Ticker

    Loading......

Mene Ne Ma'anar Pornography?

TAMBAYA (75)

Me kalmar pornography take nufi?

AMSA

Alhamdulillah

Allah SWT yace;

(إِنَّ السَّمْعَ وَالْبَصَرَ وَالْفُؤَادَ كُلُّ أُولَٰئِكَ كَانَ عَنْهُ مَسْئُولًا )

الإسراء (36) Al-Israa

Lalle ne jĩ da gani da zũciya, dukan waɗancan (mutum) ya kasance daga gare shi wanda ake tambaya.

An karbo daga Jabir RA ya ce: Na tambayi Annabi SAW akan kallon da banyi niyya ba. Sai Annabi SAW ya ce: "Ka daidaita ganinka"

(Sunan Abi Dawud 2148)

Ma'ana ka kawar da ganinka akan kallon haramun

An tambayi Ibn Taimiyya (Rahimahullah) dangane da kallon haramun, sai yace;

Kawar da gani ya hada da kauda kai da barin kallon al'aurar mutane da sauran abubuwan da aka haramta. Haka kuma nesanta kai daga kallon cikin gidajen mutane. Gidan mutum shi ne shamakinsa kamar yanda tufafi suke rufe al'aurarsa. Allah SWT ya bada umarnin nesantar kallon haramun da kuma rufe al'aura bayan ayar da ta yi hani akan shiga gidan mutum ba tare da izini ba saboda gida yana rufe mutum ne kamar yanda tufafi yake rufe jikinsa

(Majmoo' al-Fatawa (15/379)

Ibn al-Qayyim (Rahimahullah) a cikin Madaarij al-Saalikeen (1/117) yace;

"Abubuwan da aka haramta kallo sun hada da; kallon al'aura wanda ya kasu gida biyu; kallon al'aurar dake cikin tufafi da kuma cikin gidan mutane"

Ibn al-Manzoor (Rahimahullah) yace;

"Ghadd al-basr na nufin kauda kai ga barin kallon haramun"

(Lisaan al-'Arab 7/196)

A yaren Greek ma'anar porney yana nufin prostitution wato karuwanci, graphis kuma writing wato rubutu. Idan an hada kalmomin guda biyu, pornography zai zama rubutu ko kuma zanen mutane wadanda suke siyar da jikinsu don yin karuwanci

Yaren Greek ya samo asali ne daga kasar Greece, wadda take a southeastern Europe (Kudu maso gabashin Europe) wadda ta yi iyaka da Albania (kasar su Shaikh Muhammad Nasiriddin Albany), tsohon sunanta shi ne; Yugoslav Republic of Macedonia, haka kuma ta yi iyaka da kasar Bulgaria, da Turkey. Greece ta kasance Member state of the European Union tun shekarar 1981. Official name dinta shi ne: Hellenic Republic (Grek Ελληνική Δημοκρατία)

Kallon pornography yanada matuqar wuyar dainawa kamar yanda bayanai suka gabata a amsar da na bayar shekaranjiya to amman na bamu mafita tun a jiyan ga wadanda suka karanta zasu fa'idantu, in sha Allah

Kwanannan archaeologists (masana ilimin kimiyya na kayan tarihi) suka gano wasu gunkinan mutane a Pompeii City dake kasar Rome, al'umma guda, yara da manya, maza da mata wadanda bincike ya tabbatar da cewar sun mutu ne sakamakon volcanic eruptions (wato dutse mai aman wuta) ne ya zama silar halakar su, dalilin haka suka zamo dunqulalliyar toka

Ba wai komawarsu toka bane abin tsoro, a'a, halin da suka mutu akai shi ne abin tsoro. Sun mutu ne suna aikata Zina da Luwadi a bainar jama'a, kamar dai yanda wani yanki na garin Los Angeles dake kasar Amurka yake a bangaren shagala to haka garin Pompeii yake a kasar Rome. Azabar Allah SWT ta zo musu tun kafin su tuba, sunyi mutuwar wulaqanci, sun zama tarihi kuma darasi ga al'ummar da za ta zo a baya, kamar dai mutanen zamanin Annabi Lut AS

A binciken da nayi kwanannan naga wasu Archeologist (masana tarihin ragowar kasa da abinda ta kunsa tun zamanin da) sun gano wani gunki mai suffar mace a garin da aka halakar da mutanen Annabi Lud AS (Ana kiran wajen da "Dead Sea" wanda yake a kasar Jordan) da sukayi bincike sai sukaga gunkin macen ya dace da abinda ya faru a yankin shekaru dubunnai da suka gabata (Wallahu a'alam)

Allah SWT ya sanardamu irin zunubin da mutanen Annabi Lud AS suke aikatawa na neman jinsi a cikin Suratul A'araf ayata 80

"Da Lũɗu, a lokacin daya ce wa mutanensa: "Shin, kuna j wa alfasha, babu kowa da ya gabace ku da ita daga halittu?"

81) "Lalle ne ku, haƙĩƙa kuna j wa maza da sha'awa, baicin mata; A'a, kũ mutane ne maɓarnata."

82) "Kuma babu abin da ya kasance jawabin mutanensa, face ɗai suka ce: "Ku fitar da su daga alƙaryarku: lalle ne sũ, wasumutane ne masu da'awar tsarki!"

83) "Sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da iyalansa, face matarsa, ta kasance daga masu wanzuwa"

84) "Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa; Sai ka dũba yadda aƙibar masu laifi ta kasance!"

Haka kuma bayanin hallakar da tsohuwar (wato matar Annabi Lud AS) da kuma mutanensa yazo a cikin Suratu Ash-Shu'araa daga ayata 165 har zuwa ayata 175

165) "Shin kuna j wa maza daga cikin talikai?"

(Yana nufin kuna luwadi?)

166) "Kuma kuna barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga matanku? A'a, ku mutane ne masu ƙẽtarwa!"

167) Suka ce: "Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, ya Lũɗu! Tĩlas ne kana kasancwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)."

(Ya zama tilas ga kowanne musulmi yayi hani kuma ya qyamaci wannan ta'asa ta auren jinsi kamar yanda Annabi Lud AS ya qi sa)

168) Ya ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, ina daga masu ƙinsa."

169) "Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyalĩna daga abin da suke aikatawa."

170) Saboda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutanensa gaba ɗaya

(إِلَّا عَجُوزًا فِي الْغَابِرِينَ )

171) Face wata tsohuwa a cikin masu wanzuwa

(Wannan tsohuwar itace matar Annabi Lud AS, wadda masu bincike suka ce sun gano gawarta a suffar dutse wanda ke daukeda sinadarin gishiri a kasar Jordan. Wallahu a'alam)

172) Sa'an nan kuma Muka darkake wasu

173) Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana

174) Lalle ne ga wannan, akwai aya, kuma mafi yawansu ba su kasance masu ĩmani ba

(To ammanfa dukda haka idan sun tuba Allah mai Jin Kai Ne ga bayinSa kamar yanda ya rufe labarin da:)

(وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ )

175) Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwayi, Mai jin ƙai

Sannan kuma yawancin zanen dake garin na Pompeii duk zanen mata da maza ne tsirara, wanda tanan ne aka fitar da ma'anar pornography wato rubutun mace karuwa kamar dai yanda bayani ya gabata

Haqiqa Iblis yana aiki a zuciyarmu laakari da labarin wani kafirin da ya musulunta yazo wajen Shaikh Hamza Yusuf Hanson (Founder Zaytuna College dake California, USA), kafirin yace masa yanzu ya kasance yana Istighfari amman hotunan blue films din da yake kalla kafin ya musulunta suna dawo masa kamar dai suna masa gizo. Wannan shi ne illar ido, wanda ko da ka rufe shi to zuciyarka za ta dinga suranta maka su

A wata gayyata ta musamman da Robert George (wanda sun fara haduwa ne a Witherspoon Institute) yayiwa Shaikh Hamza Yusuf a Princeton University, wanda aka bashi lecture mai taken: "Muslim voice about the problem of pornography" ma'ana: "Muryar musulmai akan matsalar kallon fina-finan batsa", yace; pornography ba matsala bace ba, sakamakon matsala ne, babbar matsala itace lust wato sha'awa

Hamza Yusuf ya ci gaba da cewa, abinda ya bashi mamaki shi ne bayanan da abinda Pamela Paul ta fada a cikin littafin ta mai suna "Pornified", a wani conference da suka yi a Princeton University. Tace: "Masu kallon pornography ba sa kula da cewar suna fadawa state of heightened stimulation wato tarkon saurin motsawar sha'awa saboda yawan ganin mace da namiji a tube, haihuwar uwa silar haka suke dabi'antuwa da cutar homo erotic impulses

A cikin tattaunawar da Pamela ta yi da wadanda suka dabi'antu da kallon batsa sunce a hankali a hankali suka fara yanzu kuma ji suke zasu iya zina da qananan yara

Imam al-Busairy (Rahimahullah), ya ce: kada kayi fada da kanka akan abinda ya rinjayeka. Misali; yawan cin abinci zai iya saka maka cutar qiba

Imam al-Ghazzali (Rahimahullah) yace; sha'awa ta rabu gida biyu. Na farko shi ne; sha'awar cin abinci domin kula da lafiyarmu. Na biyu kuma; sha'awar sex wato saduwa ta mu'amalar jinsi da jinsi domin kula da tsatson bani Adam

Akwai wani littafi da J.D Unwin ya wallafa mai suna "Sex and Culture" wato "Saduwa da Al'ada", wanda yayi bayani sosai akan yanayin al'adun mutane akan saduwa

A lokacin da Shaikh Hamza Yusuf ya kammala wata lecture a RIS (Reviving the Islamic Spirit) a garin Toronto, dake Canada yace; bayan ya gama, akwai matan aure da yawa da suka zo suka sameshi sukai masa bayani akan mazajensu suna yawan kallon fina finan batsa sun rasa me zasuyi musu. Jin haka, yayi matuqar mamaki ta yanda har abin yakai ga haka. Ya basu shawarar babu wani zunubi da mutum zai kasa dainawa saidai idan bai nemi taimakon Allah Azzawajallah ba

Kamar yanda wata baiwar Allah ta yiwa Shaikh Assim Alhakim tambaya lokacin da aka gayyacemu wani conference mai taken "Journey Of Faith: A Path To Paradise" anan "The Afficient" dake Nasarawar jiharmu ta Kano, tace masa; malam na kasance ina yawan aikata zunubbai a boye, shin Allah SWT zai min gafara?

Ni kaina amsar da Shaikh Assim Alhakim ya bayar ta bani dariya (dayake mutum ne mai barkwanci), ya ce: Idan da za kiyi ta zunubi sau ba adadi kuma kiyi ta tuba na adadin to Allah Gafurur Rahim ne zai karbi tubanki

Ya bada wannan amsar ne a shekarar 2019, lokacin muna tare da Shaikh Muhammad Salah, John Fontain, Dr. Jabir Maihula Sokoto, Ashraf Sunusi Lamido da Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya. (Ya Allah ka ci gaba da hadamu da mutanen alkhairi magada annabawa)

Don haka a karshe shawarar da zan bamu itace mu dinga yawaita Istighfari a ko da yaushe. Domin kuwa ko iya yawan kallace kallacen fina finan batsan nan kan iya zama sanadin janyo mana halin da muke ciki na tsadar rayuwa

Wallahu ta'ala a'alam

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments