𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Malam. Malam dan ALLah wata matsala ce da
wata kawata nakeso inyi tambaya akanta wallahi malam ita yarinya ce sai Allah
yasa ta aure miji babban mutum to shi kuma baya iya biya mata bukatarta ta
aure, daga ya fara jima'i shike nan har ya biya bukatarsa ita kuma kullum kamar
wanda ake kara mata bukatarta. Idan har ya biya tasa ba zai kara amfani da ita
ba. Ta kai inhar taga wani namijin da ya burgeta sai tana kiyasta yadda za tayi
rayuwar aure dashi (alhali fa ba mijinta bane). kuma har suna da yara da shi
wannan mijin nata, shi yasa mukeso muji menene mafita acikin wannan abun. Dan
wallahi tana cikin wata babbar matsala tana bukatar mafitar wannan abun.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Mafita ta farko acikin al'amari irin wannan ita ce jin
tsoron Allah. Wajibi ne duk matar da ta tsinci kanta a irin wannan yanayin ta
sanya tsoron Allah azuciyarta, ta guje ma kalle-Kallen duk abinda zai tada mata
sha'awa, tun daga kallon fina finai, har karanta irin novels ɗin nan na hausa.
Sannan ta guji shiga shafukan dake nuna batsa a internet, da
groups ɗin batsa a
facebook ko whatsapp ko duk wata kafar sadarwa.
Sannan ki dubi mijinki amatsayin wani jagora ne na musamman
wanda Allah ya haɗaki
dashi domin ya jagoranci rayuwarki tanan duniya, da kuma samun dacewa arayuwar
lahira.
Sannan wajibi ne ki amince wa zuciyarki cewar Allah bai
halicci ɗan Adam don
cin abinci da shan abin sha da kuma jima'i ba. A'a Allah ya yimu ne domin mu
bauta masa mu samu dacewa da rahamarsa.
Shi Ɗan Adam abu biyu ne. Wato jiki da ruhi. Shi jiki yana ginuwa
ne ta hanyar ci da sha, da kuma biyan bukatar sha'awa. Shi kuwa ruhi yana
ginuwa ne ta hanyar ibadah da yawaita zikirin Allah da kuma tsaftace zuciya.
Idan kika rinjayar da bukatun jikinki akan bukatun ruhinki,
to kin hallaka. Domin babu abinda hakan zai haifar miki sai nadamar duniya da
lahira. Amma idan kika rinjayar da bukatun ruhinki bisa bukatun gangar jikinki,
to in Sha Allahu za ki samu dacewa da tsaftacecciyar rayuwa aduniya da lahira.
Allah ya umurci Annabinsa Sallallahu alaihi Wasallam cewa
وَقُلْ
لِلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ
...
"Kuma ka gaya wa muminai mata cewa su runtse
idanuwansu, kuma su kiyaye farjojinsu......" (Surah: An-Noor, Ayat: 31)
Sannan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yace "Shi
Kallo, wata kibiya ce mai dafi (wato poison) daga kibiyoyin Shaiɗan. Duk wanda yabar shi
dan tsoron Allah, Allah zai sanya masa wani hasken imani wanda zai ji ɗanɗanonsa acikin zuciyarsa".
Ki gode wa Allah da ya baki lafiya kuma ya baki miji nagari,
kici gaba da kyautata mu'amalarki dashi domin shi ne kaɗai rabonki daga cikin mazaje. Ki dena hangen
wasu mazan domin yin hakan ba zai haifar miki da alheri ba.
Awajen jima'i kuma, ki yawaita yin wasanni da mijinki kafin
jima'i, sannan idan da hali ki rika haɗa
mishi wasu nau'o'in kayan marmarin dazai rika sha da yamma ko bayan isha'i
domin samun nishaɗi
wajen kwanciyar aure. Misali kamar ki haɗa
masa irin su abarba, kankana, da ayaba yaci yasha.. In sha Allahu zai sami
Qaruwar Qarfi da nishaɗii.
Idan kuma yana da wata larura ta musamman kamar hawan jini
ko ciwon sugar (Diabates) to sai ku kiyaye dokokin kula da chutar, kuma arika
amfani da magani yadda ya dace da umurnin likitoci.
Daga karshe za ki iya neman Saki akan wannan matsalar.
Saboda za a Kalli yanayinki, ma'ana bukatuwarki da namiji, dan Kar ki fada
cikin Halaka (zina).
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.