Ticker

Hukuncin Sanya Turare Ga Mata

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam dafatan kowa lfy Malam Ni ce na sanya turare mai kamshi asaman kayana tom danaje gidan kanin mamata sai yake min fada wai hakan bai dace ba infita ina kamshin turare har jama'ar waje suji inason karin bayani malam Nagode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum Salaam Warahmatallahi Wabarkatahu

To ‘yar’uwa ya haramta ga mace Baliga ta sanya turare, ta fita unguwa, saboda faɗin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam “Duk matar da ta sanya turare, ta wuce ta wani majalisi, to ta zama mazinaciya, kamar yadda Abu dawud ya rawaito.

A wani hadisin kuma yana cewa: “Duk matar da ta sanya turare, kar ta halarci sallar Isha tare da mu.

Daga Ubaidu Ya ce: "Lallai Abu Hurairata, ya haɗu dawata mata wacce ta sanya Turare, Sai Yace Mata: Ina kikeson zuwa ne haka Baiwar Allah? Sai matar tace: Masallaci zanje. Sai Ya ce: Saboda za ki Masallacin ne kika sanya Turare? Sai matar tace eh, Sai Abu Hurairata Yace Lallai naji Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Yace "Duk matar da ta sanya turare tafita da nufin zuwa Masallaci, to Allah mai girma da Ɗaukaka ba zai karbi sallarta ba har saita dawo ta yi wanka Irin wankanta na Janaba."

{Ibn majah ne ya ruwaito shi acikin KITABUL FITAN babin Fitnatun Nisa'i (4002)

Malaman Muslunci sun inganta hadisin, Sheik Nasurudden albany yayi ta'aliqi akan haka, yakara dacewa"Idan har(sanya turare saboda) zuwa Masallaci yazama Haramun toya (ake tunanin) hukuncinsa zai Kasance akan wacce ta sanya shi saboda zuwa Kasuwa, titi da kuma hanyoyi? Babu makawa yin hakan yafi tsananin haramci, Amma ya halatta taci ado maikyau da turare mai kamshi agidan mijinta da kuma muharranta kamar yanda yazo a Alkur'ani suratul an-nor (31)

Imam at-taimey yana fada acikin (Az-awajir 36/2) Lallai fitar mace da za tayi tana mai sanya Turare kuma tana mai kwalliya, yana daga cikin MANYAN LAIFUFFUKA kuma koda mijinta ne yayi Mata izini, kuma duk Waɗannan Hadisan waɗanda suke nuna haramcin sanya turare ga mace idan za ta fita waje) baki Ɗayansu sun shafi gaba ɗayan lokuta ne Mukhtasar Kitabu jalbab Al-mar'atul muslimah (shafi na 44)].

Nassoshin da suka gabata suna haramta sanya turare ga mace balagaggiya idan za ta fita, kuma ba su bambance tsakanin matar aure ba da budurwa ko bazawara, wannan sai ya nuna gamewarsu ga dukkan mata waɗanda sharia ta hau kansu, tun da ba’a samu abin da ya keɓance wasu nau’i ba, sannan kuma an haramta sanya turaren ne: saboda yana kaiwa zuwa tada sha’awar Maza, wannan kuma baya bambanta tsakanin matar aure da wacce ba ta yi ba. Amma za ta iya sanyawa ta zauna a gida mijinta ya ji kamshi, in ta yi hakan za ta samu lada. Haka ma budurwa, za ta iya sanyawa a tsakanin ‘yan’uwanta mata, ko gaban muharramanta waɗanda ta san ba za su yi sha’awarta ba.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments