Ticker

    Loading......

Gurbin Kaza a Zamantakewar Hausawa: Duba Cikin Adabin Baka

Citation: Aminu, N. & Rambo, R.A. (2024). Gurbin Kaza a Zamantakewar Hausawa: Duba Cikin Adabin Baka. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 349-357. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.040.

Gurbin Kaza a Zamantakewar Hausawa: Duba Cikin Adabin Baka

Daga

Dr. Nasiru Aminu
Department of Nigerian Languages,
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
Phone - 07067706006
nsrklg@gmail.com  

Da

Dr. Rabi’u Aliyu Rambo
Department of Nigerian Languages,
Usmanu Danfodiyo Univesity, Sokoto.
Phone: 08125507991
dirindaji12aa@gmail.com

Tsakure

Wannan ma k ala ta yi nazari a kan rayuwar Hausawa a zamantakewarsu da kazar Hausa. Tunanin wannan ma ƙ ala ya samo asali ne daga duban irin yadda Bahaushe ya sha ƙ u da kiwon kaza zamunna da yawa, da yadda sunanta ya samu matsayi a wasu sassan adabin baka. Ma ƙ alarta kuma hango cewa ko bayan sassan jama’a, akwai wasu abubuwa kamar dabbobi da tsuntsaye da tsirrai da ke da muhimmanci a cikin muhallin Bahaushe wan ɗ anda zumuncinsu da al’umma na da tasiri da matsayin da ya kamata a yi nazari. Manufar wannan ita ce yin amfani da wasu sassan adabin Hausa a fito da wani sashe na falsafar rayuwa da al’adu da zumunci a tsakanin Bahaushe da kazar Hausa. Daga cikin hanyoyin da aka yi amfani da su domin cimma manufar wannan bincike akwai tattaunawa da jama’a da duba ayyukan masana da tattaro maganganun azanci da wasu bayanai na adabi masu ala ƙ a da aiki kai tsaye a cikin al’ummar Hausawa. An kuma yi amfani da Ra’in Nazarin Al’adu daga adabin baka (Cultural Studies Theory) wanda ya ba da dama tsauro bayanan al’ada daga adabin baka ta hanyar yin la’akari da yanayin rayuwar al’umma da tattalin arziki da tsarin zamantakewa da yadda suka yi tasiri a rayuwar al’umma. Wannan ya ba bincike tsakuro bayanai game da adabin baka da ƙ unshiyarsa da kuma wasu al’adu da ɗ abi’u da suka shafi rayuwar Hausawa dangane da dangantakarta da kaza. Sakamakon bincike ya tabbatar da cewa akwai zumuncin zamantakewa tsakanin al’ummar Hausawa da wasu tsuntsaye kamar kaza wanda tasirin ya haifi wasu nau’o’in adabin bakan Hausa masu bayanin wasu al’adu da ɗ abi’un Hausawa.

1.0 Gabatarwa

Al’adun al’ummar Hausawa suna tsira ne a muhallin da ake aiwatar da su, su ya ɗ u, su bun ƙ asa wasu wurare. Shi kuma adabi wani fage ne da ake nazari domin fito da yadda al’adu suke, da kuma matsayinsu a cikin al’umma, Ɗ angambo, (1984). Don haka. kowace irin al’umma a duniyar nan tana da nata ke ɓ a ɓɓ un ɗ abi’u da al’adu da ke iya tantance kowace iri ce, mai amfani da tsarin rayuwa tun kaka da kakanni ko na zamani, wa ɗ anda hotonsu ke iya fita daga adabinta. Wannan tunani ne ya tayar da magana a kan duba rayuwar Hausawa ta gargajiya daga adabin bakan Hausa. Sai dai a nan, akwai wasu abubuwa da aka yi la’akari da su a ƙ o ƙ arin fito da hoton rayuwar da ake tunani. Daga ciki akwai tsarin rayuwa da ƙ addarorinta da tunanin Bahaushe a tsarin zamantakewa da rayuwa. A cikin takardar an yi bitar yadda zumuncin mutum yake gudana a tsakaninsa da kazar da yake kiwo da yadda wannan zumuncin ya haifar da wani sashe na adabin bakan Hausa da ya zama taskar al’adu da halaye da ɗ abi’un al’umma.

Wannan ma ƙ ala tana da tunanin cewa kaza na da matu ƙ ar muhimmanci ga rayuwar Hausawa wadda ta zama sanadin bun ƙ asar adabin bakan Hausa. Shi kuma adabi da ɗ a dd en abu ne da ake aiwatarwa da ka, a kuma adana shi da ka. Yana kiyaye al’adu da ɗ abi’un al’umma, ya fito da halin rayuwar al’umma zamunna masu tsawo zuwa zamanin yau. An kasa wannan ma ƙ ala zuwa sassa guda uku. An yi tsokaci game da adabin baka da matsayin kaza ga Bahaushe da kuma fito da wasu sassan rayuwa daga adabin kazar Bahaushe.

Ita kuma yanayin zamantakewar Hausawa na nuni da irin dangantaka da mu’amala da ke wanzuwa cikin al’umma tsakaninta da jama’a ko wasu abubuwa da ke zaune ko tare da ita a rayuwar yau da kullum. Irin wannan yanayi na zama tare ne ake iya hangowa domin gano wata dangantaka da ke gudana tsakanin jama’a da al’dunsu. Wannan yana da ala ƙ a da cewar Adoro, (2013:127), “Halaye da al adu su ne al’umma, duk al’ummar da ta rasa su, to ita kaman an gama da ita, domin su ne madubin kowace al’umma. A cikin wannan nazari an kalli yadda zamantakewa da kaza ta haifar da wasu al’adu tsakaninsu da magidanta da sauran jama’a da ke kiwon kaji a matsayin sana’a ko don biyan wasu bukatu kamar yadda suka fito a cikin adabin baka na Hausawa.

A nan yana da kyau a fahimci cewa bayan ita kanta kazar wadda jigo ce a wannan bincike, shi ma adabin da aka gina da sunanta da al’adun da ya ƙ unsa na da babban matsayi wannan aiki, da kuma matsayinsa ga al’ummar Hausawa.

2.0 Manufar Bincike

Manufar wannan takarda ita ce yin amfani da wasu sassan adabin bakan Hausa a fito da wani sashe na al’adu da falsafar rayuwa da irin zumuncin da ke akwai tsakanin Bahaushe da kazar Hausa wadda yake mu’amala da ita a matsayin abukiyar zama ta hanyar kiwo.

3.0 Dabarun Bincike

 Dabarun bincike na nufin hanyoyi da hikimomin da mai bincike ya yi amfani da su wurin aiwatar da bincike tun daga farko har zuwa ƙ arshensa. ƙ amusun Hausa, (2006:82) ya bayyana dabara a matsayin kyakyyawan shiri ko wayo ko hikima ko tsari, na aiwatar da wani abu. A ta ƙ aice, dabarun bincike na nufin bin diddidgin wani abu bisa tsari cikin haza ƙ a domin gano wani sabon abu ko tabbataswa da yin gyara. Daga cikin hanyoyin da aka yi amfani da su a wannan bincike sun ha ɗ a da;

Duba ayyukan da masana suka gabatar game da ma’ana, matsayi da muhimmancin adabi da rabe-rabensa, kamar karin magana da habaici da salon magana da tatsuniya da labarai da makamantansu.

An kuma shiga a cikin al’ummar Hausawa aka yi hira da wasu mutane aka tattaro wasu nau’o’in adabin baka da suka shafi kaza, wa ɗ anda su ne zuciyar wannan aiki.

Sai ɗ ora aikin a kan Ra’in Nazarin Al’adu daga adabin baka (Cultural Studies Theory) wanda ya ba da dama tsakuro bayanan al’ada da wasu dab’iu da halayya jama’a daga adabin baka ta hanyar yin la’akari da yanayin rayuwarsu ta yau da kullum wadda ta shafi tattalin arziki da tsarin zamantakewa da tarbiyya da jagoranci don fito da yadda suka yi tasiri a rayuwar al’umma.

4.0 Waiwayen al’adun zamantakewa tsakanin Hausawa da kaza

Masana da dama sun yi bincike a cikin mujallun ilimi da kimiyya, kan kiwon kajin Turawa da kajin gargajiya na Hausa. Daga cikin akwai Nwosu, (1979) wanda ya yi bincike game da wasu ɗ abi’u da suka shafi kajin gida (na gargajiya) da Ayieko, (2014), shi kuma ya yi bincike ne yadda kiwon kaji ke amfanin al’umar Masueni ta ƙ asar Kenya. Sai Maikasuwa da Jabo, (2011), sun yi nazari kan matsalolin kiwon kajin Turawa a ƙ asar Sokoto. Akwai Nwagu, (2002), ya gudanar da bincike kan matakan kiwon kaji na gargajiya da na Turawa.

Daga cikin manyan dalilai da ke sa Bahaushe ajiye kaza sun ha ɗ a da bukatar kiwo da kasuwanci da abinci ( ƙ wai da nama) da sha’awa da magani. Bahaushe ya da ɗ e da al’adar kiwon dabbobi da tsuntsaye har zuwa lokacin da Allah ya hore masa su, tamkar abokan zama a muhallinsa. Dalilin haka ne, a yau ake samun ‘yan kasuwa wa ɗ anda hajarsu ba ta wuce kaji ba. A ƙ asar Hausa abu ne mai wuya a sami gidan da ba a kiwon kaza, saboda tana da sau ƙ in kulawa, kusan ma a ce ita take kiwon kanta, Aminu, (2015)

5.0 Nau’o’in Kajin Hausa

Daga cikin nau’o’in kaji akwai farare da ba ƙ a ƙ e da jajaye da wake-wake. Bayan haka, akwai masu kama da zabuwa da hankaka (mai yankan batta) da kaza durgu (mai guntayen ga ɓ o ɓ i), haka kuma akwai ƙ uzugu (maras gashi a jikinta) da kuma ja da surkin ba ƙ i a jikinta) da ƙ yanshen zakara, Aminu, (2015). Har ila yau, a wata tattaunawa da Samaila Umar na Gidan Igwai Sakkwato, ya ce daga cikin nau’o’in kaji akwai kaza mai tuntuwa da kaza fingi da higirgita.

