Ticker

    Loading......

Gurbin Adawa a Siyasar Zamani

Citation: Ɗangulbi, A.R. (2024). Gurbin Adawa a Siyasar Zamani. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 364-371. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.042.

Gurbin Adawa a Siyasar Zamani  

Na

Aliyu Rabi’u Ɗ angulbi
Sashen Koyar da Harsuna da Al’adu
Jami’ar Tarayya Gusau
aliyurabiu83@gmail.com
07032567689, 07088233390

 Tsakure

Salon mulkin siyasa wani tsari ne da al’umma suke za ɓ en wakilansu da kansu bisa ga cancantar ɗ an takara da kundin tsarin mulki ya yarda da shi. Wato, siyasa wani salon mulki ne na farar hula da ke bai wa ‘yan ƙ asa yanci da damar saka kansu a dama da su a sha anin mulki. Wannan bincike mai taken Gurbin A dawa A Siyasa r Zamani , b incike ne da ya shafi gudummawar da adawa take bayarwa wajen kawo sauyin salon tafiyar da shugabanci, ta hanyar haska wa masu mulki kurakuransu domin su gyara da kuma yi musu hannunka-mai-sanda ko garga ɗ i ga yadda ya kamata su aiwatar da abubuwan da za su amfani al’ummar da suka za ɓ e su. A wani ɓ angare kuma adawa tana ilmantar da al’umma game da kyawawan ayyukan da shugabanni suka yi, ko kuma su yi ƙ orafe- ƙ orafe ko soke-soke a kan  abubuwan da shugabanni ko yan siyasa suke aikatawa wa ɗ anda ba su dace ba. Haka kuma su jawo hankalin masu za ɓ e su za ɓ i mutane nagari da suka dace a lokacin jefa ƙ uri a. Hakan zai kawo gyara ga kurakuran da shugabanni suke tafkawa a lokacin da suke gudanar da mulkinsu. Ha ƙƙ in kowane shugaba ne ya aiwatar da al ƙ awuran da ya yi wa al umma a lokacin da yake ya ƙ in neman za ɓ e. Al ƙ awuran sukan ha ɗ a da: Samar da ingantaccen ilimi da ruwan sha da hanyoyin sufuri da kiwon lafiya da bun ƙ asa aikin gona da samar da  tsaro da zaman lafiya da kuma bun ƙ asa tattalin arziki. Rashin cika wa ɗ annan al ƙ awura kan sa a sami yan adawa su ri ƙ a soke-soke da ƙ orafe- ƙ orafe domin su tunatar da masu mulki ko yan siyasa game da al ƙ awurran da suka yi wa jama a a lokacin ya ƙ in neman za ɓ e domin su gyara. Wannan bincike zai mayarda hankali ne a kan matsayin adawa a siyasa da amfaninta da illolinta da kuma rawar da kafafen ya ɗ a labarai ke takawa wajen kawo gyara da sauyi mai ma’ana ga yadda ake gudanar da mulkin siyasa don amfanin talakawa da ƙ asa baki ɗ aya.

1.0 Gabatarwa

Rayuwa tana inganta ta hanyar kyakkyawar zamantakewa tsakanin al’umma da shugabanninsu bisa ga samun shugabanci nagari. Kamar yadda aka sani siyasa, salon mulki ne da al’umma take za ɓ en mutanen da suka dace. Sannan su samu damar t o fa albarkacin bakinsu a sha’anin gudanar da mulki . Dokar tsarin mulki ta bai wa ‘yan ƙ asa damar kafa jam iyyun siyasa fiye da ɗ aya bisa ga ra’ayoyin jama’a, kamar yadda kundin tsarin mulki na ƙ asa ya tanada. Kowace jam iyya tana tsara manufofinta daidai da bu ƙ atar al ummar ƙ asa, sannan ta yi al ƙ awarin aiwatar da duk manufofinta idan aka za ɓ e ta ta kafa gwamnati. Manufofin sun ha ɗ a da : Samar da ingantaccen ruwan sha ga mazauna birni da karkara, da bun ƙ asa ilimi, da kiwon lafiya, da bun ƙ asa kasuwanci, da noma da samar da zaman lafiya. Wa ɗ annan manufofi da kowace jam’iyya ta tsara, su ne suke jawo hankalin talakawa su za ɓ i jam’iyyar da ta dace da bu ƙ atunsu. Duk jam iyyar da ta samu nasarar kafa gwamnati tun daga matakin taryya har zuwa ga ƙ ananan hukumomi, to akan sami sauran jam iyyu su  kasance jam iyyun adawa ga jam iyya mai mulki. Hakan kan ba su dama su ri ƙ a yin soke-soke da ƙ orafe- ƙ orafe, idan ba su gamsu da yadda jam iyar ke gudanar da mulkinta ba. Wa ɗ annan ƙ orafe- ƙ orafe da soke-soke su ne matsayin adawa. Wannan bincike ya yi ƙ o ƙ arin gano matsayin adawa a siyasa da gudummawar da adawa ke bayarwa wajen kawo sauyi da cigaban mulkin siyasa a Nijeriya da kuma duniya baki ɗ aya. Har wa  yau binciken zai yi duba ga irin amfani da illolin da adawa da rawar da kafafen ya ɗ a labarai ke bayarwa wajen habaka adawa a tsakanin al’umma da masu mulki wajen samar da walwala da ɗ an ɗ ana romon dimokura ɗ iyya da talakawa ke yi. Haka kuma su haska wa masu mulki su gudanar da mulki cikin adalci ta hanyar gyara kurakuransu, su aiwatar da al ƙ awuran da suka yi wa al umma domin cigaban ƙ asa.

1.1 Manufar Bincike

Kowane irin bincike da za a gudanar akan ɗ ora shi bisa ga manufar da ta dace da bu ƙ atar wa ɗ anda aka yi domin su. Wannan bincike na nufin gano matsayin adawa a siyasar zamani da rawar da  take takawa wajen ilmantar da al'umma a siyasance domin a samu sauyi ga mulkin kasa. Haka kuma da tasirin adawa ko amfaninta da illolinta ga al’umma baki ɗ aya. Adawa tana kawo sauyi a salon mulki wajen bai wa  masu mulki damar gyara kurakuransu da aiwatar da ayyukan raya ƙ asa baki ɗ aya. Haka kuma, bincken yana da manufar za ƙ ulo abubuwan cigaban al umma da adawa take kawowa ga talakawa ta hanyar ba su yancin fa ɗ ar albarkacin baki da haska musu fitila su gano yadda za ɓ en shugabanni nagari ke tafiyar da mulki cikin gaskiya da ri ƙ on amana, ko akasin haka ga shugabanni marasa gaskiya da amana. Mulkin adalci shi ne tushen samun zaman lafiya da cigaban ƙ asa baki ɗ aya.

1.2 Farfajiyar Bincike

Mulkin jama’a abu ne da ke fuskantar ƙ alubale daga kowane ɓ angare na al’umma, musamman tsakanin masu mulki da wa ɗ anda ake mulka. Hakan yana faruwa a dalilin bambancin ra’ayi da ɓ angaranci ko ƙ abilanci ko kuma addini. Wannan bincike ya mai da hankali ne dan gano matsayin adawa a siyasar zamani  da amfaninta da illolinta da kuma gudummawar da adawa ke bayarwa wajen samar da ha ɗ in kan al’ummar kasa da kawo sauyi mai ma’ana, musamman wajen kawo gyara da sauyi ga yadda shugabanni ke tafiyar da mulki domin cigaban ƙ asa. Misali, rashin cika al ƙ awura, da tauye ha ƙƙ in talakawa da cin hanci da rashawa. A dalilin haka ya sa wannan bincike ya ta ƙ aita a kan gano matsayin adawa a siyasar zamani da amfaninta ga al umma da kuma illolinta ga yan siyasa. Wato akan yi amfani da adawa domin a haska wa masu mulki kurakuransu don su gyara.

1.3 Dubarun Gudanar da Bincike

Taken wannan bincike shi ne, ‘Gurbin Adawa a Siyasar zamani’. An bi hanyoyi da dama domin samun bayanai da za su taimaka a sami nasara ga kammala wannan bincike. Da farko an yi tattaki zuwa wuraren da aka samo bayanai da ke da ala ƙ a da kuma muhimmanci ga wannan aiki. Misali an yi hira da masana harkokin siyasa da masu nazarin siyasa da kuma yan siyasa da masu ri ƙ e da mu ƙ aman siyasa. Bugu da ƙ ari, an duba littattafai da ma ƙ alu da kundayen binciken digiri daban - daban da suke da ala ƙ a makusanciya ko ta nesa da wannan bincike.

1.4 Tambayoyin Bincike

a. Mece ce adawa?

b. Mene ne asalin adawa?

c.  Mene ne matsayin adawa a siyasa ?

d. Wane ne ɗ an adawa ?

e. Mene ne amfanin adawa a siyasa?

f. Wace illa adawa take da ita a siyasa?

  2.0  Ma’anar Adawa

Adawa a siyasa tana nufin yin ƙ orafe- ƙ orafe da yan siyasa ko yan adawa ke yi dangane da rashin gamsuwarsu ga yadda wani mutum ko wasu mutane ke gudanar da wani tsari ko shiri da ya shafi al amurran yau da kullum, (Bello Muhammad Kwakwazo dan shekara 56, a hira da aka yi da shi a  ranar Asbar, 24/10/2022). Hausawa sukan kalli adawa a matsayin kushewa ko kyashin wani mutum da Allah (S. W. A) ya yi wa wata baiwa ko ɗ aukaka ta fuskar ilimi ko dukiya ko shugabanci. Bargery,(1993, p. 5), ya bayyana adawa a matsayin  ƙ iyayya ko kushewa da wani mutum zai nuna ga wani tsari ko shiri da hukuma  ko wasu shugabanni ke aiwatarwa. Wannan ya bayyana adawa a tunanin masana cewa, ita ce kushewa ga abin da ya tsone wa mutum ido, ko bai gamsu da yadda ake gudanar da abin ba. Marian Webster (10th edition), ya bayyana cewa, adawa tana nufin rashin amincewa ko yarda ga wani abin da ya sa ɓ a wa ra’ayin sauran jama’a a cikin shugabanci domin a maye gurbinsa da abin da mafi ri n jayen mutane suke da ra’ayi. Shi ma Hornby, (8th edition:), ya bayyana adawa da cewa, rashin yarda ce ga wani tsari ko shiri da wani ko wasu mutane da ke jagorancin jama’a; da nufin kawo sauyi mai ma’ana. Wato, rashin yarda da wani tsari ko shiri da wani mai mulki ko shugaba ke aiwatarwa domin cigaban ƙ asa ko wani yanki.

2.1 Asalin adawa

Kalmar adawa ta samo asali daga kalmar Larabci, ‘Al-Adawatu’,. Da Hausawa suka aro wannan kalma ta adawa daga Larabci, sai suka bar ta yadda  suka aro  ta daga Larabcin, wato, “Adawa”, amma ma’anarta ba ta canja ba daga ma’anar da Larabci ya ba ta ba. Wato, ƙ iyayya ko rashin gamsuwa da wani abu da wani ke aikataw, musamman shugabanci. Kalmar adawa a Bahaushen tunani, ita ce, ƙ iyayya ko nuna rashin jin dadi ga wata baiwa da Allah ya yi wa wani ko wata, ko kuma wani shiri ko tsari da wani mutum ko hukuma ke aiwatarwa, wanda ya sa ɓ a wa ra’ayi ko bu ƙ atar wani ko wasu mutane. Da wannan ta ƙ aitaccen bayani ake ganin cewa adawa ta samo asali daga kalmar Larabci, wato, adawa. Mutane suna amfani da wannan kalma ta adawa domin su bayyana ƙ iyayyarsu ga duk wani tsari ko shiri da ake gudanarwa wanda ya sa ɓ a wa ra’ayinsu domin masu aiwatar da  abin su ji, su  gyara ko su sauya tsarin ta yadda zai amfani al’umma, musamman a tsarin gudanar da shugabanci na siyasa.

A ta ƙ aice adawa na nufin kishi ko kushewa ko jiyewa ko ƙ yashi ko ƙ iyayya ga yadda wasu ke nuna rashin gamsuwa ga yadda wani mutum yake gudanar da sha anin mulki da ya sa ɓ a wa ra’ayin jama’a domin ya gyara kurakuransa. Idan aka dubi dukkan ma’anonin da masana suka bayar, dangane da ma’anar adawa, sai a ga cewa, adawa a dunkule tana nufin rashin gamsuwa ko yarda da wani tsari ko shiri da wani zai kawo,wanda ya sa ɓ a wa ra’ayoyin mafi rinjayen jama’ar da aka yi dominsu, (Bargery, 1934, P. ).

3.0 Gurbin Adawa a S iyasa

B ayyana kushewa tsakanin masu mulki da wa ɗ anda ake mulka ko ‘yan siyasa a kan tafiyar salon mulkinsu. Kamar yadda aka sani, dokar kundin tsarin mulki na ƙ asa ta bai wa jama a dama su kafa jam iyyun  siyasa daban - daban, sannan mutane su yanki katin jefa ƙ uri a kafin gudanar da za ɓ e. Kowace jam’iyya tana  tsayar da ɗ an takaranta tun daga mu ƙ amin shugaban kasa har zuwa kujerar kansila a ƙ ananan hukumomi. Yawancin jam iyyun siyasa sukan yi tarayya akan manufofi iri ɗ aya, sai dai a sami sa ɓ ani ta fuskar zartarwa. Duk jam’iyyar da ta kafa gwamnati a ƙ asa, ita ce jam iyya mai mulki. Yayin da sauran jam iyyu da ba su yi nasara ba suke zama yan adawa. Misali, akwai jam iyyun siyasa fiye da ɗ aya a Nijeriya tun daga farkon jamhuriya ta farko har zuwa wannan jamhuriya ta hu ɗ u da muke ciki. A jamhuriya ta farko akwai ja’iyyar NPC da NEPU da N. C .N.C. da  A.G. da sauransu. Jam’iyyar NPC ita ke da shugaban ƙ asa da mafi rinjayen yan majalisu, sauran jam iyyu suka zama yan adawa saboda ba su da shugaban ƙ asa. Haka abin yake a jamhuriya  ta biyu, inda jam iyyar NPN, ita ce ke da shugaban ƙ asa, yayin da jam iyyun G.N.P.P., da U.P.N. da A. D. da sauransu suka zama jam iyyun adawa, (Birniwa:1987). A wannan jamhuriya ta hu ɗ u jam’iyyar P.D.P ta kasance jam’iyya mai mulki a farkon jamhuriyar, wato shekarar 1999, yayin da jam’iyyun A.P.P, da A.N.C. APGA da sauransu suka zama ‘yan adawa. Da aka sake wani juyi, sai jam’iyyar A.P.C. ta kar ɓ i ragamar mulki, yayin da jam’iyyar P.D.P. da sauransu suka koma jam’iyyun adawa.

Duk gwamnati ko jam’iyyar da ba ta da ‘yan adawa, to ba za ta ta ɓ a aikata wani abun a zo a gani ba ga jama’ar da ta za ɓ e ta. Hausawa suna cewa, ‘ M utum bai san ana kallon sa ba lokacin da yake kashi, sai an tokare shi da tsinke’’. Saboda haka, adawa ita ce gishirin siyasa, kuma ita ce tubalin gina ingantaccen shugabanci a ƙ asa ( Ɗ angulbi :2003). Idan babu adawa a siyasa, dukkan ƙ udurorin da jam iyyun siyasa za su kawo dangane da bun ƙ asa tattalin arzikin ƙ asa da samar da ingantaccen ilimi, da ruwan sha da kiyon lafiya da sauransu, ba za su kammalu ba domin shugabanni ba za su kula da aiwatar da su ba, sai idan yan adawa sun fa ɗ akar da su. Amma da kasancewar adawa a siyasa makamin ya ƙ i da yan siyasa za ka ga shugabanni sun tuna da al ƙ awurran da suka yi wa talakawa, nan take su farka su aiwatar da wa ɗ annan al ƙ awurra saboda amfanin talakawansu. Adawa tana fa ɗ akar da masu mulki su fahimci inda kurakuransu suke, sannan su ƙ aurace wa bin son zukatansu wajen tafiyar da sha anin mulki da aka ɗ ora masu amana. Saboda haka, adawa tana da babban matsayi a cikin al’amurran siyasa, musamman wajen jawo hankalin masu mulki da shugabannin siyasa su gyara kurakuransu da suke tafkawa a lokacin da giyar mulki take bugunsu.

Jam’iyyun adawa sukan taka muhimmiyar rawa wajen soke-soke da ƙ orafe- ƙ orafe dangane da yadda jam’iyya mai mulki take gudanar da mulki domin su nuna irin kurakuran da ke tattare a cikin tafiyar gwamnati mai mulkin ƙ asa. Wa ɗ annan ƙ orafe- ƙ orafe da soke-soke da jam iyyu  da ya yan jam iyyun da ba su da rinjaye a gwamnatance ke yi, su ne ake kira adawa. Adawa  makami ce ta ya ƙ ar salon mulki maras adalci da ri ƙ on amana. Wato mataki ce ta nuna wa shugabanni ko masu mulki kurakuransu don su gyara, ko kuma a yaba musu inda suka yi abin a zo a gani domin su ƙ ara ƙ wazo wajen aiwatar da ayyukan cigaban ƙ asa. Saboda haka ne ya sa aka samu adawa gida biyu. Wato, akwai adawa mai ma ana, da kuma adawa maras ma ana. Kowace daga cikin wa ɗ annan adawoyi tana da muhimmanci ga kawo canji ko sauyi ga gudanar da mulki a kowace ƙ asa, musamman a ƙ asashen Afirka da ma Nijeriya da ba su ƙ ware da mulkin siyasa ba.

3.1 Wane ne Ɗ an Adawa?

Ɗ an adawa wani mutum ne ko gungun mutane masu kushe duk wani aiki na alheri ko akasin haka da shugabanni ko ‘yan siyasa ke aiwatarwa ga al’umma. Wato ɗ an adawa yana nuna ra’ayinsa a fili ta hanyar furta kalaman ɓ atanci ko fa ɗ ar gaskiya ko ƙ orafi ko suka ga masu mulki ko yan siyasa dangane da yadda suke tafiyar da ragamar mulkin ƙ asa. Ɗ an adawa kan sa ido ga yadda ake gudanar da harkokin jagorancin jama a. Idan shugabanni sun yi adalci sai ya yaba, ko ya yi ƙ orafi a kan abin da ya sa ɓ a wa bu ƙ atar mutanen da suka za ɓ e su. Bungu ɗ u (2017:60 ), ya bayyana cewa, abubuwan da ke haddasa adawa tsakanin ‘yan siyasa ko masu mulki da wa ɗ anda ake mulka, sun ha ɗ a da rashin cika al ƙ awari da masu mulki suka ɗ auko a lokacin da suke ya ƙ in neman za ɓ e, ko sa ɓ a wa tsarin kundin tsarin mulkin ƙ asa wajen gudanar da mulkinsu. Haka kuma rashin samun nasarar lashe za ɓ e da wasu jam’iyyu suka kasa samun nasara yakan haifar da adawa ga wa ɗ anda suka yi nasara.

Jam’iyyar da ta kafa gwamnati a matakin tarayya ta zama jam’iyyar mulkin ƙ asa, yayin da jam iyyun da ba su sami nasara ba, sukan kasance jam iyyun adawa. Haka abin yake ga magoya bayan jam iyyun da ba su sami nasara ba, sai su zama yan adawar jam iyya da shugabannin da suka kafa gwamnati. Ƙ orafe- ƙ orafe da bayyana ra ayin yan adawa ga masu mulki ta hanyar soke-soke ko furta maganganun ɓ atanci, su ne ake ɗ auka a matsayin adawa. Su kuwa masu ƙ orafe- ƙ orafen, su ne ake kira, ’yan adawa. A Nijeriya akwai jam’iyyu da dama da suka taka muhimmiyar rawa wajen  gudanar da mulki tun daga jamhuriya ta farko, har zuwa wannan jamhuriya ta hu ɗ u da muke ciki. Misali a jamhuriya ta farko jam’iyyun siyasa irin su N.P.C da N.E.P.U., da N.C.N.C., da A.G da sauransu; su ne suka jagoranci tafiyar mulkin dimokura ɗ iyya bayan samun ‘yancin kai daga Turawan mulkin mallaka ( Ɗ angulbi: 2003:41). Jam iyyar N.P.C. ita ce ta kafa gwamnatin Tarayya, wato, ita ke da shugaban ƙ asa da mafi rinjayen yan majalisun tarayya, yayin da sauran jam iyyun NEPU da A.G da sauransu suka kasance yan adawa a 1957-1966. Haka abin yake a jumhuriya ta biyu, inda jam iyyar N.P.N. ta kasance jam iyya mai mulki, yayin da jam iyyun G.N.P.P da U.P.N. da N.P.P. da P.R.P suka kasance jam iyyun adawa a 1979-1983 A jamhuriya ta uku da ba ta yi nasara ba, jam’iyar N.R.C. da S.D.P su ne jam’iyyun da gwamnati ta ƙ ir ƙ iro. Jam iyyar S.D.P. ita ce ta sami nasarar cin za ɓ e, amma aka soke. A lokacin Janar Sani Abacha kuma jam’iyyun  U.N.C.P. da G. D.M. da N.A. C., suka fafata, amma jam’iyyar U.N.C.P. ta lashe za ɓ e, sauran jam’iyyun suka zama ‘yan adawa.

A wannan jumhuri ta hu ɗ u da muke ciki, jam’iyyar P.D.P, ce ta fara kafa gwamnati a 1999, sauran jam’iyyun A.P.P. da A.D., da A.N.C. suka kasance jam’iyyun adawa. Bayan da wa’adin mulkin jam’iyyar P.D.P. karo na hu ɗ u ya ƙ are, sai jam iyyar ha ɗ aka ta A.P.C. ta lashe za ɓ e a 2015. A wannan lokaci ne jam’iyyar P.D.P. ta dawo cikin jam’iyyun adawa tare da sauran jam’iyyun da ba su kafa gwamnati ba. Wannan ya nuna cewa, babu jam’iyyar da ke zama mai mulki na dindindin, domin akan sami canji ya faru, jam’iyya mai mulki ta dawo cikin ‘yan adawa. Wato, kowace jam’iyya tana iya zama mai mulkin ƙ asa, wani lokaci ta koma yar adawa. Saboda da haka a matakin tarayya duk jam iyyar da ta kafa gwamnati, ita ce mai mulkin ƙ asa ko da ba ta da rinjaye a jihohi ko ƙ ananan hukumomi. Don haka a yau an sami canji a matakin tarayya, inda jam iyyar A.P.C, ta kafa gwamnati yayin da jam iyyar P.D.P da sauran jam iyyun da ba su yi nasara ba suka kasance yan adawar A.P.C. Haka yake ko a jihohi duk jam iyyar da ta kafa gwamnati a jiha ita ce ke da ƙ ananan hukumomi, yayin da sauran jam iyyu sukan zama jam iyyun adawa ( Ɗ angulbi 2003).

4.0 Ire-iren Adawa

Adawa a siyasa, kamar gishiri ne ga abinci, domin abinci ɗ an ɗ anonsa ba ya cika ba tare da shi ba, haka yake a lamarin siyasa, idan babu adawa to, siyasa ta samu ragisa. Bugu da ƙ ari, siyasa tana da nau’o’i daban-daban kamar haka:

4.1 Adawa Mai Ma’ana

Adawa mai ma’ana ita ce wadda ‘yan adawa suke soke-soke ko ƙ orafe- ƙ orafe zuwa ga masu mulki ko gwamnati domin su haska masu fitila ga wasu muhimman ayyuka na cigaban ƙ asa da suka kamata su mayar da hankali ga aiwatar da su domin amfanin al umma. Wannan adawa tana tunatar da gwamnati ko yan siyasa  su tuna da al ƙ awurran da suka ɗ auka a lokacin da suke ya ƙ in neman za ɓ e. Misali, ana  tunatar da su al ƙ awurran da suka shafi harkokin kiyon lafiya wanda suka yi al ƙ awarin gina ɗ akunan shan magani ko asibitoci, da samar da takin zamani ga manoma, da ingantaccen ruwan sha ga mazauna birni da ƙ auyuka da tallafa wa yan kasuwa da jari don bun ƙ asa kasuwancinsu da inganta hanyoyin sufuri da sauransu. Sannan adawa mai ma ana tana jawo hankalin masu mulki su aiwatar da wasu ayyukan raya ƙ asa masu muhimmanci ga jama a, ko da ba su daga cikin tsarin manufofin jam iyyarsu. Amma saboda muhimmancinsu ga al umma sai gwamnati ta kar ɓ i wannan ƙ orafi ta aiwatar da abubuwan da aka yi ƙ orafi a kansu matu ƙ ar ba su sa ɓ a wa bu ƙ atun sauran jama a ba. (Hira da  Alhaji Bello Muhammad Kwakwazo Gusau, wani ɗ an siyasa mai shekara 57, a ranar Litinin 24/10/2022, da ƙ arfe 3:30pm.). Ɗ an siyasar ya ƙ ara da cewa, ayyukan tsaftace muhalli da makamantan haka suna daga cikin ayyukan da ba su cikin tsarin muhimman ayyukan raya ƙ asa, amma saboda da muhimmancinsu ga samar da ingantaccen kiyon lafiya, ya sa yan adawa suke ƙ orafi ga masu mulki domin a samar da tsaftataccen muhalli ga al umma ta hanyar kwashe shara a bola da gyara magudanun ruwa a layukan unguwanni domin kauce wa ambaliyar ruwan sama lokacin damina.

A ta ƙ aice adawa mai ma ana ita ce, soke-soke ko ƙ orafe- ƙ orafe da yan adawa ko masu fashin ba ƙ i a kan al amurran siyasa ke yi domin su haska wa shugabanni hanya ga wasu muhimman ayyuka da suka kamata su aiwatar da kuma yaba ma shugabanni dangane da ƙ o ƙ arinsu na samar da ayyukan raya ƙ asa don kyautata wa mutanen da suka za ɓ e su. Haka kuma su nuna wa masu mulki inda ya kamata su mai da hankalinsu wajen aiwatar da ayyukan da ke da amfani ga jama’a. Sannan kuma su tunatar da masu mulki (gwamnati)  game da al ƙ awurran da ta yi wa jama a na kyautata wa talakawa da sauran yan siyasa. Ta hanyar adawa mai ma ana ne ake samun sauyi ga salon mulkin dimokura ɗ iyya, saboda a nuna wa masu mulki kurakuransu, komi da ɗ i, komi wuya don su gyara.

 4.2 Adawa Maras Ma’ana

Ita kuma adawa maras ma’ana wasu ƙ orafe- ƙ orafe ne da soke-soke marasa kan-gado da tushe da yan adawa ke yi ga masu mulki domin kawai su nuna kasawarsu ga aiwatar da ayyukan cigaban ƙ asa da sauran abubuwan more rayuwa. Wato, komi kyawon ayyukan da masu mulki suka yi ko gwamnati ta yi, matu ƙ ar ba su gamsar da yan adawa ba, to babu yadda za a yi su amince da yin haka. Abin nufi a nan, shi ne, yan adawa maras ma ana, ba ayyukan raya ƙ asa ko cigaban tattalin arziki suke so a yi ba, a a sai dai a yi masu gatar da za su ri ƙ a sharholiya ta son ransu. Amma ayyukan da za su amfani al umma ba shi ne a gabansu ba. Wato duk ayyukan da gwamnati za ta aiwatar matu ƙ ar ba yan adawa za su amfana da su cikin aljihunsu ba, to a ganinsu gwamnati ta kasa. Misali, kamar gwamnati ta gina burtali da makiyaya ta dabbobi domin ke ɓ e su daga fa ɗ awa gonakin talakawa, wanda yakan haddasa tashe-tashen hankula da kashe-kashen rayuka da ba su ji ba, ba su gani ba, tsakanin manoma da makiyaya. Wannan yakan haifar da matsalolin rashin tsaro a ƙ asa da halakar ɗ inbin dukiyoyi da rayukan al’umma. Saboda haka adawa maras ma’ana tana kawo tarna ƙ i ga masu mulki har su kasance sun manta da abubuwan alheri da suke ƙ udirin aiwatarwa ga al ummar da suka za ɓ e su.

A ta ƙ aice adawa maras ma ana ita ce wadda yan adawa ke jefa ƙ orafe- ƙ orafe ko soke-soke marasa asali da tushe ga shugabanni. Yan adawa suna nuna kushewa ga wasu ayyukan cigaban ƙ asa da shugabanni suka aiwatar komi muhimmancinsu ga al umma. Bu ƙ atar yan adawa maras ma ana ita ce a yi wa talakawa gata da ku ɗ i suna sharholiya, ba ayyukan alheri ke gabansu ba. Saboda haka irin wannan adawa ta ‘yan a fasa kowa ya rasa, adawa ce mai tattare da ƙ azuffa da ƙ ir ƙ ire- ƙ ir ƙ iren ƙ arya da soke-soke marasa ma ana zuwa ga shugabanni da sauran masu ri ƙ e da mu ƙ aman siyasa komi ƙ wazonsu wajen kyautata wa jama a ta hanyar samar da ayyukan cigaban ƙ asa da al ummar ƙ asa baki ɗ aya.

4. 3 Adawa A  Kafafen  Ya ɗ a Labarai.

Ana amfani da kafafen ya ɗ a labarai daban-daban domin fa ɗ akar da al’umma da wayar masu da kai a kan abubuwan da ke faruwa a tafiyar gwamnati da su kansu suka za ɓ a da hannayensu. Misali’ gidajen radiyon B.B.C da muryar Amurka (V.O.A) da gidan radiyon Tarayya na Kaduna da gidan radiyon Vission da sauransu. Wa ɗ annan kafaf en ya ɗ a labarai suna gabatar da shirye-shiye masu ƙ ayatarwa domin wayar da kan al umma game da yadda gwamnatin farar hula take tafiyar da al amurranta na shugabanci. Haka su ma gidajen Talabijin masu zaman kansu da sauran kafafen sadarwa na zamani suna amfani da yan siyasa domin su wayar da kan mutane dangane da yadda shugabanni suke tafiyar da mulkinsu. Misali gidan Talabijin na Farin Wata suna gabatar da shirye-shirye da suka ha ɗ a da: Idon Mikiya, da Madafun Iko da shirin Cinnaka da na Ina Aka Dosa na gidan radiyon FM Vission da Farin Wata TV ke gabatarwa. Sukan gayyato masa fashin ba ƙ i daban-daban da yan adawa domin su yi sharhi mai gauni ga gwamnati mai mulki da kuma wasu fitattun mutane masu ruwa da tsaki a harkokin mulki. Haka gidan radiyon B.B.C. suna gabatar da shirin Sai Bango ya Tsage wanda kan tattauna da yan siyasa da masu fashin ba ƙ in siyasa daban-daban domin fa ɗ akar da al’umma game da tafiyar salon siyasar Nijeriya.

Bugu da ƙ ari, gidan radiyon muryar Amurka da na Faransa da Jamus ba a bar su a baya ba wajen gabatar da irin wa ɗ annan shirye-shiryen fa ɗ akarwa ga shugabanni da ‘yan siyasa da su kansu talakawan Nijeriya, ta hanyar tattaunawa da ‘yan siyasa na jam’iyyun adawa daban-daban da kuma masu ruwa-da-tsaki a kan harkokin siyasar Nijeriya. Misali, gidan radiyon muryar Amurka yana gabatar da shirin ‘Tsaka Mai Wuya’ inda ake tattaunawa da masu ruwa da tsaki ga siyasa da shugabannin jam’iyyun adawa da sauransu. A nan gida Nijeriya, gidajen radiyon Tarayya Kaduna da Pride FM na Gusau da Gold City FM da Gamji TV, da Al ’umma TV, duk ba a bar su a baya ba wajen ilmantar da al’umma a kan rawar da adawa take takawa wajen samar da siyasa mai inganci da cigaba a Nijeriya.

4.4 Amfanin Adawa a  Siyasa

Duk wani bincike ko aiki da ake gudanarwa ba zai rasa amfani ga al’ummar  da aka yi dominsu ba. Siyasa wani salon mulki ne da ake samun jama’a su yi maraba da shi saboda muhimmancinsa ga bai wa talakawa damar furta albarkacin bakinsu a tafiyar salon mulkin shugabannin da ke jagoran tar su. Adawa tana da amfani mai yawa ga al’umma domin tana ilmantar da mutane game da yadda mulki yake gudana. Haka kuma tana fa ɗ akar da ‘yan siyasa tare da garga ɗ in su da su gyara kurakuransu ga yadda suke tafiyar da shugabancin al’umma. Wato ta hanyar adawa ake fa ɗ akar da shugabanni kurakuransu domin su gyara ta hanyar aiwatar da ayyukan raya ƙ asa. Su ma kansu talakawa adawa tana tasiri gare su wajen ilmantar da su a kan muhimman ayyukan da ya kamata a yi m u su, wa ɗ anda za su amfane su a rayuwarsu ta yau da kullum. Adawa tana da amfani ga siyasa domin tana taimakawa wajen jawo hankalin masu mulki su gyara kurakuransu. Haka su ma talakawa tana taimaka masu su fahimci yadda ‘yan siyasa ke gudanar da jagorancin al’umma cikin adalci ko cikin zalunci. Daga cikin mahimmanci adawa akwai tunatar da shugabanni a kan al ƙ awurransu na bun ƙ asa tattalin arzikin ƙ asa ta hanyar kafa kamfuna da masana antu da bun ƙ asa hanyoyin sufuri don amfanin talakawa. Haka kuma ta fuskar ha ɓ aka ilimi, adawa tana da amfani domin shugabanni suna ƙ o ƙ arin gyara da gina makarantu da kyautata wa malamai ta hanyar ba su albashi mai tsoka da muhalli da kuma ba su kulawa ta musamman. Idan aka koma ta fannin noman damina da na rani adawa kan taimaka wajen tunatar da shugabanni al ƙ awurran da suka yi wa talakawa na samar da isasshen takin zamani don bun ƙ asa noman rani da na damina. Ta hanyar adawa ne gwamnati za ta yi ho ɓɓ asa wajen samar da abubuwan more rayuwa da kyautata wa al’umma ta hanyar ba su kyautuka na ababen hawa da ingantaccen kiwon lafiya da ruwan sha ga birane da ƙ auyuka. Idan akwai adawa shugabanni za su fi mai da hankali wajen kyautata wa jama ar da suka za ɓ e su, saboda su wanke tukunyarsu domin tuwon gobe. Amfanin adawa ga al’umma ba ƙ arami ba ne, domin wata fitila ce da ake haska wa shugabanni da masu neman mu ƙ amin siyasa su gano kurakuransu ko su gano hanyar da ta dace su bi wajen gyara tafiyar siyasarsu da kyautata wa al ummar da suka za ɓ e su.

4.5 Illolin Adawa a Siyasa

Duk wani abu da aka ce yana da amfani, to ba zai rasa illar da yake da ita ba. Adawa tana da illoli da dama ga al’umma domin ta hanyar adawa ne ake samun ma ƙ iya su shigo fagen tozartar da shugabannin da ba su kyautata masu ba. Saboda rashin aiwatar da abubuwan da suka dace ga jama a yana haifar da babbar illa ga shugabanni ko yan siyasa. Wata illa ita ce, adawa tana haifar da gaba tsakanin ya yan waccan jam iyya da wannan ko tsakanin jam iyya mai mulki da jam iyyar adawa. Haka kuma, tana yi wa tafiyar shugabanni kwan-gaba-kwan-baya wajen aiwatar da ayyukan ci gaban ƙ asa da suka ɗ auko al ƙ awari a lokacin da suke ya ƙ in neman za ɓ e, su sake tsayawa takarar wata kujera ta siyasa ko neman wani mu ƙ ami na siyasa. Bugu da ƙ ari, adawa tana bai wa mutane dama su ɓ aci wanda suke son su ɓ ata da sunan yi wa masu mulki hannunka- mai- sanda, wanda yin haka kan assasa fitina ko fa ɗ ace-fa ɗ ace tsakanin magoya bayan masu mulki da sauran ‘yan adawa ko wasu jama’a. Adawa tana haifar da rashin bin doka da oda da tsarin mulki ya tanada ta yi wa dokokin ƙ asa biyayya. Wato, ɓ angaren masu mulki da na ‘yan adawa. Ƙ orafe- ƙ orafe maras ma ana suna haifar da illa ga kyautatawa da masu mulki suke yi wa talakawa. Irin wannan adawa ita ce ake ce wa, adawar son zuciya ko adawa maras ma ana, wadda yan adawa ke ƙ orafe- ƙ orafe ba domin amfanin jama a ba, sai don biyan bu ƙ atar kansu. Saboda haka adawa tana  kawo ƙ iyayya tsakanin masu mulki da ya yan jam iyyun adawa ta hanyar gurguncewar tafiyar siyasar zamani.

5.0 Sakamakon Bincike

Wannan bincike ya gano cewa, adawa a siyasa tana da matu ƙ ar amfani wajen taimaka wa masu mulki su gyara tafiyarsu ga yadda suke gudanar da shugabanci. Adawa tana ƙ ara wa shugabanni ƙ arfin guiwa wajen aiwatar da ayyukan raya ƙ asa, da ayyukan kyautata ma al umma wajen samar musu da abubuwan more rayuwa. A fannin bun ƙ asa tattalin arzikin ƙ asa, adawa tana sa masu mulki su yi ha ɓɓ asa wajen samar da masana’antu da kamfunna domin samar da ku ɗ a ɗ en shiga da hana matasa zaman banza. Haka ta fannin bun ƙ asa ilimi, adawa tana taka rawar gani a siyasance wajen jawo hankalin masu mulki su gyara makarantu da gina wasu sabbin makarantu da azuzuwa domin samar da ingantaccen ilimi ga ya yan al umma. Bugu da ƙ ari, malaman makaranta suka amfana da duk wani shiri na inganta rayuwarsu ta hanyar kyautata albashinsu da sauransu. Haka yake a fannin noma da kiyon lafiya da tsaro da makamantan haka.

A ɓ angaren kawo sauyin shugabanci, adawa ta taka muhimmiyar rawa wajen jawonkalin masu jefa ƙ uri a su za ɓ i mutanen da suka dace domin gina ƙ asa; domin adawa tubali ne na gina ƙ asa. Idan babu adawa a siyasa, to ba za a sami ci gaba ba, domin kuwa ta hanyar adawa ne talakawa suke sanin yancinsu har su nemi shugabanni su yi musu ayyukan da za su amfana da su. Duk gwamnatin da ba a yi mata adawa, babu shakka za ta fuskanci matsaloli wajen gudanar da ayyukan cigaban ƙ asa. Talakawa suna amfana da adawa domin suna amfana da alhairai daga ɓ angaren masu mulki da na jam’iyyun siyasa ta hanyar samar masu da kayayyakin more rayuwa da suka ha ɗ a da abubuwan hawa da ku ɗ a ɗ en sana’a da na gudanar da ayyukan yau da kullum. Adawa ita ce sandar da ake amfani da ita wajen ke ɓ o shugabanni idan sun so su ƙ itare gona da iri. Adawa fitila ce ta haskaka wa shugabanni su gane kurakuransu domin su gyara. Kowa ya yi mulki sai ya sami yan adawa da adawa mai ma ana da kuma marasa ma ana.

6.0 Kammalawa

Adawa hanya ce ta nuna rashin gamsuwa da abubuwan da wani ko wasu mutane ko shugabanni ke yi, wanda ya sa ɓ a wa ra’ayi ko manufar jam’iyya ko jam’iyyu. ‘Yan adawa mutane ne da suke ƙ o ƙ arin fa ɗ akar da shugabanni ko masu ri ƙ e da mu ƙ aman siyasa daban-daban game da wata bada ƙ ala da gwamnatin jam iyar da ke mulki take tafkawa. A siyasance, adawa ba ƙ iyayya ko hassada ba ce ta ha ƙ i ƙ ani, a a Hausawa na cewa, gyara kayanka, wanda ya fi sauke mu raba . Wato adawa wata hanya ce ta fa ɗ akarwa da ilmantar da shugabanni ko masu ri ƙ e da mu ƙ amai daban-daban a kan kurakuran da ke ƙ unshe a cikin tafiyar mulkinsu don su ji su gyara kurakuransu. Haka kuma, tana wayar da kan al umma ko talakawa dangane da yadda shugabannin da ke mulki ke gudanar da sha anin jagorancinsu . Matsayin adawa a siyasa bai tsaya kawai ga wayar da kan masu mulki ba, a a har ma da taimaka wa talakawa su fahimta da yadda masu mulki ke tafiyar da al amurransu ko gudanar da harkokin mulki, tare da jawo hankalinsu su lura da halaye da ɗ abi’u na mutanen da suke neman a za ɓ e su, su shugabanci al’umma.

6.1 Shawarwari

Wannan bincike yana ba masu mulki shawarar cewa, duk wata adawa da ‘yan adawa suka yi zuwa gare su kada su ɗ auka ƙ iyayya ce, a a gyara kayanka ne, wanda Hausawa ke ce wa, ya fi sauke mu raba. Saboda haka su ɗ auka cewa adawar da ake yi gare su wata manuniya ce ga irin yadda suke gudanar da mulkinsu a cikin adalci ko akasin haka. Sannan su masu adawa su ɗ auka cewa suna yin adawa ne ba domin ba su son shuganni ba, a’a suna yi ne da zuciya ɗ aya domin su nuna wa shugabanni kurakuransu don su gyara.

Ya dace su kansu ‘yan siyasa su yi amfani da adawa wajen aiwatar da abubuwan cigaba da aka nuna musu domin a samu ingantaccen mulkin siyasa mai ɗ orewa. Su kuma jama’a su ri ƙ a kallon adawa a matsayin wani makami da mawa ƙ an siyasa ke amfani da shi don ya ƙ i da miyagun a ƙ idodin wasu yan siyasa da ke amfani da mu ƙ ami suna cutar al ummar da suka za ɓ e su. Duk wani aikin raya ƙ asa da masu mulki za su yi, ya kasance sun yi abin da zai amfani jama a ba wai  don su gina kansu ka ɗ ai ba.        

Manazarta

Aminu, K. (1987), Tarihin  Kafuwar Jam’iyyun Siyasa a Nijeriya. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Al ƙ anci H.A. (1987), Harsashen Ƙ asa Tsarin Mulki.Nelson Ibadan.

Bergery, G.P. (1993), Ƙ amusun Hausa-English da English Hausa vocabulary. London, Oxford University Press.

Birniwa H.A. (1987), Conservatism and Dissent; a Comparative Study of NPC/NPN and NEPU/PRP Hausa P olitical V erse F rom Circa 1946-1983. Kundin D igiri na U ku (Ph D), Jami’ar Sakkwato.

Bunza A.M. (2006), Gadon F e ɗ e A l’ada, Lagos Tiwal Nig. Ltd.

Bungudu A.I. (2017), Tarken Rubutattun Wa ƙ o ƙ in Siyasa na Kabiru Yahaya Kilasik. Kundin Digiri na Biyu, Jami ar Bayero, Kano.

Ɗ angulbi A.R. (1996), Habaici da Zambo a Cikin Wa ƙ o ƙ in Baka na Hausa, ma ƙ alar da aka gabatar a taron ƙ ara wa juna sani a kwalejin ilmi ta Shehu Shagari, Sakkwato.

Ɗ angulbi A.R. (2003), Siyasa a Nijeriya: Gudummawar Marubuta Wa ƙ o ƙ in Siyasa na Hausa Wajen Kafa Dmokura ɗ iyya a Jumhuriya ta Hu ɗ u Zango na Farko. Kundin D igiri na B iyu a J ami’ar Usmanu Ɗ anfodiyo, Ssakkwato.

Post a Comment

0 Comments