Ticker

Ina Yawan Fitar Da Maniyyi, Saboda Mijina Ba Lafiya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Dr., mace ce mijinta ba shi da lafiyar aure tsawon lokaci, sai ya kasance tana yawan releasing, ba sai ta yi wani dogon tunani na sha'awa ba, ya matsayin ibadarta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To gaskiya abin da yake daidai shi ne, mijinta ya nemi magani, in kuma bai samu ba, ana iya raba auren, tunda yana daga cikin manufofin aure, katange ma'aurata daga faɗawa haramun, kamar yadda shahararren hadisinnan ya tabbatar.

Yawan fitar maniyyi zai iya zama lalurar da za ta iya haifar da saukin Shari'a, sai dai naki ba zai zama lalura ba, saboda iyayenki za su iya lazimtawa mijinki neman magani, in kuma bai samu ba, za ku iya rabuwa, Allah ya azurta kowa daga falalarsa. Ci gaba da zamanku a wannan yanayin yana iya jefa ki cikin haɗari. Mata nawa ne suka zama mazinata ta hanyar wannan sababin?

Ya wajaba ki yi wanka duk lokacin da maniyyin ya fita, tunda ya fita ne ta hanyar jin daɗi.

Allah ne mafi sani.

Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBqfaiPwf28l

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments