanɗano da ƙamshi.
Kwaɗon Dambu da Kabeji
Duk wani dambun
da aka yi fari ba tare da haɗi ba, to za a iya kwaɗo da shi. Yayin
samar da wannan kwaɗo, akan kwaɗanta dambun da kayan haɗi
ne kai tsaye. Su kuwa kayan haɗin da ake amfani da su sun haɗa da:
Kayan haɗin da za a tanada su ne:
i. Albasa
ii. Dambu
iii. Gishiri
iv. Kabeji
v. Magi
vi. Mai
vii. Ƙuli
viii. Tarugu
Kwaɗon Garin Kwaki da Salat ko Zogale ko Tafasa ko Rama
Garin kwaki ma akan kwaɗanta shi da ɗaya daga cikin nau’o’in ganyaye da aka
lissafa a sama. Da fari ana jiƙa
garin ne. Bayan ya jiƙa
sai a haɗa shi da kayan haɗi a gauraya kamar dai yadda ake sauran kwaɗo da aka yi bayani a sama. Kayan haɗin da ake amfani da su sun ƙunshi:
Kayan haɗin da za a tanada su ne:
i. Garin Kwaki
ii. Gishir
iii. Magi
iv. Mai
v. Ƙuli
vi. Ruwa
vii. Tumatur
viii. Tarugu
ix. Salat ko zogale ko tafasa ko rama
Kwaɗon Salat
Shi ma kansa ganyen salat ana iya kwaɗanta shi. Wato zai kasance an yayyanka salat ɗin ne sannan a sanya masa kayan haɗi (a maimakon a sanya shi cikin wani nau’in kwaɗo a matsayin kayan haɗi). Nau’o’in kayan haɗin da ake buƙata yayin kwaɗon salat sun haɗa da:
Kayan haɗin da za a tanada su ne:
i. Albasa
ii. Gishiri
iii. Magi
iv. Mai
v. Ƙuli
vi. Ruwa
vii. Salat
viii. Tarugu
ix. Tumatur
Kwaɗon Kabeji
Shi ma kabeji akan iya kwaɗanta shi a ci. Ana yin kwaɗon
nasa ne kamar yadda ake na
sauran ganyayen
da Bahaushe yake kwaɗantawa,
musamman salat. Kayan haɗin da ake amfani da su sun ƙunshi:
Kayan haɗin da za a tanada su ne:
i. Albasa
ii. Gishiri
iii. Kabeji
iv. Kukumba
v. Magi
vi. Mai
vii. Ƙuli
viii. Ruwa
ix. Tarugu
x. Tumatur
Kwaɗon Tumatur
Shi ma tumatur akan iya kwaɗanta shi. Yayin samar da wannan nau’in kwaɗo, akan samu tumatur masu kyau a
yayyanka. An fi so a samu tumatur mai nama sosai (ma’ana wanda ruwan cikinsa kaɗan ne). Akan tanadi kayan haɗi kamar su:
Kayan haɗin da za a tanada su ne:
a. Albasa
b. Gishiri
c. Magi
d. Mai
e. Ƙuli
f. Ruwa
g. Tarugu
h. Tumatur
Kammalawa
Kamar dai yadda aka gani a sama, kwaɗo ya kasance nau’o’i
daban-daban. Duk da cewa
akan yi kwaɗo domin rashi ko toshe yunwa, sau da dama kwaɗo na kasancewa abin marmari, musamman yayin da aka sanya
kayan haɗi sosai. Wani abin da ya sa ake son kwaɗo shi ne,
sauƙin sarrafawa da kuma kasancewarsa
abincin gaggawa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.