Table of Contents
Citation: Sanusi, H. (2024). Kwatanci Tsakanin Korewa a Jumlolin Hausa da Fulatanci: Tsokaci Daga Jumla Maras Aikaitau. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 257-265. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.029.
Kwatanci Tsakanin Korewa a Jumlolin Hausa da Fulatanci: Tsokaci Daga
Jumla Maras Aikaitau
Daga
Hariratu Sanusi
Sashen Harsuna da Al’adun
Afirka
Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria
harirahamzasanusi4@gmail.com
08030812667
Tsakure
Hausa da Fulatanci harsuna ne
mabambanta ta fuskar tarihin tushensu da kuma nahawu. Duk da haka, ba a rasa
wuraren da suka yi kama da juna ta fuskar jumlolinsu ba. Manufar wannan mu
ƙ
ala ita ce
ƙ
o
ƙ
arin kwatanta korewa a
jumloli marasa aikatau na Hausa da na Fulatanci domin a fito da kamancinsu da
kuma bambancinsu ta fuskar gininsu. Hakan zai samu ne ta yin la’akari da
ire-iren wa
ɗ
annan jumloli a harsunan
Hausa da Fulatanci. An yi amfani da hanyar hira daga wasu rukunin Hausawa da
Fulani tare da nazartar littattafan nahawu na harsunan guda biyu wajen tattara
bayanai a wannan bincike. Sannan mai gudanar binciken ta yi amfani da
kasancewarta mai jin Fulatanci kuma manazarciyar harshen Hausa wajen
ƙ
alailaice bayanan da ta samu wa
ɗ
an
da suka kai ga samar da sakamakon wannan bincike. Haka kuma, an
ɗ
aura aikin a kan ra’in
ɗ
oriya na Haliday. A wannan mu
ƙ
ala, an kwatanta ire-iren
jumloli wa
ɗ
anda suka ha
ɗ
a da jumla ganau da jumla
ƙ
addamau da kuma jumla rayau.
An gano cewa akwai kamanci musamman ta fuskar adadin kalmomin korewa da kuma
yadda ake sarrafa su a jumloli marasa aikatau na Hausa da na Fulatanci. Bugu da
ƙ
ari, an gano bambanci a tsakanin jumla korau ta
fuskar kalmomin da suke yin tarayya da
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa wajen isar da sa
ƙ
o.
1.0
Gabatarwa
Hausawa
da Fulani (Ful
ɓ
e) suna zaune tare tun da da
ɗ
ewa har ma ana ikirarin cewa asalinsu guda ne. Johnston (1967:52)
ya bayyana cewa sun ha
ɗ
u ne tun daga
ƙ
arni na tara, wato shekara kusan dubu daya da
ɗ
ari biyu da suka wuce. Sun
zauna tare suna mu’amala tare kuma sun kasance suna tarayya ta wajen bigire da
al’ada da kuma zamantakewa ta yau da kullum. Auratayya ma na kadancewa a
tsakaninsu har suka zama tamkar tsatsonsu
ɗ
aya ne. Asali harsuna ne mabambanta wa
ɗ
anda suka fito daga tsatso mabanbanta
a inda Greenberg (1947) ya bayyana cewa harshen Hausa yana
ɗ
aya daga cikin harsunan Chadi
dangin Afro-Asiatic. Shi kuwa Fulatanci na
ɗ
aya daga harsunan yammacin
Atalantika dangin Niger- kordofanian. Wannan dalili ya sa ake ganin wa
ɗ
annan harusuna ba su da
dangantaka ta tsatso sai dai sun ha
ɗ
a ala
ƙ
a ta zamantakewa da kuma aurataya har ma da al’ada ta fuskar abinci
da sutura da wasu
ɗ
abi’u.
Jumla muhimmiyar aba ce a fagen nazarin harsuna, domin al'umma na
sarrafa ta, yau da kullum, a magance da kuma a rubuce. Asali ma ita ce kan gaba
a fagen ilimin harshe, domin ta ji
ɓ
anci nazari a kan furucin
kalmomi masu jeren ma’ana. Har wa yau, a fannin nazarin ginin jumla ake duba
sigar jumla da tubalan da ke gina jumla ko furuci idan mai magana ya furta ko
marubuci ya rubuta. Masana da dama irin su Arnott (1970) da Galadanci (1976) da
Zaria (1996) da kuma McIntosh (1984) da Zaruk (2005) da Batagarawa (2019), sun
yi ittifakin cewa jumla ta rabu zuwa manyan rassa guda biyu, watau jumla mai
aikatau da kuma maras aikatau. Dalilin yin haka kuwa shi ne, a cewarsu, kowace
irin jumla na
ɗ
aya daga cikin wa
ɗ
anan biyun ne. Jumla mai aikatau, jumla ce wadda aikatau
ɗ
inta ke aiwatar da aiki. Ita
kuwa jumla maras aikatau ba wai ba ta da aikatau ba ne a’a, amma aikatau
ɗ
in ne ba ya aiwatar da aiki.
Asali ma a matsayin mahadi (linking
v
erb) yake, domin yana sadar
da aikau da ita jumlar kanta. Rabe-raben jumla irin su Jumla Sassauka da Har
ɗ
a
ɗɗ
iyar Jumla, na iya zama
jumloli masu aikatau ko marasa aikatau. Saboda da haka ne wannan mu
ƙ
ala ta zabi ta yi kwatancin siga da yadda ake sarrafa korewa a
jumloli marasa aikatau na Hausa da kuma na Fulatanci domin a gano kamanci da
bambancin da ke tsakaninsu a wa
ɗ
annan harsuna.
An yi amfani da hira da wasu rukunin Hausa da Fulani tare da
nazartar littattafan nahawu na harsuna guda biyu wajen tattara bayanan wannan bincike.
Sannan mai binciken ta yi amfani da kasancewarta mai jin Fulatanci kuma
manazarciyar harshen Hausa wajen
ƙ
alailaice bayanan da ta samu da suka kai ga samar da sakamakon
wannan bincike. Dangane
da ra'i
kuwa, takardar ta yi amfani da
Nahawun
Ɗ
oriya wanda Halliday (1985) ya assasa.
Ra’i ne da ya fi bai wa ma’anar yankuna na jumla muhimmanci wajen nazari. Ana
bayani ne a kan abin da
ya
shafi yadda ake
gina ma’ana ta hanyar za
ɓ
a
ɓɓ
un kalmomi da sauran dabarun nahawu kamar karin sauti da makamantansa a jumla.
Bloor da Bloor (2013:2) da Lamidi (2016:17) sun yi
tarayya wajen bayyana cewa, ra’in
ɗ
oriya hanya ce wadda ke nazarin sa
ƙ
on da yake
ƙ
unshe cikin lafazi ko magana. Haka shi
ma O’Donell (2012:2) ya bayyana cewa, ra’in
ɗ
oriya ya danganci yadda ake amfani da harshe domin yin
mu’amala tsakanin mutane.
Shi ya sa ya ba
i
wa
yin
amfani da ma’anar kalmomi a jumla’ muhimmanci a fagen
nazarin harshe.
2.0 Jumloli Marasa Aikatau
Jumloli marasa aikatau
suna dauke da aikatau wadanda ba su aiwatar da aiki.
A cewar Hegedus (2013:58) aikatau da ke bayyana a irin wa
ɗ
anan jumloli ba su aiwatar da aiki, akasari suna sadar da aikau da
jumla ne kawai. Ana kuma iya kiran su da jumloli masu shamaki domin aikatau da
ke tattare da su yana kasancewa shamaki ne tsakanin aikau da kuma jumlolin.
Stennes (1967) da Arnott (1970) da McIntosh (1980) da Newman (2000) da Jaggar
(2001) da kuma
Ɓ
atagarawa (2013), sun
tabbatar da haka. A cewar
Ɓ
atagarawa (2013:60), jumla
maras aikatau a Hausa tana
ɗ
auke da aikatau amma ba a
mastayin kai yake ba, sai dai a mastayin shamaki, tsakanin aikau da jumlar
. S
hi ya sa McIntosh (1984:59) ta kira irin wannan jumla da suna jumla
mai shamaki. Wato irin wannan jumla na da yanki guda ne maimakon yankin suna da
yankin aiki, sai aka sami yankin suna kawai. Ire-iren wannan jumla sun ha
ɗ
a da jumla
ƙ
addamau
da jumla daidaitau da
jumla ganau da jumla nunau da jumla rayau ko zamau da jumla ingantau da
kuma
jumla motsa rai.
2.1 Jumla Ganau
Jumla ce wadda ta ke bayyana aikau ko kuma yin
ƙ
arin bayani a kansa. Shi ya sa masana irin su Stennes (1967:225) da
Arnott (1970:31) da Jaggar (2001:459) da kuma Hegedus (2013:57) suka ce jumla
ce mai nuna kamanni ko kalar abu domin a fahinci abin. A Hausa, masana irin su
Newman (2000:545) da Jaggar 2001:457) da
Ɓ
atagarawa (2013:6-7) sun yi
ittifa
ƙ
in cewa ana amfani ne da dirka (nee/cee) domin sarrafa Jumla Ganau a
Hausa. A Fulatanci kuwa, dirka ba dole ba ne, asali ma, irin wannan jumla a Fulatanci
na samuwa ne ta yin amfani da Sifa.
2.2 Jumla Ƙ addamau
J
umla ce wadda ke gabatar da aikau a cikin jumla. A cewar Newman
(2000:181) da Jaggar (2001:468) jumla ce wadda aka gina ta domin jawo ha
n
kali zuwa
ga
batu da aka riga
da aka
ƙ
addamar ne kawai. A Hausa,
Newman (2000:181) da Jaggar (2001:468) da
Ɓ
atagarawa (2013:84) sun yi
tarayya a kan cewa ana sarrafa Jumla
Ƙ
addamau ta yin amfani da
ɓ
ur
ɓ
ushin ga, wanda Newman (ibid) ya ce ya tsiro daga aikatau ga(ni) → gani. Haka
ma a Fulatanci Stennes (1967:155-166) da Arnott (1970:31) sun ce akwai wasu ke
ɓ
a
ɓɓ
a
ɓ
un kalmomin da ake amfani da
su domin sarrafa irin wannan jumla kamar ndaa
da kuma Hiin. Wannan na nuni da cewa,
ɓ
ur
ɓ
ushin ga a Hausa da kuma ndaa ko hiin a Fulatanci na da amfani matuka a gini irin wannan jumla ta
Hausa da ta Fulatanci.
2.3 Jumla Rayau
J
umla ce mai ishara ga rayuwa. Jespersen a shekarar (1924:155) ya
ƙ
ir
ƙ
iro irin wannan jumla, a inda ya ce jumla ce mai ishara ga rayuwar
abu ko rashinta. Shi ya sa
Ƙ
uirk da Greenbaum (1980:419) suka ce jumla rayau, kawai, jumla ce
mai nuna rayuuwar abu ko rashinta. Shi kuwa Newman (2000:176) ya ce ana furta
jumla rayau ne ta yin amfani da kalmomin maha
ɗ
i akwai da kuma da. A Fulatanci
kuwa Arnott (1970:32) ya ce a amfani ne da
ɓ
ur
ɓ
ushin
ɗ
on
domin sarrafa irin wannan jumla. Saboda haka, za a iya cewa a kan
sarrafa jumla rayau ta yin amfani da
ɗ
aya ko ma duka biyun kalmomin maha
ɗ
i domin furta irin wannan
jumla a Hausa, a Fulatanci kuwa, ana amfani ne da
ɓ
ur
ɓ
ushin
ɗ
on
.
3.0 Korewa
Korewa,
ƙ
wayar ma’ana ce gama-gari wadda take da muhimmaci sosai a nahawu
kuma ana sarrafa samunta a kusan duk
k
an harsunan duniya. Dalili
kuwa shi ne kowac
e
hanyar sadarwa ta
ɗ
an
’
adam
ta
na
ɗ
auke da tunanin kalmar
korewa. A cewar Jackson (2007:43)
,
k
almar korewa na nufin furucin hani ko soke wani al’amari ko
matsayi. Shi kuwa Crystal (2008:323) cewa ya yi, hanya ce ta ginin ma’ana wadda
ta
a’
anta
wani
ɓ
angare na jumla ko kuma
ɗ
ungum
ɗ
in
jumla. Shi ya sa Forest (1993:50-64) ya
ce
,
kalmar korewa
ƙ
wayar ma’ana ce mai canza daraja
r
furuci daga gaskiya zuwa akasin hakan. Ha
ƙ
i
ƙ
a, haka maganar take, tun
da ita kalmar korewa ba wai
tana gabatar da sab
o
n batu ba
ne a’a, ana amfani da ita ne a muhallin da muhawara ta riga ta
kafu. Shi ya sa Mohsen (2011:1) ke cewa
,
amfanin korewa a bayyane
take, domin tana kore wa
ni
al’amari na
ɓ
angaren jumla ko ma na jumlar baki
ɗ
aya. Hageman (1996:71) ya
bayyana cewa
,
ana samun korewa a ya
n
kin aiki na jumla korau domin ita korewa
ɗ
in
ta
na da ala
ƙ
a ta
ƙ
u
t-
da
-
ƙ
u
t
da aikatau a jumla
.
Amma
,
a jumla wadda ta kore
ɓ
angare guda k
a
wai, korewar na ala
ƙ
an
cewa ne da ganga wadda take korewa ka
ɗ
a
i. Saboda haka, ana iya cewa
,
korewa
a
b
u
c
e mai muhammanci a f
a
gen ginin jumla
dangane da nahawun harsunan duniya
.
Sigar korewa ta
kasance
ta
sha bamban a harsuna, a yayin
da wasu harsuna k
an yi
amfani da
ɓ
ur
ɓ
urshin kalma, wasu
kan yi
amfani da
ɗ
afi,
a yayin
da
wasu kuwa
sukan yi amfani
da
kalmar
aikatau ta musamman domin
nuna
kore
wa a cikin
jumla. Hakan
ne
ya sa Dahl (1979:3) da Payne (1985:1) suka raba harsuna bisa ga
irin sigar korewa da k
o
wane
ya
ke amfani da
ita
. Wato rukuni uku ke nan. Kodayake
,
wa
ɗ
a
n
nan
nau’o’i
n sigar korewa su ake samu a mafi akasarin harsunan duniya, Hausa
da Fulatanci ma ba a bar su a baya ba tun
da
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa a wa
ɗ
a
n
nan harsuna biyu kan yi amfani da
ɗ
aya ko
ma biyun cikin ukun.
A Nahawun Hausa, masana da
manazarta da dama irin su Galadanci (1976) da Skinner (1977) da Newman (2000)
da Jaggar (2001) da Zegelmeyer (2009) da kuma
Ɓ
atagarawa
(2019) sun bayyana cewa, Hausa takan yi amfani da
ɓ
ur
ɓ
urshin korewa wajen kore
jumla marasa aikatau. Har wa yau, jumloli marasa aikatau na Hausa suna amfani
da
ɓ
ur
ɓ
urshin korewa guda biyu
domin kore jumla, wa
ɗ
anda
suka ha
ɗ
a da ra
ɓ
au baa…ba da kuma korau baabu/baa.
Haka ma a Fufulde, masana da manazarta da dama irin su Taylor (1953) da Stennes
(1967) da McIntosh (1984) da Ahmed (2011) da Aminu (2017) sun bayyana cewa,
jumla korau maras aikatau a Fulatanci tana amfani ne da sigar
ɓ
ur
ɓ
urshin korewa guda biyu wa
ɗ
anda suka ha
ɗ
a da naa da kuma korau walaa/ngalaa.
4.0 Ƙ alailaicewa
Game da sarrafa korewa a jumloli marasa aikatau, ya dogara ne ga
irin jumlar da ake sarrafawa. Domin, kowace jumla korau maras aikatau tana da
irin
ɓ
ur
ɓ
ushin kalmar korewa da ake sarrafawa. Wato, wannan mu
ƙ
ala ta ta
ƙ
aita
ne
a kan misalai daga jumla ganau da ta
ƙ
addamau da
kuma
jumla rayau
.
4. 1 Korewa a Jumla Ganau
Jumla ganau jumla ce wadda take bayyana aikau ko kuma yin
ƙ
arin bayani a kansa.
Ƙ
ara wa jumlar ganau
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa yana kore gaskiyar al
’
amarin da jumlar ta bayyana. A Hausa ana amfani da korau ra
ɓ
au baa…ba tare da dirka nee ga
jinsin
namiji da kuma jam’i sai kuma cee
ga jinsin mace.
Mu
dubi wa
ɗ
annan jumloli:
Misali
na 1:
Lamba |
Jumla Ganau |
Jumla Korau |
i. |
i
ta cee.
|
baa
ita cèe ba. |
ii. |
gwado
nee. |
baa
gwado nee ba. |
iii. |
mataashi
nee shi. |
baa
matashi nee shi ba. |
iv. |
doguwa
cee. |
baa
doguwa cee ba. |
A wa
ɗ
annan misalai,
an ga amfanin
ɓ
ur
ɓ
ushin korau baa…ba, a
inda yake kore aikau da jumlar ta bayyana. A nan, amfanin korau baa…ba a wannan jumla,
shi ne
ta kore ko a’anta ko kuma soke aikau da jumlar ta bayyana. Hakan
na faruwa ne idan aka ha
ɗ
a
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa ra
ɓ
au baa…ba da dirka cee ko kuma ga namiji ko jam’i ana
amfani da nee.
Misali na 2:
Lamba |
Jumla Ganau |
Jumla Korau |
i. |
s
uu nee.
|
b
aa su nee
ba
.
|
ii. |
f
arare nee.
|
b
aa farare nee
ba
.
|
iii. |
ƙ
onannu nee.
|
b
aa
ƙ
onannu nee
ba |
iv. |
d
oogaye nee su
|
b
aa dogaye nee su
ba. |
A nan, kalmar dirka nee
tare da korau ra
ɓ
au ba
a
…ba
(wato korau mai
ƙ
a
f
a biyu, a farko da
ƙ
arshen jumla) duk a
ka
n sarrafa su
ne a
yayin kore jumla ganau ta Hausa. A wa
ɗ
anan misalai, za a ga cewa
,
kor
au
tare da dirka su suka
n
gina yankin aiki a jumlar kuma suka ba
i
wa jumlar ma’anarta ta jumla korau. Kodayake dirka a irin wannan
jumla, ba dole ne
ba
, tun
da a
ka
n iya sarrafa jumlar kuma ta ba da ma’ana ba tare da an yi amfani
da dirka ba
, kamar
yadda za a gani a misali na 3.
Misali na 3
:
Lamba |
Jumla Ganau |
Jumla Korau |
i. |
i
ta cee.
|
b
aa ita ba.
|
ii. |
s
hi nee
. |
b
aa shi ba.
|
iii. |
f
ara cee
. |
b
aa fara cee
ba. |
Wa
n
nan
ya
na nuni cewa
,
yin amfani da dirka a jumla ganau ta Hausa ba dole ne
ba
. Wato, jumlar
ta
na sarrafuwa
ne
ko da
ta
kasance
babu dirka a cikinta.
A Fulatanci kuwa, kodayake ba a tantance jinsi, amma ana amfani ne
da wakilin suna wanda yake nuna ajin kalmar da kuma adadi tare da
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa naa
domin kore jumla ganau.
Misali na 4:
Lamba |
Harshe |
Jumla Ganau |
Jumla Korau |
i. |
Ful
ɓ
e |
n
du sonndu.
|
ndu
naa sonndu. |
|
Hausa |
(wannan
+ tsuntsuu) |
(wannan
+ korau + tsuntsuu) |
|
Jumla |
wannan
tsunstuu nee. |
wannan
ba tsuntsuu nee ba. |
A wannan misali na 4 da yake
sama, an ga yadda harshen Fulatanci
,
kamar
dai
a Hausa, yake sarrafa
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa wajen kore jumla. Bambamci tsakanin tsarin harsunan kuwa
ya
bayyan
ta fuskar kalamomin da su ke ha
ɗ
uwa da
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa domin kore
tabbacin alamari.
Ɓ
ur
ɓ
ushin korewa a harshen Fulatanci na ha
ɗ
ewa da kowane azuzuwan
wakilin suna nunau guda ashirin da shida da ake da su a harshen domin
samar da
irin wannan jumla
.
Wannan ya bambanta da ta
Hausa a inda
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa ke ha
ɗ
ewa da dirka domin kore jumla. Saboda haka, za a iya cewa kalmar
dirka a harshen Hausa da kuma wakilin suna nunau a Fulatanci na taimakawa wajen
kore tabbacin alamari a jumla
na
nau. Haka ma idan wakilin suna a Fulatanci na nuna jam’i, ta yin
amfani da wakilin suna
ɗ
i a maimakon ndu na misali da ya gabata.
Misali na 5:
Lamba |
Harshe |
Jumla Ganau |
Jumla Korau |
i. |
Ful
ɓ
e |
ɗ
iya
colli
. |
ɗ
iya
naa colli. |
|
Hausa |
(wa
ɗ
ancan +
tsuntsayee + nee) |
(wa
ɗ
ancan + korau +
tsuntsayee) |
|
Jumla |
wa
ɗ
ancan tsuntsayee nee. |
wa
ɗ
ancan ba tsuntsayee ne
ba. |
A nan, an
ga cewa
wajen
furta jumla ganau a Fulatanci, ana amfani da jam’in wakilin suna
nunau tare da
ɓ
ur
ɓ
ushin korau. Ita wakilin suna nunau kan iya zama tilo ko jam’i,
wanda ya sha bamba
n
da
dirka
na Hausa wanda yake nuna bambamcin jinsi. Haka kuma idan aka dubi amfanin
wa
ɗ
anan kalmomi a irin wannan jumla za a ga cewa suna kore jumlar ne.