5.1 Amfanin Kaza

Bayan nau’o’in kaji bincike ya gano cewa kaza na k yan ƙ yasar ƙ wai a sami ‘ya’ya ‘yan-tsaki kafin su zama ‘yan burtaye zuwa matasan kaji har a samu kaji budare da da ƙ wale. Daga wannan matakin rayuwa sai zama kwalinto (zakaru) zuwa shekarun tsufa.

Bayan haka yana da kyau a fahimci wata ala ƙ a da ke tsakanin kajin Hausa da al’umma, kamar yadda bincike ya nuna, Aminu, (2015) da Abdullahi, (2008), sun nuna cewa, idan uba ya zana wa ɗ ansa sunan mahaifinsa, idan aka ɓ ata wa yaron rai, ana yanka masa kaza a matsayin rarrashi ga yaron. Bayan haka akwai wasu muhimman batutuwa da suka shafi ala ƙ ar kaza da Baahaushe kamar haka;

i . Tsafi da neman biyan bukata

a.      Haka ana yanka jan zakara a wurin tsafin Uwar-gona, da wurin Bori da wurin ƙ auri, inda ake fige wa mai haihuwa kaza guda a matsayin tallafin kula da lafiyarta.

b.      A mafi yawancin matsafun Hausa, Tsafi da Bori ba su kammala sai da kaza.

c.       Sadaka don neman biyan bukata a wajen wasu- malamai, ana yanka kaji.

ii . Al’ada

a.      Haka ma a fa ɗ uwar haure ga yaro. Idan ya jefa a kan ɗ aki zai samu zakara da safe. Wannan ma wani camfi ne da aka fi amfani da shi a can dauri.

b.      A al’adar ginar rijiya a wasu wurare akan ba mai aikin ginar kaza da farawa da kuma idan ya ƙ are.

c.       Akan biya shara irin ta taubasantaka da kaza.

iii . Abinci

a.      Abinci/ ƙ wai- Bahaushe na amfani da kaza a matsayin abinci na morewa ga attajirai, ko a wurin liyafa, da tarbon ba ƙ i, kaza na kashe kunya inji Bahaushe.

iv . Bukukuwa

a.      Bukukuwa: A nan ma duk wani buki na Bahaushe da ba a yi bushasha da nama ba kaji ba, to lallai ana iya cewa bai ƙ ayatar ba, ko tsarin abincin ya yi rauni.

v Aikata Ayyukan Alheri, kamar;

a.      Tarbon mahajjata bayan sun dawo gida daga aikin hajji. Al’ada ce ta Hausawa.

b.      Ziyarar dangi a ƙ auye. Dangi kan ba maziyarta kyautar kaza.

c.       Sallamar ɗ an reno. Idan kaka mace ta yi reno ko yaye takan ba da kaza sallama ga jikanta.

vi Magani

Magani don neman waraka da inganta lafiya. Wasu wurare da ake magani da kaza ko warkarwa da inganta lafiya sun ha ɗ a da:

a.      Kaciya: Reno da jinyar sabuwar kaciya ga yara

b.      Kariya: Jinyar mai sabuwar kariyar ƙ ashi saboda wani hatsari ko wata ƙ addara

c.       Budurcin ‘ya mace/ gyara ‘ya mace a satin aure.

d.     Mura: Shirya farfesun kaza mai isasshen kayan yaji

e.      Maganin maza da mazan zakara/gidibe

f.        Zuciyar kaza

g.      Bali ƙ oto.

Daga bayanan da aka jeranta a sama, za a fahimci akwai zumunci da babbar ala ƙ a ta rayuwa a tsakanin Bahaushe da kaza lokaci mai nisa zuwa yau. Wannan na iya zama dalili da ake iya ganin hoton wannan zamantakewa a cikin wasu sssan adabin bakan Hausa.

6.0 I llolin Kaza

Bayan da wannan takarda ta yi bitar wasu fa’idojin ko amfanin kaza a cikin al’ummar Hausawa, ta kuma yi kokarin fito da wasu muhallai da Bahaushe ke ganin illar kazar a zamantakewarta da Bahaushe, daga cikin akwai yawan yin kashi da banna da tono da rashin tsafta da makamatansu. Ga bayanin wasu daga ciki;

a.      Kashi: Kashi a Hausar Sakkwato na nufin tutu. Kaza tsuntsuwa ce da ke yawan yin tutu a duk inda ya zo mata ba tare da la’akari da cewa ta ɓ ata wuri ko ta ƙ azamtar da wani bagire ba. Tana iya yin kashi a saman shimfi ɗ a ko a baranda ko a cikin ɗ aki ko wani bagire da bai dace ba. Wannan ne ya sa mafi yawan Hausawa ba su bukatar zama da ita a wuri daya. Daga cikin ɗ abi’unta na yin kashi, tana da bukatar jama’a su gayara wuri mai kyau ko su yi shimfida domin zama amma da kaza ta hau kansa sai ta zuba kashi kafin ta wuce. Idan kaza na kwa c in ƙ wai, a duk lokacin da ta fito sai ta zuba kashi mai warin gaske. Shi kuma kashin kaza yana daga cikin na’u’in najasa da Bahaushe ya tsananta.

b.      Ɓ anna: Kazan na da yawan yin ɓ anna. Wato ishe an yi shanyar wani abu mai daraja kamar garin abinci ko an tara shara, sai ta shiga ciki ta yi tono, ta watsar da shi. A wasu lokuttan takan waste shi ta yadda za a iya yin hasararsa har idan mai amfani ne. Haka idan ta samu an ajiye tumatir ko kayan miya ko ruwa ko wani abu tana iya sa bakia ciki ta ɓ annatar da su. Don haka wasu rukunin jama’a ke ganinta a matsayin ma ɓ annaciya.

c.       Rashin tsafta. Ana ganin kaza kamar mai yawan tsafta ta hanyar gyaran jikinta a koyaushe, amma Bahaushe na ganinta a matsayin dabba mai rashin tsafta ta hanayar cin kowane abinci da ya ja hankalinta. Daga ciki kuwa har da najasa tana i ya sa baki ga najasa cikin gida ko bayan gida. Kaza na da sha’awar zama kusa ruwan ta ɓ o. Wani lokaci takan yin wanka da habdi ko kasa ko wani rairayi maras tsafta. Irin wannan dabi’a c eta sa ake ganinta maras tsafta.

d.     Cin najasa. Kaza na cin kashin yara ko na manya a bayan gida. Cin kasha kuwa ba ɗ abi’a ce mai kyau ba. Don haka Bahaushe ya tsane ta a irin wannan yanayi

e.      Shan ƙ wai; Yayinda Bahaushe yake ajiye kaza don amfani da ita a wasu mahallai na abinci ko samun ‘ya’yan kaji domin nama ko kasuwanci, akwai kajin da ke sa mai su yin hasara. Ana samun irin wannan hasara ta shan ƙ wai. Takan sha ƙ wan da ta nasa kafin tai kwanciya, ko kuma a lokacin da take kan kwanciya da ƙ yan ƙ asa. Bahaushe ba ya son hasarar ko da ƙ wai ɗ aya ne na kazarsa. Ya fi so ta ƙ yan ƙ yashe su baki ɗ aya.

f.        Tono; Hauswa na ka ce kaza mai yawan tone-tone. Kaza takan yi wannan ne domin ta samu kwari da tsutsa da ke cikin kasa a matsayin abinci gare ta ko ya’yanta. Sakamakon haka takan ɓ ata shar a r da aka yi ko kuma ta t ay a r da ƙ ura a cikin gida .

g.      Kafar-kai: Kazan na da kafewa, a yi kora har a gaji ba ta tafiya. A wasu lokutta sai an hada da kare sannan a kora tat a gudu ko ta bar wuri. Ita ma kazar da ta saba da shiga cikin daki ko hawan tabarma, bat a bari sai an kai ruwa rana da iyalin gida.

h.      Fa ɗ a/ sa ƙƙ wata: idan kaza ta fito daga ƙ yan ƙ yasa, a koyaushe za a tarar tana da fa ɗ a da yara ko wasu kaji. Wannan kan kai ga sa ƙƙ wata ko c i zo domin ta kare ‘ya’yanta daga yara ko wasu kaji.

Irin wa ɗ annan abubuwa da aka lissafa a sama na daga cikin wasu illoli dab AHAUSHE ya fahimta na halaye da dabi’un kazar Hausa. Wannan baa bin mamaki ne ba, domin Hausawa na cewa mutun dan tara ne bai cika na goma ba. Manufa dukda cewa mafi yawanci daga rayuwarta abin amfani ce ga Bahaushe, amma, a kan samu wasu muhallai da take da gaira ko sabani.

7.0 Tasirin Zamantakewar Hausawa da Kaza a Adabin Baka

Adabi ya kasance wata taska da ake iya adana dukkan al’adun al’umma daga aure da haihua har zuwa mutuwa. Dalilin wannan bayani shi ne, domin duk wani abu da ake nema game da al’umma, za a iya samun sa a cikin adabi al’ummar. Adabi yakan fito da darajar al’umma a idon duniya. Akwai ir-iren adabi guda biyu a ƙ asar Hausa. Adabin gargajiya da adabin zamani. A wani ƙ aulin akan kira su adabin baka da rubutaccen adabi.

Masana sun ba da bayani game da adabin baka wa ɗ anda ra’ayoyinsu ke da ala ƙ a makusanciya . Alal misali, Bunza, (1995) ya ce “Adabin baka na Hausa shi ne wanda ake ya ɗ a shi, ake aikata shi, ake tsara shi da adana shi duk da ka”. Shi kuma Ibrahim, (1985) ya bayyana adabin baka a matsayin abin da Hausawa suka gada tun iyaye da kakanni. Su ma Muhammad, (2003) da Junaidu, I. da ‘Yar’aduwa, T. M. (2007) suna da madangancin wannan ra’ayi.

 Ganin irin yadda Bahaushe ya kusanci kiwo da zama da kaji da yake amfani da su, don abinci da biyan wasu bukatoci na rayuwa da gina tattalin arzikinsa, ya sa rayuwarsa ta yau da kullum a baki- ɗ aya take da ala ƙ a da irin abubuwan da yake da dangantaka ko zumunci da su, zamani mai tsawo zuwa yau, Aminu, (2015).. Wannan ne ya haifar da wata makusanciyar dangantaka a tsakanin Bahaushe da kaza a dukan ɓ angarorin rauwa. Ana iya tabbatar da haka ta hanyar kafa hujja da da ɗ a dd un hikimomin magana da tatsuniya ko labaran Hausawa. Wannan kan faru a lokacin maganar yau da kullum a tsakanin jama’a ta furta maganganu ko yin tsokaci na habaici ko gugar zana da karin magana, ko labarai na gargajiya, bisa kwatance da rayuwar kaza a gidan Bahaushe. Bisa ga al’adar Bahaushe duk abin da ya samu matsayi a adabin bakan Hausa, abu ne da ya ratsa tunani da rayuwarsa ta yau da kullum. Za a iya fahimtar haka idan aka yi la’akari da yadda aka yi amfani da suna ko halin rayuwar kaji domin gina wa ɗ annan karin maganganu na azanci da ake isar da sa ƙ onni, kamar haka:

7.1 Tasirin Kaza a Cikin Karin Magana

Karin magana, wata dabara ce ta dun ƙ ule, magana a cikin ‘yan kalmomi ta amfani da hikima a ta ƙ aice, yayin da wasu ke yi mata kallon dun ƙ ulalliyar magana wadda ke ɗ auke da sharhi a kan rayuwa cikin hikima da fasaha. Tana nuna ƙ warewar harshe da ƙ ara wa magana armashi, bayan zamanta madubi na al’adun al’umma.

Da yawa a cikin Karin maganar Hausa Hausawa maza da mata kan yi amfani da karin magana mai ala ƙ a da kaza domin isar da wani sa ƙ o fito da hoton wani abu ko wata dangantaka zuwa ga wanda yake son isarwa. Alal misali, “A bar kaza cikin gashinta”. Wannan karin magana ne da ke ƙ o ƙ arin nuna hali ko bukatar sirrantawa ko rufin asiri a tsakanin mai magana da masu sauraro. Akan gabatar da irin wannan domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wani al’amari mai rikitarwa. Hakan ba ya rasa nasaba da halin Bahaushe na bukatar rufa wa juna asiri a addinance.

Bayan haka idan Bahaushe na cikin wani tashin hankali ko da alamunsa ya fahimta, ba shakka yakan ɗ auki matakai na janyo hankalin makusantansa ko dangi ko ma ƙ wabcinsa domin samun taimako ko ba da shawara. Haka yake yake, a irin ƙ arar da kaza kan yi idan ta za a yanka ta, kusan duk wanda ke kusa yakan ji ƙ ararta. Saboda haka idan akwai wani hali na tashin hankali ga wani akan gabatar da Karin Magana mai cewa “Awai! Kaza ta ji wu ƙ a a wuya”.

A halayen Ɗ an’adam akwai nuna iyawa da ƙ wazo da ƙ asaita da za ƙ ewa a wurin aiwatar da wani abu. To haka shi ma Bahaushe yakan samu kansa a cikin irin wannan hali da yanayi na rayuwa, nan take za a yi masa garga ɗ i a cikin Karin Magana da ke nuna masa ya wuce wuri. A irin wannan ne ake samun Karin maganar da ke cewa “Abin mamaki kaza ta jawo muzuru kwanan gida” ko kuma

‘Karambanin kaza auren muzuru’. Wato a duk inda aka frta irin wannan karin magana, an aikata abin da bai dace ba, kuma ana zaton mummunan sakamako tare da shi. A cikin al’ummar Hausawa akan samu irin wannan ko a tsakanin matasa da masu sana’ar maza.

Wani al’amari ko yanayi da ake iya amfani da Karin Magana mai ala ƙ a da kaza, musamman wurin kwananta (akurki) shi ne a inda mutun ya shiga halin ƙ a ƙ a-nikan-yi, hali na wahala na rashin mafita. A nan tilas ya yi wa kansa mafita domin ceton rayuwarsa don haka a wurin ba da labari yakan yi amfani da Karin maganar da ke cewa “Akurki ma abin kwana ne idan rana ta ɓ aci” wato Karin Magana ce mai kama da “wanda yace duhu, to bai ji zawo ba”. Idan aka duba ba sunan kaza a ciki, amma a sanadinta ne aka samu akurki. Don haka Karin Magana ne mai ala ƙ a da kaza, sanadiyar zama-tare.

 Bayan haka akwai jerin Karin maganganu dake fitar da wani yanayi ko hali ko ɗ abi’a irin ta rayuwar Hausawa da a kaikaice ake tsarma Karin Magana mai ala ƙ a da kaza domin samun mafita ko garga ɗ i ko horarwa da dai makamantanu ga misalansu:

Karin Magana

Jigonta

Ala ƙ a da darasi

Albarkacin kaza ƙ adangare kan sha ruwan kasko

Samun Alfarma

Darajar wani, wani kan samu

Buki na farar kaza, balbela ba gayyata akai ba

Bukin Dangi

Gayyata da zumunci

Ana muzuru ana shaho, zakaran da Allah ya nufa da cara sai ya yi

Arziki da samu

ƙ addarorin rayuwa

Fatara mai sa a sayar da kazar kwanci

Talauci

Neman mafita

Wuya mai sa a sayar da damen iri

In ka ga da ƙ walwar kaza kasuwa, in babu gurdumu/ ɗ an hoda , akwai shan ƙ wai

Ciwo da rashin ɗ a’a

Cuta da cutarwa

Wurin tone -tone kaza ta tono wu ƙ ar yanka ta

Garga ɗ i

Tsaro

Kada kaza ta yi murna don ta ga ana jan hanjin ‘yar’uwarta

Garga ɗ i/ jin ƙ ai

In ka ga gemun ɗ an uwanka ya kama da wuta..

Inda saniyar gaba ta sha ruwa na ta baya kan sha

 

7.2 Tasirin Kaza a Cikin Tatsuniya

Tatsuniya wata al’ada wani tsararren labari ne da ke ɗ auke da hikima da nuna ƙ warewa da shiryawa da nuni zuwa ga halaye na gari da tarbiyatarwa da nisha ɗ antarwa.

Ɗ an Kaza Mai Layar Ƙ amzo

Ɗ an Kaza ne mai layar ƙ amzo, ya kama hanya zai je kar ɓ ar bashin babansa. Kan hanya ya ha ɗ u da Kyanwa. Ta ce “ ɗ an kaza mai layar ƙ anzo ina za ka” ya ce “zan je kar ɓ ar bashi ne”. Ta ce “ina zuwa”. Ya ɗ auke ta ya ka ɗ a cikin burgame. Yana cikin tafiya. Ya ha ɗ u da kura, ta ce tana zuwa, ya ka ɗ a ta cikin burgame. Ya ha ɗ u da zaki ya ce yana binsa. Ya ɗ auka ya ka ɗ a shi cikin burgame, ya ha ɗ u da talalla ɓ iya da ruwa. Da ya isa mutanen suka ce wanga wane irin ɗ an kaza ne marar kunya. A ha ɗ a shi da ɓ era, sai nan take ya fitar da kyanwa, ta cinye ɓ era. Aka sa shi cikin akuyoyi don su take shi, sai kura ta fito ta cinye su. Mutane suka ɗ auko ta ɓ arya za su buge shi, sai talalla ɓ iya ta kwashe su. Aka ɗ ebo wuta, ruwa suka wanke wuta. ƙ urungus.

7.3 Tasirin Kaza a Cikin Kacici-kacici

Kacici – kacici a matsayin adabin baka tambaya ce ko tambayoyi na wasa ƙ wa ƙ walwa kuma zaunannu masu zaunannun amsoshi da mafi yawan lokuta yara kan yi a tsakaninsu.

Misali: -Yadda kaza takan yi ƙ wan nan, haka ƙ wan nan yaka yin kaza

 - Da kwai da kaza, wa ya riga duniya

7.4 Tasirin Kaza a Cikin Kirari

Shi ma kirari yana ɗ aya daga cikin adabin bakan Bahaushe wanda ya gada kaka da kakanni. Ana yin kirari a lokuta daban-dabam. Wasu na ganin sarakuna da muhimman mutane ka ɗ ai ake yi wa kirari domin fitar da kamanni da halayensu. Ko ta yaya, kirari ya yi kama da yabo. ‘Yan ma’abba da maro ƙ a da masunta da ‘yan wasan kokawa ko dambe da ‘yan tauri da mafarauta duk suna yin kirari yayin da suke gudanar da wasanninsu ko sana’o’insu.

Kirarin da Sunan Kaza

Kirari

Asali

Alaka da darasi

Zakara mai neman suna ba da ƙ waya ka ci tsakuwa

Magidanci da ciyarwa

Daukar nauyi da nuna isa

Kaza uwar tone-tone

Zama tare

Yawan tayar da zaune-tsaye

Zakaran gwajin dafi

Tsaro a zamantakewa

Nuna zaruntaka

Ɗ an Kaza Mai Layar Ƙ amzo

 

Sihiri

Siddabaru

Kaza a ci a goge baki

Cimaka

Tsafta da nuna hadama ko butulci

Ɗ an kaza samu ka ƙ i dangi

Nakkaso cikin habaici

Raunan matsayi

 

7.5 Tasirin Kaza a Cikin Habaici

Wani ɓ angare na adabin bakan Hausa shi ne Habaici. Habaici zance ne da ake yi da ɓ oyayyar ma’ana wanda ke ƙ auke da wata manufa ta daban wadda ba kowa ya san tab a, sai wanda aka yi wa. Akan gina habaici a kan wani abu da ake tsammanin ya ta ɓ a faruwa.

