𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Nakasance mai yawan mafarkin tashin alqiyama kuma acikin
mafarkin saida naga na tsira, dan Allah kokasan fassarar abunda mafarkin ke
nufi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Gaskiya bansan fassarar wannan mafarkin ba, nidai ban iya
fassarar mafarki ba kowanne iri domin bankoyi yanda akeba.
Tabbas akwai fassarar mafarki acikin shari'ar musulunci
saidai ba haka kawai mutum zai goge fuska yace yanada kansa amatsayin mai
fassarar mafarki ba, Saidai yanda zamani yagurbace kuma galibi mun ɗauki mafarki kamar wata
al'amara shi ne yasa kwata-kwata babu mutanen kirki afannin fassarar mafarki,
yawanci saidai madamfara masu cin dukiyar mutane batareda hakkiba da masu ci da
addinine suke riqe da fannin ayanzu awannan zamanin.
Amma tabbas akwai fassarar mafarki a musulunci kus-kurene
kai mafarki kabarshi haka kawai baka samu malamin Allah wanda ya iya fassarar
mafarki yafassara maka wannan mafarkinba.
Shaik usmanu Bin fodio rahimahullahu acikin littafinsa
ihya'ussunnah ya ce: yana daka cikin bidi'ar da mutane suka auka cikinta shi ne
insunyi mafarki basa zuwa afassara musu mafarkinsu.
Shawara kawai da zamu iya baki Shi ne: Kilazimci yin Addu'ar
da Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yakarantar damu dangane da mafarki
Maikyau ko mara kyau, domin Inkikace za ki a fassara miki tabbas za ki wahalar
dakankine kawai, addu'ar itace
Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: idan mutum
yaimafarki yaga abunda ya burgeshi mafarkin yagodewa Allah, sai ya ce: (Ya
Allah ina rokonka Alkhairin wannan mafarki da Alkhairin dake cikinsa) Idan kuma
mummunan mafarkine saiya ce: *(Ya Allah ina neman tsarinka daka sharrin wannan
mafarkin dasharrin abundake cikinsa) Bayan yai tofi abarin hagunsa na hagu.
kuma karya bawa kowa labari.
Sannan lallai kada kibiyewa rudin Shaiɗan dangane dagani dakikai
amafarkin cewa kin tsira ki godewa Allah akan hakan, kuma kada yasaki ki saurara
wajan biyar Allah dakiyaye dokokinsa saidai kiqara kaimi da himmah darike
dokokin Allah, Allah yaimiki tsari daka sharrin Shaiɗan dakuma sawa kicika da imani.
Inkika ɗauka
keɓance cikin
mutane, babu shakka Shaiɗan
ne zaici nasara akanki yalalata miki imaninki.
kiyi koyi da Annabawa da salihan bayi da magabata nakwarai,
duk da sun san cewa Allah yaimusu alkawarin su 'yan aljannane hakan baisa sunyi
rauniba sunshantake ba, A'a kara kaimi da himma suke akan biyar Allah, Allah maɗaukakin sarki yace
كَانُوا
يُسَارِعُونَ فِي الْخَيْرَاتِ وَيَدْعُونَنَا رَغَبًا وَرَهَبًا ۖ وَكَانُوا لَنَا
خَاشِعِينَ
Sun kasance suna rige-rige wajan ayyukan Alkhairi, kuma suna
rokonmu dare darana suna masu saka rai daka rahamar Allah dakuma tsoran
Azabarsa, Sun kasance masu tsoran mune. (Suratul Anbiya: 90)
Tare dacewa Su Annabawane, Sahabbbaine Allah yaimusu
Alkawarin Aljannah tun suna aduniya, Amma hakan baisa Sun nade kafaba.
Ina kuma gamu nakusa dakarshen duniya, kuma tare da hakan
bamu dayakini ko tabbas akan abunda muka gani cikin mafarkin.
Ga wasu kadan daka cikin litattafai na fassarar mafarki kina
iya samun malamin Sunnah mai tsoran Allah tsayayye yabincika yafassara miki
mafarkin ki.
Littafin fassarar mafarki na muhammad Ibnu sireen. Saidai
shi malamin zai fada miki cewa ba'a dogara da abunda yake ciki na fassarar
mafarkin dake cikin wannan littafin da sauran litattafan fassarar mafarkin sai
abunda dalili nashari'a ya nunar ko wani abu dayake nuna hakan amma kada mutum
yadogara da fadin wani akan fassarar mafarki.
Atakaice dai idan mutum yai mafarki mai kyau yana aikata
alkhairi koya kubuta daka wani bala'i ko macen dabata hai-huwa tai mafarkin
Samun haihuwa kota haihu duk wani mafarki dai na alkhairi mutum zai godewa
Allah akansa yakuma fadawa wanda yaso cikin mutane.
Amma idan na sharri ne kamar yanda muka fada mutum zai nemi
tsarin Allah daka Shaiɗan
dakuma tsarin munin mafarkin yatofa ahagunsa sau uku, Sannan kada yabaiwa kowa
labarinsa.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.