Hukuncin Wanda Ya Yiwa Allah Bakance

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Salem Allah gafarta Mallam, kwanaki ina ta neman aiki ban samu ba, sai nayi ta addu'a har nayi bakace cewa idan Allah ya bani aikin nan nayi alkawarin zan yi sadakan naira dubu ashirin daga cikin albashina na farko ga masu tsananin bukata. Sai kuma rannan da aka biya salary nayi hatsari da motata kuma gyaranta zai ci kuɗi da yawa, sannan kuma ga bukatan iyaye da Iyali.

    Tambaya na anan shi ne

    1. Zan iya jinkirta wannan sadakan da na yiwa Allah alkawari zuwa wata Mai zuwa idan aka biya albashin?

    2. zan iya bawa wani sadaqan cikin dangi na mubakata ko kuma dole ne sai wasu awaje.

    Wallahi banaso in butulci in karya alkawari da nayiwa Allah SWT. Nagode

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

    Shi yin bakance halal ne a addinin Musulunci. Shi ne duk wani alkawarin da mutum zai daukar wa kansa na yin wata ibada ta musamman bisa sharadin cikar wata bukata tasa. Kuma idan har wannan bukatar tasa ta yiwu, to fa wajibi ne akansa sai ya aikata abinda yayi wa Allah alkawarin akansa.

    Allah Madaukakin Sarki yace

    وَمَا أَنفَقْتُم مِّن نَّفَقَةٍ أَوْ نَذَرْتُم مِّن نَّذْرٍ فَإِنَّ اللَّهَ يَعْلَمُهُ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ

    Kuma abin da kuka ciyar daga ciyarwa, ko kuka cika alwashi daga wani bakance, to, lalle ne, Allah Yana sanin sa. Kuma azzalumai ba su da wasu mataimaka. (Suratul Baqarah ayah ta 270).

    Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya ce: "Wanda yayi bakancen zai aikata wani aikin bin Allah, to lallai ya bishi. Wanda kuwa yayi bakancen saɓa wa Allah, to kar ya saɓeshi".

    (Bukhariy da Muslim ne suka ruwaitoshi daga Nana A'ishah r.a.).

    Don haka tunda har Allah ya biya maka bukatarka, to wajibi ne kai kuma ka nuna masa godiyarka ta hanyar aikata abinda kayi alkawari akanka tunda kana da ikon yin hakan. Amma Qin cika alkawarin daga ɓangarenka zai iya zama laifi ko kuma rashin ladabi ga Ubangiji (SWT).

    Shawarar da zan baka anan ita ce idan har yin sadakar 20,000 ɗin nan ba zai janyo afkuwar yunwa ko rashin abinci ga iyayenka da iyalanka ba, to kada ka jinkirtashi. Amma idan yin hakan zai janyo tozartar da hakkokin mahaifa ko iyalanka, to ka iya jinkirtawa zuwa wani watan mai zuwa in sha Allahu.

    WALLAHU A'ALAM.

    DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.