Ticker

Iddar Mace Mai Jego

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum wa Rahmatullah. Malam don Allah ina neman karin bayani akan IDDAH ko TAKABA akan matar da mijinta ya rasu bayan ta hahihu da kwana uku (3). Shin dagaske ne za tayi kwana arba'in (40) ne na TAKABA sai kuma wata uku na IDDAH? Toh idan kuma wacce bata jini ce a lokacin shayarwa to minene hukuncin IDDARTA? Nagode. Allah saka da mafificin Alkairi

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Matar da mijinta ya rasu bayan ta haihu da 'yan kwanaki, iddar takaba za tayi (wato iddatul wafat) wata huɗu da kwana goma kamar yadda Allah ya faɗa acikin Alqur'ani

وَالَّذِينَ يُتَوَفَّوْنَ مِنْكُمْ وَيَذَرُونَ أَزْوَاجًا يَتَرَبَّصْنَ بِأَنْفُسِهِنَّ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَعَشْرًا ۖ فَإِذَا بَلَغْنَ أَجَلَهُنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ فِيمَا فَعَلْنَ فِي أَنْفُسِهِنَّ بِالْمَعْرُوفِ ۗ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ

Kuma waɗanda suke mutuwa daga gare ku suna barin matan aure, matan suna jinkiri da kansu wata huɗu da kwana goma. To, idan sun isa ga ajalinsu, to, babu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu ga al´ada. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne. (suratul Bakara aya 234)

Al Imam Alhafiz Ibnu Katheer acikin tafseerin wannan ayar ya ce: wannan umurni ne daga Allah ga matayen da mazajensu suka rasu suka barsu cewa zasuyi iddar wata huɗu da kwanaki goma. Kuma wannan hukuncin ya kunshi matar da mijin ya taɓa saduwa da ita har wacce ma mijin bai taɓa sadu da ita ba.

Hujjah ita ce wannan ayar da aka ambata, da kuma hadisin nan wanda Imamu Ahmad ya riwaitoshi acikin Musnad (juzu'i na 3 shafi na 480) da ma'abota sunan, Imam Abu Dawud (hadisi na 2114) da Tirmidhiy (hadisi na 1145) da Ibnu Maajah (hadisi na 1891) Kuma Tirmidhiy ya inganta hadisin, daga Sayyiduna Abdullahi 'dan Mas'ud (ra)

Wasu mutane sun tambayeshi game da Mutumin da ya auri mace kuma ya rasu tun kafin ya tare da ita (wato bai taɓa saduwa da ita ba).

Sai yace zan baku fatawa bisa ra'ayina. Idan na dace to wannan daga Allah ne. Idan kuma nayi kuskure to wannan daga gareni ne kuma daga shaiɗan.

Sannan ya yanke hukuncin cewar "Tana da cikakken sadaqi, za tayi masa takaba, kuma tana da gadonsa".

Daga nan sai Ma'aqal bn Sinaan Al-Ashja'iy (rta) ya mike ya ce: " Na shaida hakika naji Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yayi irin wannan hukuncin game da (Wata mata mai suna) BURU'U BINTU WASHIQ"

Amma idan miji ya rasu ya bar matarsa da ciki (wato juna-biyu) to da zarar ta sauke cikinta (ta haihu) to shike nan ta kammala takabarta. Kamar yadda ya faru ga wata mata mai suna Subai'atul Aslamiyyah matar Sahabin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam mai suna Sa'adu bn Khaulah (rta). Ta haihu bayan sati biyu da rasuwar mijinta, Kuma Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya umurceta ta yi aure idan ta samu miji.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments