Ticker

Najasa A Jikin Tufa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Ni ne na dawo sallar Isha’i yanzun nan sai na ga busasshen najasa a wandona, to yaya matsayin sallar ke nan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Sahabi Abu-Sa’eed Al-Khudriy (Radiyal Laahu Anhu) ya riwaito cewa: Watarana Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yana cikin yin sallah da sahabbansa sai aka ga ya cire takalmansa ya ajiye su a gefen hagunsa. Da sahabbansa suka ga haka sai su ma suka ciccire takalmansu. Da ya kai ƙarshen sallar sai ya tambaye su: Meyasa kuka kwaɓe takalmanku?’ Suka ce: Mu dai mun ga ka kwaɓe takalmanka, shi ne mu ma muka kwaɓe takalmanmu. Sai ya ce

« إِنَّ جِبْرِيلَ -صلى الله عليه وسلم- أَتَانِى فَأَخْبَرَنِى أَنَّ فِيهِمَا قَذَرًا ». وَقَالَ « إِذَا جَاءَ أَحَدُكُمْ إِلَى الْمَسْجِدِ فَلْيَنْظُرْ فَإِنْ رَأَى فِى نَعْلَيْهِ قَذَرًا أَوْ أَذًى فَلْيَمْسَحْهُ وَلْيُصَلِّ فِيهِمَا ».

Haƙiƙa! Malaika Jibril (Alaihis Salaam) ne ya zo ya sanar da ni cewa, akwai ƙazanta a jikinsu. Ya ce: Idan ɗayanku ya zo masallaci to ya duba, idan ya ga ƙazanta ko najasa a jikin takalmansa sai ya goge ta, kuma ya yi sallah da su. (Ahmad da abu-Daawud da Ad-Daarimiy suka riwaito shi, kuma Al-Albaaniy ya inganta shi a cikin Al-Irwaau: 284).

Wannan hadisin dalili ne a kan kawar da najasa daga jikin tufafi kafin tsayawa a wurin Sallah. Sai dai sun sha bamban ne a kan hukuncin hakan

Mazhabar Shaafi’iyyah da Hambaliyyah da Hanafiyyah sun zaɓi cewa sharaɗi ne na ingancin sallah.

Daga Al-Imaam Maalik kuma an samu riwayoyi biyu: Na-farko: Gusar da najasa Sunnah ce ba farilla ba ce. Na-biyu: Yin hakan farilla ne tare da tunawa, amma tana faɗuwa tare da mantuwa.

Al-Imaam As-Shawkaaniy kuma ya zaɓi cewa: Gusar da najasa wajibi ne amma ba sharaɗi ba ne.

Daga cikin dalilansa akwai wannan hadisin na Abu-Sa’eed da ya gabata. Domin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cigaba da sallar ya yi bayan an sanar da shi cewa akwai najasa a jikin takalminsa bayan ya rabu da ita, bai tsaya ba. Idan da sharaɗi ne da kuwa ya maimaita ta daga baya. (Tamaamul Minnah: 1/203).

A ƙarƙashin wannan akwai masaloli kamar haka

Babu komai a kan wanda ya ga najasa a jikin tufafinsa bayan ya yi sallama daga sallarsa. Sallarsa ta yi. Sai dai zai gaggauta wanke ƙazantar kawai domin abin da zai biyu na salloli.

Amma idan yana cikin sallar ce ya tuna ko aka tuna masa da najasar, to sai ya rabu da najasar kamar idan a jikin tufar da yake iya rabuwa da ita ne ba tare da buɗe tsiraicinsa ba.

Idan kuwa ba zai yiwu ba, to sai ya yi sallarsa a hakan muddin dai ya ji tsoron ficewar lokaci. Domin kiyayewa a kan lokacin sallah ya fi kiyayewa a kan tsarki a cikinta, in ji malamai.

Allaah ya fahimtar da mu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments