𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mun samu matsala da
mijina ne: Ba ma shiri yau kusan watanni biyu ke nan, yanzu har ya fara fita daga
raina saboda halin ko-in-kula da yake nuna min. Ina mafita?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Yanzu wannan mai tambayar - ko wata ma ba ita ba - za ta iya
tambayar cewa: ‘Mun samu matsala da mahaifina?’ Har da bayanin cewa: ‘Ba ma
shiri da shi mahaifin nawa na kusan watanni biyu?’ Sannan kuma har da cewa:
‘Yanzu mahaifin har ya fara fita daga raina saboda halin ko-in-kula da yake
nuna min?!’
Na san abu ne mawuyaci wannan tambayar ta fito daga wata
mace, ba a kan mahaifi ko mahaifiyarta ba, har ma a kan yayyi ma abu ne ba mai
yiwuwa ba, inshaa’Allaah. Saboda yanayin yadda gidajenmu suka ginu a kan
tarbiyya da girmama iyaye da sauran na-gaba. To, amma meyasa ake samun hakan a
kan miji, alhali kuwa miji ya fi mahaifi matsayi a mahangar addininmu na
musulunci?!
Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa wa wata mace matsayin
mijinta a wurinta, inda ya ce: Shi ne Aljannarki kuma shi ne wutarki! Haka kuma
da aka tambaye shi a kan mafi girman haƙƙi a kan mace sai ya ce: Mijinta. Bai
ambaci mahaifinta ko mahaifiyarta ba, balle kuma ƙawarta ba!
Don haka, bai kamata duk mai imani ya yi wasa da abin da
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: Shi ne Aljannarsa ko
Wutarsa ba, matuƙar dai akwai imani da tunani da hangen-nesa.
Yawanci abin da ke saka mata a cikin wannan matsalar shi ne
irin maganar da suka gada daga wasu yayyi da ƙawayensu cewa: MIJI GOMA BA UBA GOMA BA
NE! Watau ana iya sauya miji har sau goma, amma ba a iya sauya uba! Haka ne.
Amma dai shi ma miji ba kanwar lasa ba ne, kuma ba abin wasa ba ne, kamar yadda
hadisan da suka gabata suka nuna.
Don haka, mafita a ganina kawai ita ce: Idan kin san akwai
wani abu da ke kike aikatawa ko wanda kika aikata da ya janyo wannan rashin
shirin a tsakaninku, to wajibi ne ki yi gaggawar komawa ki janye wannan abin
domin a cigaba da rayuwa, kar Aljannarki ta samu matsala.
Idan kuma shi ne yake da laifi, to duk da haka dai gara ki
yi haƙurin
zama tare da shi domin a samu maslaha, irin yadda za ki yi in da mahaifinki ne
a matsayinsa. Gudun kar Aljannarki ta samu matsala.
Idan kuma shi ne yake zaluncin da har ba za ki iya jurewa
ba, to har hakan dai bai kamata ya zama babu shiri ba. Matakan sulhu ya kamata
ku ɗauka domin samun
mafita.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.