Kar Mutum Ya Nemi Aure A Kan Neman Auren Ɗan’uwansa.

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Mutun ne Sai a bayan da aka ƙulla musu aure da matarsa har ma ta tare ne sannan ya san cewa a lokacin da ya je neman auren ta an riga an sa mata rana da wani. Shi ne yake tambaya wai ina matsayin aurensa da ita a yanzu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Ya tabbata a cikin hadisi sahihi daga Manzon Allaah Annabi Muhammad (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« لاَ يَبِعِ الرَّجُلُ عَلَى بَيْعِ أَخِيهِ، وَلاَ يَخْطُبْ عَلَى خِطْبَةِ أَخِيهِ ».

Kar wani mutum ya yi ciniki a kan cinikin ɗan’uwansa, kuma kar ya nemi aure a kan neman auren ɗan’uwansa. (Sahih Al-Bukhaariy: 5142, Sahih Muslim: 3521).

Daga wannan hadisin malamai sun gano cewa:

1. Haram ne a nemi auren mace idan dai ita matar ko waliyinta sun amsa wa wani mai neman ta da farko.

2. Yana iya cigaba da neman matar da aka riga shi nema idan ya san ba a amsa wa mai neman na farko ba.

3. Kuma yana cigaba da neman ta idan shi kansa mai neman da farko ya yi masa izinin cewa ya je ya nema.

4. Haka kuma yana cigaba da neman ta idan ya tabbatar cewa mai neman na farko ya fasa cigaba da neman.

5. Idan ya shiga neman auren macen da bai san wani ya riga shi ba, ba shi da wani laifi. Domin ba a kama mutum a kana bin da bai sani ba.

6. Amma idan ya san wani ya riga shi amma bai san ko an amince masa ya cigaba ko ba a amince ba, a nan malamai sun sha bamban

Waɗansu sun janyo hadisin Faatimah Bint Qays wacce a bayan ta gama idda mutane biyu suka zo neman ta, amma kuma har haka Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: Ki auri Usaamah dai. (Sahih Muslim: 1480).

Suka ce: A nan ya tabbatar da neman na-uku a bayan neman mutane biyu ba tare da binciken ko ta amince da magabatan ba.

Waɗansu kuma suna ganin ba zai shiga neman auren ba har sai ya tabbatar tukuna. Ba su ga hujja a cikin hadisin ba.

7. Haka kuma kalmarsa cewa: ‘neman auren ɗan’uwansa’…

Waɗansu sun ce: Ke nan ya halatta ya shiga neman auren wanda ba ɗan’uwa musulmi mai imani ba, kamar neman auren kafiri ko fasiƙi.

Waɗansu kuma suna ganin bai halatta ba. Ba su ga hujja a cikin hadisin ba.

8. Hana neman auren ya haɗa da nema a fili ƙarara da lafuzzansa sanannu, haka kuma ya haɗa da nema a ɓoye kamar ta jirwaye da kamar wanka.

9. Idan mai nema na-biyu ya nemi aurenta bayan ya san an amince da na-farko, sai kuma aka ɗaura auren da shi na-biyun, to auren ya yi a maganar da ta fi inganci a wurin malamai. Sai dai kuma yana da zunubi a kan hakan da ya wajaba ya tuba ga Allaah, ya nemi gafararsa. Saɓanin malaman da suke ganin ƙullin auren bai yi ba.

10. Idan wani ya zo maganar neman auren mace amma kafin ta amsa masa sai kuma wani ya zo alhali bai san da zuwan na-farko ba, malamai sun ce za ta iya yarda da na-biyun ta bar na-farkon saboda hadisin Fatima Bint Qays da ya gabata.

Wannan kaɗan ke nan daga cikin mas’alolin fiqhun wannan mas’alar. A ciki akwai amsar wannan tambayar har da ƙari ma, in shaaal Laah.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RQbbrzgW

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments