Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Yi Wa Allah Alƙawari Idan Na Sake Aikata Zunubi Zanyi Azumin Wata Guda. Sai Kuma Na Sake Aikata.

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Mutum ne ya tuba daga wani saɓo da yake aikatawa, har kuma ya yi wa Allaah alƙawarin idan ya sake aikatawa, to zai yi azumin wata guda. Sai kuma ya sake aikatawan. To ina hukunci?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Wannan ya shiga ƙarƙashin abin da ake cewa: An-Nazru (alwashi), wato mutum ya ɗora wa kansa wani aiki na ƙarin kusanci ga Allaah, ya mayar da shi wajibi a kansa.

Sai dai kuma malamai sun ce shi An-Nazru ɗin iri-iri ne

1. Nazrul Qurbah Wat-Taa’ah: Shi ne mutum ya ɗora wa kansa wani aiki daga cikin ayyukan ɗa’a ga Allaah Ta’aala, kamar sallah ko azumi ko sadaka da makamantan hakan. Wannan ɗin kuma nau’i biyu ne

i. Nazrul-Mutlaq: Shi ne wanda aka yi shi a matsayin godiya ga Allaah a kan wata ni’ima kawai, ba domin wani dalili ba, kamar ya ce: Azumi ga Allaah ya wajaba a kaina. A kan irin wannan ne ake saukar da nassoshin da suka zo a kan yabon masu yin alwashin, kamar maganar Ubangiji Ta’aala

إِنَّ الْأَبْرَارَ يَشْرَبُونَ مِنْ كَأْسٍ كَانَ مِزَاجُهَا كَافُورًا

عَيْنًا يَشْرَبُ بِهَا عِبَادُ اللَّهِ يُفَجِّرُونَهَا تَفْجِيرًا

 يُوفُونَ بِالنَّذْرِ وَيَخَافُونَ يَوْمًا كَانَ شَرُّهُ مُسْتَطِيرًا

Lallai mutanen kirki za su sha daga cikakkun kofunan giya wanda abin gauraya shi kaafuur ne. Wani marmaro ne wanda bayin Allaah suke sha daga gare shi, suna ɓuɓɓugar da shi ɓuɓɓugarwa. Suna cikawa da alwashinsu kuma suna tsoron wani yini wanda sharrinsa mai tartsatsi ne. (Surah Al-Insaan: 5-7).

ii. Nazrul-Muqayyad ko Nazrul-Mujaazaat: Shi ne wanda mai yin sa ya rataya alwashin a ƙarƙashin wani sharaɗi, kamar ya ce: ‘Idan Allaah ya warkar da mara lafiyana azumin kwana kaza ya hau kai na.’ wannan irin alwashin ake nufi da nassoshin da suka zo da zargi a kansa kamar wannan

Daga Ibn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa) ya ce

نَهَى النَّبِىُّ - صلى الله عليه وسلم - عَنِ النَّذْرِ قَالَ « إِنَّهُ لاَ يَرُدُّ شَيْئًا ، وَإِنَّمَا يُسْتَخْرَجُ بِهِ مِنَ الْبَخِيلِ » .

Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya hana yin alwashi, ya ce: ‘Ba ya mayar da komai (na ƙaddara), kaɗai da shi ake fitarwa daga marowaci.’ (Sahih Al-Bukhaariy: 6608).

2. Nazrul Ma’asiyah: Kamar wanda ya yi alwashin aikata wani saɓo, kamar shan giya ko yin zina ko sata, ko yin azumi a ranar Idi ko kuma yin yanka ko zuba gari a kan ƙabari, da sauransu. Hadisi daga Aishah (Radiyal Laahu Anhaa), daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« مَنْ نَذَرَ أَنْ يُطِيعَ اللَّهَ فَلْيُطِعْهُ ، وَمَنْ نَذَرَ أَنْ يَعْصِيَهُ فَلاَ يَعْصِهِ »

Wanda ya yi alwashin zai yi wa Allaah ɗa’a, to ya yi masa ɗa’a. Wanda kuma ya yi alwashin zai saɓa wa Allaah, to kar ya saɓa masa. (Sahih Al-Bukhaariy: 6696).

3. Nazrul Lijaaj Wal-Ghadab: Shi ne ya yi alwashin a cikin fushi ko a lokacin husuma, kamar ya rataya alwashin a kan wani sharaɗi da nufin hana kansa aikata wani abu ko ɗora shi a kan aikata wani abu, kamar ya ce: ‘Idan na aikata abu kaza zan yi azumin wata ko shekara’, ko ya ce: ‘Idan ban aikata abu kaza ba zan bayar da dukiyata sadaka saboda Allaah.’ Ka ga wannan ba nufin shi yin azumi ko sadaka ba ne. Manufarsa kawai ya ɗora kansa ne a kan aikata abin, ko kuma hana kansa aikata abin da ya faɗa.

Malamai sun ce

Hukuncin irin wannan alwashin shi ne hukuncin rantsuwar da aka rataya ta a kan wani sharaɗi, yana da daman zartar da alwashin, ko kuma ya bar ta ya yi kaffarar rantsuwa. Wannan ne zaɓin Shaikhul-Islaam Ibn Taimiyah a cikin Majmuu’ul Fataawaa: 35/253.

Riwaya ta tabbata daga Sahabi Abdullaah Bn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) ya ce:

« مَنْ نَذَرَ نَذْرًا لَمْ يُسَمِّهِ فَكَفَّارَتُهُ كَفَّارَةُ يَمِينٍ ، وَمَنْ نَذَرَ نَذْرًا فِى مَعْصِيَةٍ فَكَفَّارَتُهُ كَفَّارَةُ يَمِينٍ ، وَمَنْ نَذَرَ نَذْرًا لاَ يُطِيقُهُ

فَكَفَّارَتُهُ كَفَّارَةُ يَمِينٍ ، وَمَنْ نَذَرَ نَذْرًا أَطَاقَهُ فَلْيَفِ بِهِ ».

Wanda ya yi wani alwashin da bai ambaci sunansa ba, to kaffararsa ita ce kaffarar rantsuwa. Kuma wanda ya yi alwashi a cikin saɓon Allaah, to kaffararsa ita ce kaffarar rantsuwa. Kuma wanda ya yi alwashin da ya kasa iya zartar da shi, to kaffararsa ita ce kaffarar rantsuwa. Kuma wanda ya yi alwashin da yake iya zartar da shi, to lallai ya cika alwashinsa. (Sunan Abi-Daawud: 3324).

Kaffarar rantsuwa kuwa ita ce a cikin maganar Ubangiji Tabaaraka Wa Ta’aala

لَا يُؤَاخِذُكُمُ اللَّهُ بِاللَّغْوِ فِي أَيْمَانِكُمْ ، وَلَـــكِنْ يُؤَاخِذُكُمْ بِمَـــا عَقَّدْتُمُ الْأَيْمَانَ ، فَكَفَّارَتُهُ إِطْعَامُ عَشَرَةِ مَسَاكِينَ مِنْ أَوْسَطِ مَــا

تُطْعِمُونَ أَهْلِيكُمْ أَوْ كِسْوَتُهُمْ أَوْ تَحْرِيرُ رَقَبَةٍ ، فَمَـــنْ لَمْ يَجِدْ فَصِيَامُ ثَلَاثَةِ أَيَّامٍ . ذَلِكَ كَفَّارَةُ أَيْمَانِكُمْ إِذَا حَلَفْتُمْ ، وَاحْفَظُوا

أَيْمَانَكُمْ ، كَذَلِكَ يُبَيِّنُ اللَّهُ لَكُمْ آيَاتِهِ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ

Allaah ba ya kama ku a kan rantsuwoyi na wargi, amma dai yana kama ku ne a kan rantsuwar da kuka ɗaura zuciya a kanta. To kaffararta: Ciyar da musakai guda goma ne daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyalinku, ko tufatar da su, ko kuma ’yanta baiwa. Wanda kuma bai samu iko ba, to sai ya yi azumin kwanuka uku. Wannan ne kaffarar rantsuwoyinku idan kun karya rantsuwoyin. Sai ku tsare rantsuwoyinku. Kamar haka ne Allaah yake yi muku bayanin ayoyinsa ko kwa gode masa. (Surah Al-Maa’idah: 89).

Don ƙarin bayani ana iya duba Tamaamul Minnah: 4/380-388.

Allaah ya ƙara mana ilimi mai amfani.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments