𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘��❓
Assalamu alaikum malam na kwanta bacci da daddare sai na yi
mafarkin ubangiji yana tambayata wa'yan ne ɗiya
nika son ya ba ni? Sai na ce masu yawa masu albarka, amman fa bangan shi da
idona ba, kawai dai na yi mafarki ne, shin da gaske ne ko aikin sheɗan ne?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salám, daga cikin malamai akwai waɗanda suka ce mutum zai
iya yin mafarki ya ga Ubangiji Subhaanahu Wata'ala a cikin barci, amma fa abin
da ya gani ɗin nan
ba shi ne haqiqanin zatin Allah ba, saboda shi Allah babu wani abu da ya yi
kama da shi kwata-kwata. Har ma Imam Albagwiy ya hakaito daga wani malaminsa
cewa: Ganin Allah a cikin barci (mafarki) halas ne, idan mutum ya yi mafarkin
Allah har ya yi masa alqawarin Aljannah, ko alqawarin gafara, ko alqawarin
samun tsira, to wannan maganar tasa gaskiya ce, alqawarin Allah gaskiya ce,
idan kuma ya yi mafarkin Allah yana kallon sa, to rahamar Allah ne ya gani,
idan kuma ya yi mafarkin Allah ya kawar da kai daga gare shi, to gargaɗi ne game da zunubansa,
idan kuma mutum ya yi mafarkin Ubangiji ya ba shi wani abun duniya, har kuma ya
karɓi wannan abu, to
wannan zai gamu da jarabawa da rashin lafiyar da za ta taɓa jikinsa, kuma hakan zai
girmama ladan bawa, har ya kai ga samun rahamar Allah...
Duba Sharhus Sunnah (12/227, 228) na Imam Albagwiy.
Haka shi ma Imamun Nawawiy ya hakaito daga Alqadhiy Iyadh ya
ce: "Malamai sun yi ittifaqi a kan halascin yin mafarkin Allah a cikin
barci, ko da kuwa mutum ya gan Shi ne a cikin wata siffa da ba ta dace da
halinSa ba na daga cikin abubuwa masu jiki, to lallai wannan abin da aka gani a
mafarki ba shi ne zatin Allah Maɗaukakin
Sarki ba..."
Duba Alminhaaj (10/25), na Imam Annawawiy.
Wannan ya nuna cewa zai iya yiwuwa mutum ya yi mafarkin
Ubangiji, amma ba zai ga Ubangijin a zatinsa ba, ko da ma ya ga wani abu ne, to
wannan abin ba shi ne Allah ba, saboda ba wani abu da yake kama da Allah, kuma
ba ya yiwuwa mutum ya ga Allah a haqiqanin zatinSa a wannan duniya kamar yadda
nassoshi da dama suka tabbatar, amma za a iya yin mafarkinSa kamar yadda bayani
ya gabata daga waɗancan
malamai.
Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.
Jamilu Ibrahim, Zaria.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.