Idan aka kalli ta ƙ aitatun bayanai da ke sama, ana iya fahimtar cewa dukansu sassa ne na adabin bakan Hausa, kuma bayanan da aka gabatar suna da ala ƙ a ta kusa da wannan takarda.

a.      Ko ba a gwada ba linzami ya fi ƙ arfin bakin kaza.- FIFIKO

b.      Mu aka wa sammu a ƙ asa, da zakara ya tono wu ƙ a a ƙ asa.- WAIBUWA

c.       Ba samun abin duniya ba wurin ci nai.- HADAMA

d.     Da walakin tuwon ‘yan ga aiki da guraye.- WUCE GONA DA IRI/TUHUMA

e.      Wata sabuwa kaza ta ji shi ƙ ar dare.- KWANKWANTO/ZAMANANCI

f.        Kaza a ci a goge baki.- HA Ɗ AMA/TSAFTA/BUTULCI - KA WA MUTUM RANA YA YI MA DARE

g.      In fitsari banza ne kaza ta yi.- ABIN DA BA YA YIYUWA/GAGARA

h.      Ɗ an kaza in ka samu gudani dangi.- HADAMA

i.        Cin dan ƙ o har da su kaza.- ABU YA YI BANZA

7 .6 Tasirin Kaza a Salon Magana

Yadda ƙ wan nan yakan yi kaza, haka kaza takan yi ƙ wan nan.

7 .7 Tasirin Kaza a Labara Hausa

Labarin Muzuru da Zakara da Kare

Wata rana da Mazuru da zakara ana wasa, sai kwa ɗ ayi ya kama mazuru. Nan da nan, ya canja ra’ayinsa ya kame zakara da niyyar ya cinye shi. Ya kama hanya zuwa bayan gari domin ya cika gurinsa, sai suka ha ɗ u da kare ya fito yawon neman abinci. Sai ya shiga tsakanin zakara da mazuru, ya ce me ke faruwa? Nan take muzuru ya ce “Ai wasa ce muke yi”. Zakara ya ce ‘Haka ake wasa da kaina a cikin bakinka? Nan take mazuru ya saki zakara ya gudu, shi ma ya ranta a cikin na kare don kada kare ya gama da shi. Ashe ko gaba da gabanta.

8 .0 Na ɗ ewa

Daga bayanan da suka gabata ana iya fahimtar cewa akwai tasirin adabin baka a zamantakewar kazar Hausa da al’ummar Hausawa. Bincike ya yi amfani da wasu sassan adabin baka da aka gina da kazar Hausa, aka fito da wani sashe na falsafar rayuwa da zamantakewa a cikin al’umma. Daga ciki, akwai tsarin rayuwa da halaye da ɗ abi’u da fa ɗ akarwa da makamantansu. Don haka yana da muhimmanci manazarta su fa ɗ a ɗ a kafofin bincike ta hanyar duban dangantakar Hausawa da wasu abubuwa ko halittu da suke zaune tare, maimakon mayar da hankali kan al’adun aure da haihuwa da mutuwa da suka shafi jama’a. wannan zai inganta fito hoton al’umma a wasu muhallan rayuwa.

Manazarta

Abdullahi, I. S. S. (2008) Bamaguje da Ɗ an Akuya: Ƙ auna ko Ƙ iyayya? Departmental Seminar, Department of Nigerian Languages Sokoto: Usmanu Danfodiyo Universty.

Adamu, M. (1976), “The Spread of Hausa Culture in West Africa 1700 – 1900” Savannah A Journal of the Environmental and Social Sciences. Zaria: No 5. Vol. 1, Ahmadu Bello University.

Adoro, A. L. (2013) Halin Zamantakewar Hausawa Tsakanin Jiya da Yau, in Experts of International Seminar on Ta ɓ ar ɓ arewar Al’adun Hausawa (The Deterioration of Hausa Culture) Organised by Katsina State History and Culture Bureau and Umaru Musa ‘Yar’adua University, Katsina. Zaria: Ahmadu Bello University, Press.

Ajayi, F.O. 2010. Nigerian Indigenous Chicken: A Valuable Genetic Resource for Meat and Egg Production.  Asian Journal of Poultry Science, 4: 164-172.

Alhassan, H. (1982). Zaman Hausawa Zaria, A.B.U. Press.

Aminu, N. (2015) Kaza ga Bahaushe, Jiya da Yau, Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies. Special Edition. Department of Nigerian Languages, Bayero University, Kano. Vol. 1 no. 1, Pages 631 – 638. ISSN: 2141-9434, Zaria: Ahmadu Bello University, Press.

Ayieko, D.M.O. and Bett, E.K. and Kabuage, L.W. (2014) Profitability of Indigenous Chicken: The Case of Producers in Makueni County, Kenya. Journal of Economics and Sustainable Development, Vol 5, No. 11, 2014. ISSN 222-2855.

Blench, R. (1997) Neglected Species, Livelihoods and Biodiversity in Difficult Areas: How Should the Public Sector Respond? In Natural Resources Perspectives, Number 23, Sept. 1997.

Chicken – Wikipedia, the Free Encyclopedia- en.wikipedia.org/wiki/chicken – Retrieved 08/11.2023, 8:58 p.m

Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano (2006) Ƙ amusun Hausa. Zaria, Ahmadu Bello University Press.

Copland, J.W. and Alders, R. G. (2005) The comparative advantages of village or smallholder poultry in rural development, in the Proceedings of an international conference held in Dar es Salaam, Tanzania, 5–7 October 2005. ACIAR

Ɗ ahiru, I. (2012) Nuni Cikin Rayuwa Daga Labaran Dabbobi, Kundin Digiri na Biyu,. Department of Nigerian Languages, Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.

Ibrahim, A. A, Aliyu, J., Wada, N.I and Hassan, A. M (2012) Effect of Sex and Genetype on Blood Serum Electrolylete and Biochemical Parameters of Nigerian Indigenous Chickens, Iranian Journal of Applied Science, 2012, Vol, 2 No. 4, PP. 361-365, Dec. 2012.

Ishaq, Y. (2013) Sirrin Mijinka a Tafin Hannunka Bugawar Da ɗ in Kowa Publishers, Kano, Nijeriya

Junaidu, I. da ‘Yar’aduwa, T. M. (2007) Harshe da Adabin Hausa a Kamalle don Manyan Makarantun Sakandare. Zaria: Spectrum Books Limited.

Maikasuwa, M. A. and Jabo, M. S. M. (2011) Profitability of Backyard Poultry Farming in Sokoto Metropolis, Sokoto State, North-West, Nigeria, in Nigerian Journal of Basic and Applied Science, 2011, 19 (1): 111- 115

Makarantar Hausa (2007) ‘Bahaushen Zakara ya Fi Mutum Iya Zama da Iyali, 1 & 2, Yuni da Yuli, Fitowa ta Biyu da ta Uku, shafi 42

Muhammad, Y. M. (2003) Adabin Hausa Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Nwagu, B.I. (2002). Production and Management of Indigenous Poultry Species. A Training Manual in National Training Workshop on Poultry Production in Nigerian National Animal Production Research Institute, Shika, Zaria. 10 – 26pp.

Nwosu, C. C. (1979) Characterization of the Local Chicken in Nigeria and its Potential for Egg and Meat Production. Proceedings of the First International Seminar on Poultry Production, December 11-13, A.B.U Zaria, Pp 187-210.

Sharif, H. S. (BS) Ƙ asaitacciyar Macce mai Mallakar Mijinta, Al-Amin Bookshop, Mandawari Printing Press, Kano.

Rataye:

Kaza a Karin Maganar Hausa

A bar kaza a cikin gashinta

A wai! Kaza ta ji wu ƙ a a wuya

Abin mamaki kaza ta jawo muzuru kwanan gida

Akurki ma abin kwana ne idan rana ta ɗ aci

Albarkacin kaza ƙ adangare kan sha ruwan kasko

Ana muzuru ana shaho, zakaran da Allah ya nufa da cara sai ya yi

Buki na farar kaza, balbela ba gayyata akai ba

Da walakin tuwon danga aiki da guraye

Fatara mai sa a sayar da kazar kwanci

Hushin kaza ya huce a kan dami

In ka ga da ƙ walwar kaza kasuwa, in babu gurdumu/ ɗ an hoda akwai shan ƙ wai.

Kada kaza ta tono wu ƙ ar yanka ta

Kada kaza ta yi murna don ta ga ana jan hanjin ‘yar’uwarta

Karambanin kaza auren muzuru.

Kaza mai ‘ya’ya ke gudun shirwa.

ƙ wai a baka ya fi kaza a akurki.

ƙ wai ma ya yi wayo balle ɗ an kaza

Maganar banza zakara ya taka wu ƙ a

Mai kaza a aljihu bai han ƙ urin has

Rashin sani kaza ta kwana a kan dami

Raina da ƙ una kaza ta kwana kan dami

Sabo da kaza ba ya hana a yanka ta

Wanda ya ci kaza shi ke da ita

Kaza a Habaici Bahaushe

Mu aka wa sammu a ƙ asa, da zakara ya tono wu ƙ a a ƙ asa.

Ko ba a gwada ba linzami ya fi ƙ arfin bakin kaza.

Ba samun abin duniya ba wurin ci nai.

Da walakin tuwon ‘yan ga aiki da guraye.

Wata sabuwa kaza ta ji shi ƙ ar dare.

Kaza a ci a goge baki.

In fitsari banza ne kaza ta yi.

Ɗ an kaza in ka samu gudani dangi.

Cin dan ƙ o har da su kaza.

Kaza a Salon Maganar Hausa

Yadda ƙ wan nan yakan yi kaza, haka kaza takan yi ƙ wan nan.

Kaza a Kirarin Hausa

Zakara mai neman suna ba da ƙ waya ka ci tsakuwa

Kaza uwar tone-tone

Zakaran gwajin dafi

 

Post a Comment

0 Comments