Ana koma iya yin amfani da
ɓ
ur
ɓ
ushin korau naa da kalmar abin da aka kora kawai a misalai
kamar haka:
Misali na 6:
Lamba |
Harshe |
Jumla Ganau |
Jumla Korau |
i. |
Ful
ɓ
e |
l
eeso on.
|
naa leeso. |
|
Hausa |
(gado
nee) |
(korau
gado) |
|
Jumla |
gado
nee. |
baa
gado nee ba. |
ii. |
Ful
ɓ
e |
ɗ
erewol
on. |
naa
ɗ
erewol. |
|
Hausa |
(tak
ά
rdaa
cee) |
(korau
tak
ά
rdaa) |
|
Jumla |
takardaa
cee. |
baa
takardaa cee ba. |
Wa
ɗ
anan jumloli d ake misali
na 6, sun nuna cewa ana iya kore jumla nunau a Fulatanci ba tare da yin amfani
da
k
almar dirka on ko kuma wakilin suna nunau ba. Wan
n
an ya bambamta da yadda jumla nunau yake a Hausa inda ya zama tilas
a yin amfani da dirka domin yin nuni
.
W
a
ɗ
a
n
nan harsuna biyu sun nuna bambanci ta fuskar kalmomi da suke ha
ɗ
uwa da
k
almar korewa domin su
samar da
korewa a jumla nunau
. A
yayin da Hausa take amfani da korewa ra
ɓ
au baa…ba tare da dirka nee/cee, Fulatanci na amfani da
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa naa da kuma wakilin nunau suna wa
ɗ
anda suke zuwa a bisa
azuzuwan suna guda ashirin da shida da ake da su a harshen tare da
ƙ
wayar
korewa naa.
4. 2 Korewa a Jumla Ƙ addamau
Irin wanan jumla na
ƙ
addamar da aikau a jumla
. K
ore irin wannan jumla a
harshen Hausa da Fulatanci na bu
ƙ
atar amfani da
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa. Har ila yau, Hausa na amfani da ra
ɓ
au baa…ba a yayin da Fulatanci ke amfani da naa. Kodayake masana da dama na
gan
in cewa ba a kore jumla
ƙ
addamau, domin sai abin da ke
akwai ake
ƙ
addamarwa. Duk da haka, ana iya amfani da korau a irin wannan jumla
domin ci
m
ma w
ani
buri
n
a
daban. A Hausa, ana amfani ne da
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa ra
ɓ
au da kuma alamar motsin rai.
Misali na 7:
Lamba |
Jumla
Ƙ
addamau
|
Jumla Korau |
i. |
gaa
dookin. |
baa
gaa dookin ba! |
ii. |
gaa
shi. |
baa
gaa shi ba! |
iii. |
gaa ni
|
baa
gaa ni ba! |
A wa
ɗ
annan misalai na Hausa,
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa baa…ba,
a nan, ba ta
kore
jumlar amma tare da alamar motsin rai da kuma
ɓ
ur
ɓ
ushin ga, sun ha
ɗ
u ne don
ƙ
arfafawa
da
ƙ
ara
ƙ
addamar
da aikau a cikin jumlar, ba don a kore ma’anar jumlar ba.
Ana kuma iya amfani da iyalin bayanau nan da can tare da
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa a irin wannan
jumla.
Misali na 8:
Lamba |
Jumla
Ƙ
addamau
|
Jumla Korau |
i. |
gaa
littafin can. |
baa
gaa littaafin can ba! |
ii. |
gaa su
nan. |
baa gaa
su nan ba! |
iii. |
gaa ni
nan |
baa
gaa ni nan ba! |
A nan, amfanin da
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa a wa
ɗ
annan jumloli ba yana
nufin sun kore jumlar ba, a’a, sun dai
ƙ
ara wa jumlar bayani ne.
Yin amfani da
ɓ
ur
ɓ
ushin korewar
ƙ
addamau
tare da
ɓ
ur
ɓ
ushin ga da kuma alamar mosin rai, na ha
ɗ
ewa ne domin su
ƙ
ara
kaddamar da aikau jumla.
Wannan na nuni da cewa ba a
kowace jumla
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa ra
ɓ
au ba
a
…ba
a harshen Hausa ke kore
tabbacin alamari ba.
Haka ma a Fulatanci, amfanin
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa naa a jumla
ƙ
addamau kamar a Hausa ne, ba ta kore jumlar, sai dai ta
ƙ
ara
ƙ
arfafa jumlar da aikau da ke cikin jumlar.
Misali na 9:
Lamba |
Harshe |
Jumla Korau |
Jumla
Ƙ
addamau
/
Ƙ
arfafau
|
i. |
Ful
ɓ
e |
n
daa defte ma.
|
n
aa ndaa d
efte
ma!
|
|
Hausa |
(korau + ga
+
littatafan + ka/ki)
|
ba
a ga
a
litatta
a
f
a
nka/ki ba!
|
A nan, in an lura za a ga cewa an yi amfani da
ɓ
ur
ɓ
ushin ndaa tare da
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa amma hakan bai sa jumlar ta
z
ama korau ba. Asali ma kalmomin na
ƙ
arfafa jumlar ne. Har wa yau, Fulatanci shi
ma
ya
na amfani da iyalin bayanau d
o
n
ƙ
ara
ƙ
arfafawa da kuma
ƙ
addamar da aikau da
ke cikin jumlar.
Misali na 10:
Lamba |
Harshe |
Jumla Korau |
Jumla
Ƙ
addamau
/Nunau
|
i. |
Ful
ɓ
e |
ndaa defte ma haa
ɗ
o!
|
n
aa ndaa defte ma haa
ɗ
o!
|
|
Hausa |
korau
+
ga
+
litattafan
+
ka/ki
a
+
(manuni
nan)
|
b
a
a
ga
a
litattafanka/ki a nan ba!
|
A
nan
,
za a ga cewa
ɓ
ur
ɓ
ushin kalmomin nan guda biyu, ndaa
da kuma korewa naa suna taimakawa
wajen jaddada sa
ƙ
on da jumlar ke
ƙ
o
ƙ
arin isarwa. Wannan na nufin sarrafa irin wannan jumla a Hausa da Fulatanci
a
na amfani da
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa iri
ɗ
aya a yayin da harsunan suke sarrafa
k
almar n
u
nau da kuma
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa domin gabatar da irin wannan jumla. Har wa yau,
aukuwar wa
ɗ
an
n
an kalmomi a irin wannan tsari ba ya nufin jumlolin a harsuna biyun
sun zama jumloli korau ne
ba
, a
’
a, kawai suna tabbatar
wa
da kuma nuna gaskiyar al
’
amari.
Saboda haka, ana iya cewa akwai kamanci na ku
t-
da
-
ku
t
t
a yadda harshen Hausa da na Fulatanci
suka yi kamanceciniya
ta fuskar sarrafa
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa da kuma sauran
ɓ
ur
ɓ
ushin kalmomi da suke ha
ɗ
uwa da korau wadda suka ha
ɗ
a da
ɓ
ur
ɓ
ushin ga a Hausa da kuma ndaa a Fulatanci, sai kuma alamar motsin
rai wa
d
da harsunan
su
k
an yi
amfani da
ita
wajen isar da sa
ƙ
o da kuma nuni da cewa wa
ɗ
anan jumloli
ƙ
addamau ne.
4. 3 Korewa a Jumla Rayau
Jumla rayau, jumla ce mai ishara ga rayuuka ko kuma mallakarsa ga
wani abu a cikin jumla.
Ɗ
afa wa jumlar
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa na nuni da cewa aikau da
ya
ke cikin jumlar ba
sh
i da ala
ƙ
a da kar
ɓ
au ko kuma shi aikau
ɗ
in bai mallaki abin ba.
Saboda haka, tsarin kore irin wannan jumla a harshen Hausa da na Fulatanci sun
yi tarayya a kan turba guda. Abin da ake nufi a nan
,
shi ne, harsunan Hausa da Fulatanci suna sarrafa
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa na musamman
(wanda ake kira da negati
v
e e
x
istential markers
) domin kore irin wannan
jumla.
A Hausa, ana amfani da kalmar korewa baabu
da
baa
ta domin kore irin wannan jumla. Wa
ɗ
a
n
nan kalmomi guda biyu, wani lokaci suna na fitowa a mastayin
ɗ
aya, a wani lokaci kuma guda
ɗ
aya kawai ake bu
ƙ
ata.
Misali na 11:
Lamba |
Jumla Rayau |
Jumla Korau
|
i. |
da shi
a cikinsu. |
baabu
shi a cikinsu. |
A wa
ɗ
annan misalai da suka
gabata, sun nuna cewa za a iya amfani da kowace kalmar korau kuma ta ba da cikakkiyar
ma’ana a jum
la. Ana iya cewa ba
ya
cikinsu
ko kuma baabu shi cikinsu, na da cik
a
kkiyar ma’ana. Korewa a jumloli duka biyu anan na kore gaskiyar
alamari. Har ila yau, idan aikau din jumla ya
na
iya
z
uwa
a farkon jumla,
ɓ
ur
ɓ
ushin
k
almar korau baa
ya
bin sa.
Misali na 12:
Lamba |
Jumla Rayau |
Jumla Korau
|
i. |
baabarmu
tana gida. |
baabarmu
ba ta gida. |
A wannan misali, an yi amfani da baa a maimakon baabu
domin aikau ya zo a gabanin shi kalmar korau
ɗ
in. Duk da hakan korau a wannan jumla
ya
na kore gaskiyar jumlar
ne
. Haka kuma
,
idan jumlar
ta
na kore abin da aikau ya mallaka, korau
ɗ
in
da za a yi amfani da shi ya
kan
daganci irin wakilin sunan
kalmomin da aka yi amfani
da su
.
Misali na 13:
Lamba |
Jumla Rayau |
Jumla Korau |
i. |
yana
da komai. |
ba shi
da komai. |
ii. |
suna
da gida |
ba su
da gida. |
iii. |
yana
cikin wa
ɗ
anda suka
ci jarrabawa |
ba yaa
cikin wa
ɗ
anda
suka ci jarrabawa. |
A wa
ɗ
annan misalai, za a g
a korewa
r
ta
zo da jer
i
n kalmomi daban daban. A na farko, za a ga jumlar ta zo da maha
ɗ
i da wanda ke karbar korau ba
kawai da kuma wakilin suna mutum na uku. Jumla ta
uk
u kuwa na iya
ɗ
aukar kowane cikin korewa
r
tun
da ba
y
a
zuwa da mah
a
ɗ
i da. Don
haka, ana iya
cewa korau da za a yi amfani a jumla ya danganci irin kalmomin da suka zo cikin
jumla.
A Fulatanci kuwa, jumla rayau
ta
na amfani da kalmar korewa walaa
g
a tilo ko ngalaa
g
a jam’i domin
nuna
kore
wa a
cikin
jumla.
Misali na 14:
Lamba |
Harshe |
Jumla
Raya
u |
Jumla Korau |
i. |
Ful
ɓ
e |
ɓ
inngel
(ngel) mari pa
ɗ
e. |
ɓ
inngel
(ngel) walaa pa
ɗ
e. |
|
Hausa |
(yaro/yarinya
+ (wannan) + korau + takalmi.) |
yaron/yarinyar
(nan) ba shi/ta da takalmi. |
|
|
|
|
ii. |
Ful
ɓ
e |
mi
mari saare mau
ɗ
ee |
mi
walaa saare mau
ɗ
ee. |
|
Hausa
|
(ina +
da + gida + babba
)
|
(
ni + korau + gida + babba)
|
|
|
|
baa ni
da babban gida. |
A wa
ɗ
annan misalai za a ga cewa
korau di
n jumloli ne ka
ɗ
ai a mastayin yankin aiki kuma
suna kore abin
da
ak
a mallaka. Haka ma yin amfani da korau mai nuna jam’i na abu ko
mutum fiye da
ɗ
aya, ana amfani da ngalaa
kuma shi ma korewa ce ko kuma nuna rashin abin da aikau ya mallaka yake yi.
Misali na 15:
Lamba |
Jumla
Rayau
|
Jumla Korau |
i. |
ɓ
e mari
ndiyam yarugo. |
ɓ
e
ngalaa ndiyam yarugo |
ii. |
(suna
+ da + ruwan + sha |
su +
korau + ruwan + sha) |
iii. |
|
baa su
da ruwan sha. |
A nan korau na nuna jam’i
da kuma kore abin da
aikau
ya
mallaka. Wannan na nufin cewa, lallai, korau da
ke zuwa a jumla rayau na kore
jumla ko ma a
ce kore abin
da aikatau
n
a jumlar ya mallaka. Don haka a iya cewa, kalmar korau baabu/baa da kuma walaa/ngalaa suna zuwa ne a jumla rayau domin kore abin
da jumlar ta gaskanta.
Jumla rayau a Hausa da Fulatanci na da kamanci masu yawa saboda
irin jumlar a harsuna biyun na amfani da korau na musaman wanda kowane harshen
na da guda biyu. Haka kuma
,
suna yin aiki iri
ɗ
aya wagen kore gaskiyar jumlolin. Bambamcin korewa a wainan harsuna
biyu shi
ne amfaninsu ta wajen mu
’
amala da jumla a inda baabu da baa a Hausa ke mu
’
amala da juna ta fuskar zamowa
mawakilta juna
, walaa da ngalaa a Fulatanci kuwa na mu
’
amala ta fuskar adadi.
5. 0 Ta ƙ aitawa da kuma Kammalawa
Idan aka yi la’akari da bayanan da suka gabata za a iya fahimtar
cewa akwai kamanci masu dama a jumloli korau marasa aikatau na Hausa da Fulatanci.
Kamancin ya shafi adadin
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa da ake sarrafawa a irin wa
ɗ
anan jumloli. A yayin da
harshen Hausa ke sarrafa da guda biyu wato, korau ra
ɓ
au baa…ba kamar a misalai na 1 zuwa na 3 da kuma korau rayau baabu/baa,
a misalai na 11 zuwa na 13, haka ma Fulatanci, korau guda biyu
yake sarrafawa, wa
ɗ
anda suka ha
ɗ
a da
ɓ
ur
ɓ
ushin naa kamar a misalai
na 4 da na 6,
da kuma korau rayau walaa/ngalaa a misalai na 14 da kuma 15.
Har wa yau, idan aka dubi aikin da ko wacce siga ke yi a harsuna biyun, za a ga
cewa suna kore jumla iri
ɗ
aya ne. Korau ra
ɓ
au baa…ba kamar a misalai
na 7 da na 8 a Hausa da
ɓ
urbushin naa na Fulatanci
da yake kore jumloli ganau da
ƙ
addamau
a misalai na 9 da na 10. Haka lamarin yake tsakanin korau baabu/baa na Hausa da walaa/ngalaa na Fulatanci da suka kore
jumla rayau a harsuna biyun kamar yadda aka kawo a misalai na 11 zuwa na 15.
Har ila yau, ta yin amfani da
ra’in Halliday, an gano cewa akwai bambamci da kamanci a yadda ake sarrafa
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa a jumloli
marasa aikatau na Hausa da Fulatanci. Ta fuskar kamanci, an gano cewa, a jumla
ƙ
addamau
, Hausa da Fulatanci sun
yi tarayya ta fuskar yin amfani da
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa tare da
ɓ
ur
ɓ
ushin ga, sai kuma alamar motsin rai.
Wato a nan, harshen Hausa da Fulatanci suna yin amfani da
ƙ
wayoyin kalma iri guda domin furta irin wannan jumla. Wa
ɗ
anan
ɓ
ur
ɓ
ushin a Hausa da Fulatanci,
ba sa kore jumla
ƙ
addamau, maimakon haka, suna tabbatar da sa
ƙ
on da jumlar ke isarwa ne. Haka ma a jumla ganau, Hausa da Fulatanci sun yi tarayya wajen sarrafa
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa. A yayin da
ɓ
ur
ɓ
ushin korewar ke fitowa a
farkon jumla, ko kuma a tsakiya idan wakilin suna ne a farko. Wannan na nufin
ɓ
ur
ɓ
ushin korewa a harsuna biyun
na aiwatar da aiki iri
ɗ
aya; ko su kore jumla ko kuma su jaddada ta, ko kuma tabbatar da
aikau
ɗ
in jumlar.
Duk da yawan kamanci, ba za a rasa bambamci ba,
a inda korau rayau baabu da baa kan iya bambanta, shi kuwa walaa da ngalaa a Fulatanci ana amfani da su ne domin nuna bambamcin adadi. Haka
ma ana samun bambamci wajen
ƙ
wayoyin kalma da ake sarrafawa, kamar yadda aka nuna a jumla ganau,
inda Hausa ke amfani da dirka, a Fulatanci kuwa, ana amfani ne da azzuzuwan
wakilin suna ashirin da shida da ake da su a harshen. Daga
ƙ
arshe, duba ga tarin kamanci a tsarin korewar jumlioli marasa
aikatau na Hausa da na Fulatanci, ana hasashen cewa, idan aka tattara irin wa
ɗ
anan bayanai, za su iya ba da
haske wajen sake bibiya, ko a ce za a iya samu dangantaka ta jini a tsakanin wa
ɗ
anan harsuna guda biyu da ake
ikirarin ba su da ala
ƙ
a ta jini.
Manazarta
Ahmed, A. I. (2011)
.
Introduction to Fulfulde Syntax.
Muenchen: Lincom Europa Academic Publications
.
Aminu, A. (2017).
Morphosyntactic Analysis of Fulfulde Voice and Tense in Adamawa Dialect: A Case
Study of Yola South. In Journal of
Linguistics Association of Nigeria Vol. 20 No. 2 p.21-27
.
Arnott, D. W. (1970). Nominal and Verbal Systems of Fula Oxford:
Clarendon Press.
Bagari,
M. D. (1986)
.
Bayanin
Hausa. Rabat: Imprimerie El
Maarif Al Jadada Press.
Bargery,
G. P. (1934)
.
Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary
London: Oxford University Press.
Bloor,
T. and Bloor, M. (2013)
.
The Functional Analysis of English: A Hallidayan Approach
USA: Routledge.
Ɓ
atagarawa, A. G. (2013)
.
Movement Operations in Hausa Non-verbal Sentences
Unpublished Ph.D. Thesis Zaria: Department of African Languages
and Cultures, Ahmadu Bello University.
Dahl, O. (1979)
.
Typology of Sentence Negation
Linguistics p.17,79-106.
Forest, R. (1993)
.
Negation
: Essai de Syntax et de
Typologie Linguistique Collection Linguistique LXXVII Paris: Klincksieck.
Galadanci, M. K. M. (1976) An Introduction to Hausa Grammar Kano:
Longman Nigeria Abdullahi Bayero College,
Greenberg, J. H. (1948)
.
The classification of African Languages
America: New series Vol. 50 No. 1 Part1 American Anthropologist
Association
Haegeman, L. (1995) The Syntax of Negation Cambridge:
Cambridge University Press.
Halliday, M. (1985)
.
Introduction
to Functional Grammar
.
London
:
Arnold
.
Halliday, M. (1994)
.
Introduction
to Functional Grammar
(
2n
d ed
).
London
:
Arnold
.
Halliday, M. &
Matthiessen, C. (
2004
)
.
Introduction
to Functional Grammar
(3rd ed).
London
:
Arnold
.
Hegedus, V. (2013)
.
Non-Verbal Predicates and Predicate Movement in Hungarian
Netherlands: LOT Trans 10
.
Horn, L. (1989)
.
A Natural History of Negation
Chicago and London: University of Chicago Press.
Jackson, E. (2007)
.
Weak and Strong Negative Polarity Items: Licensing and Inter
ɓ
ention Linguistic Analysis
p.25-181
Jaggar,
P. J. (2001)
.
Hausa.
London: London Oriental and
African Language Library
Johnston,
H. A.S
(
1967)
. The Fulani Empire of Soko
Nairobi: West African Graphic Company Ltd.
Kyambo,
B. S. (2019)
.
Kwantancin Yankin Aiki a Hausa da Fulfulde.
Unpublished Ph.D. Thesis
McIntosh,
M. (1984)
.
Fulfulde Syntax and Verbal Morphology
Great Britain: Routledge & Kegan Paul PLC.
Moscati, V. (2010)
.
Negation Rising: Logical Form and Linguistic Variation
Cambridge: Cambridge Scholars Publishing.
Mohsen, K. H. (2011)
.
Negation in
English. Unpublished MA
Dissertation Department of Foreign Languages and Translation University of
Agder.
Newman, P. (2000). The Hausa Language: An Encyclopedic
Reference Grammar London: Yale University Press.
O’Donnell, M. (2012)
.
Introduction Systemic Functional Linguistic for Discourse
Analysis-Language Function & Cognition
http://docplayernet
Payne, J. (1985)
.
Negation: Language, Typology and Syntactic Description of Clause
Structure
Cambridge: Cambridge University
Press
Ƙ
uirk, R. & Greenbaum, S. (1985)
.
A Comprehensive Grammar of
the English Language. London: Longman
Sani, M.
A. Z. (1999)
.
Tsarin Sauti da Nahawun Hausa
Ibadan: University Press PLC.
Skinner,
N. (1977)
.
A Grammar of Hausa
Zaria: Northern Nigeria
Publishing Company Ltd.
Speranza, J. L. & Horn,
L. R. (2010)
.
A Brief History of Negation Journal
of Applied Logic
V
ol.8
www.else
ɓ
ier.com/locate/jal
Stennes,
L. H. (1967)
.
A Reference Grammar of Adamawa Fulani
Michigan: Michigan University.
Taylor,
F. W. (1932)
.
Fulfulde – English Dictionary
Oxford: Oxford University Press.
Taylor,
F.W. (1953)
.
A Grammar of the Adamawa Dialect of the Fulfulde Language
Oxford: Oxford University Press.
Yusuf,
M. A. (2011)
.
Hausa Grammar: An Introduction
Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
Zaria,
A. B. (1981)
.
Nahawun Hausa
Lagos: Thomas Nelson Nigeria
Limited.
Zarru
ƙ
, R. M. (2005)
.
Bishiyar Li’irabi: Nazarin Jumlar Hausa
Zaria: Institute of Education Ahmadu Bello University.
Ziegelmeyer,
G. (2009)
.
Negation of non-indicative mood in Hausa, Fulfulde and Kanuri Negation Patterns in West African Languages
and Beyond. Amsterdam: John Benjamins Publishing Company P. 7-20.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.