Idan Na Kusanci Mijina Yana Kyamata, Menene Mafita?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum Malam. Ni ce ina da miji, a duk lokacin da zan zo kusa dashi sai yace min barci yake ji, ai shari'a ta hana na dame shi, a haka zamu yi kusan wata ba abin da ya shiga tsakanina dashi. Allah taimaki Malam, menene mafita?

    𝐀𝐌𝐒��❗️

    Wa alaikum assalam. Ki tambaye shi dalilin da yasa yake yin hakan, zai iya yiwuwa kin ɓata masa rai ko kuma akwai wata matsalar, amma ta hanyar tambaya ko shigar magabata lamura za su iya fitowa fili. Shari'a ba ta halattawa namiji ya ƙi saduwa da matarsa ba da gangan, saboda nau'i ne na cutarwa. Yana daga cikin manufofin aure katange ma'aurata daga kallon haram.

    Allah ne mafi sani.

    Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.