1. Ƙahon Dandi; Jin ɗumi kusa da wuta, musamman lokacin sanyi, ko ma duk lokacin da ake jin sanyin.
2. Zunguru; Wani abu ne, dangin ƙwarya, mai ɗan tsayi da ake yi masa ƙofa daga sama a rarake cikinsa, mata kan cusa hannunsu a ciki zuwa guiwar hannu, bayan an zuba kwaɓaɓɓen lalle domin yin ƙunshi.
3. Azargagi; Dogon
zare ko tsumman da aka kekketa aka kuma ƙulla suka yi tsawo. Mata na amfani da shi
wajen tufke ledar da suka naɗe
ƙafafu
da ita yayin ƙunsa lalle (kamar yadda yake a wannan labari, amma ya na da
wata ma'anar ta daban).
4. Mazari; Ɗan tsinke ne na Itace kamar tsintsiya,
amma ya fi tsintsiya ƙwari, an haɗa
shi da dunƙulen
laka, ya na da tsini daga ƙasa. Ana amfani da shi wajen kaɗi
ko murza auduga ta koma zare.
5. Taskira; Ɗan
kwando ne ƙarami
mai ɗan faɗi da ake saƙawa da
Kaba, sa'annan sai a shimfiɗa
masa ƴan
jemammun fatu a cikinsa. A saman fatar da aka shimfiɗa ake murza mazari wajen kaɗi. Mata kuma kan yi amfani
da shi wajen ajiya, sai a ɗaga
fatun a ɓoye abin da
ake son ɓoyewa
tsakanin fatun nan, wasu na kiransa "Tayani." Akwai kuma wani ɗan kwando na Kaba mai marfi
da ake sargafewa a jikin bango ana ajiya a ciki, wasu na kiransa
"Taskira."
6. Abawa; Zaren da
aka samar daga taffa (audugar da aka cire wa ƴaƴa) ta hanyar kaɗi da mazari.
7. Akwasa; Wani Ice
ne da aka sassaƙa, ya na da tsayi da ɗan
faɗi kamar dai Takobi.
Mata na amfani da shi wajen saƙa.
8. Gafaka; Jakar da
aka yi daga fata domin adana littattafai.
9. Agalemi; Fatar
Akuya ko rago da ba a jeme ba har suka bushe (buzu).
10. Akushi; Mazubin abinci da aka sassaƙa da
Itace (kwanon cin abinci na Itace).
11. Ƙoshiya; Cokali na Itace.
12. Gidauniya; Ƙwaryar da ake zuba wa maigida fura a rufe
da faifai.
13. Tarde; Wani ɗan
abu ne da ake saƙawa da kaba a zagaye kamar gammo. Ana ajiye Gidauniya a sama
don kada ta ɓingire.
Matan Fulani ma na amfani da shi wajen tallar nono, idan za su ajiye ƙwaryar
nono sai su ajiye shi ƙasa, su girke ƙwaryar kansa.
14. Jemo; Shi ne matsayin kofin shan ruwa a yanzu. Da ƴar ƙaramar
ƙwarya
ake yinsa, girmansa kamar ɗan
ƙaramin
kwanon sha. Matan Fulani ma na amfani da shi wajen auna nono.
15. Jallo; Ɗan goran duma da ake zuba ruwa idan za a
yi tafiya.
16. Shantu; Wani abu ne dangin ƙwarya, tsawonsa kamar
tsawon hannu, daga yatsu zuwa kafaɗa,
sai dai bai kai kaurin hannu ba. Ana yanke kowane ƙarshe nasa, a rarake
cikinsa, kamar dai ɗan
guntun fayil na ruwa. Mata na amfani da shi wajen rera waƙoƙi. Su
na buga shi a kan cinya su kuma riƙa kaɗa
shi da ƴan
yatsun hannu, musamman idan an sa zobba ga yatsun, sai ya dinga ba da sautuka
masu daɗi kamar ana kaɗa ƙwarya.
17. Jaura; Lokacin da ya fi kowane lokaci sanyi yayin sanyin
hunturu.
18. Kindai; Ɗan ƙaramin kwando na Kaba mai marfi, wadda
mata ke ajiya a ciki.
19. Farsa; Ɗaya daga cikin sunayen goro kamar daushe,
gandi dss.
20. Albada; Sautu ko saƙo.
21. Ƴar shara; Rigar da Bahaushe ya fara ƙirƙira. Riga ce mara
hannaye.
22. Kurtu; Kamar ƴar kwalba ko ɗan gwangwani ke nan a halin yanzu, amma wannan
na Duma ne. Yawanci ana zuba tawadar rubutu a ciki. Haka tsoffi kan ajiye shi a
cikin ɗaki domin zuba
yawu. Har a wasu masallatai ma a kan ajiye shi domin zub da yawu.
23. Ala; Baki ya yi ja idan an tauna goro ba a haɗiye ba.
24. Ruɗa-kuyangi;
Rana ta yi ja za ta faɗi.
25. Kwiɓin
bazawara; Ƴar
siririyar hanyar ƙauye, musamman wadda ake tafiya da ƙafa, takan ɗan yi zurfi kuma ciyawa kan
fito gefe da gefe. To gefen hanyar ita ce kwiɓin
bazawara, wadda idan mai keke ko mai babur ya kuskure tsakiyar hanyar ya taka
gefe, santsin ciyawar zai iya kayar da abin hawansa.
26. Mayani; Ƙyalle ko tsumma da tsoffi ke ƙulle
wani abu a ciki.
27. Tsariya; Ƙarƙashin gado, musamman irin gadon dauri da
akan yi na ƙasa
sai a yi ƴar
ƙofa
daga ƙasa
wadda ake sa wuta lokacin sanyi, sai gadon ya yi ɗumi
a ji daɗin kwanciya.
Yanzu da babu irin wancan gadon, ƙarƙashin kowane irin gado ana iya kiransa
tsariyar gado.
28. Asabari; Kamar labulen ƙofa ne da ake yi da siraran kara ko gamba
ko wani abu daban. Ana saka shi daga wajen ƙofa, yawanci domin kare feshin ruwa ko
rana.
29. Hirji: Addu'a ko neman kariya daga wani abin da ake
tsoro.
30. Amaryar wata; Sabon wata, kwanakin farko na wata.
Ƙarin bayani: In da aka ga kuskure, gyara ko ƙarin
bayani, ƙofarmu
a buɗe take. Mun gode.
Taskar Nasaba
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.