Nazarin Kalmomin Ta’addanci a Cikin Wasu Wakokin Baka

Citation: Sarkin Fada, I. (2024). Nazarin Kalmomin Ta’addanci a Cikin Wasu Waƙoƙin Baka. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 358-363. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.041.

Nazarin Kalmomin Ta’addanci a Cikin Wasu Wa ƙ o ƙ in Baka

Daga

Isah Sarkin Fada
Sashen Harsuna Da Al’adu
Jami’ar Tarayya Gusau
isahsarkinfada@gmail.com
08039165872

Tsakure

Samar da tsaro shi ne babban lamarin da al’umar Zamfara suke bu ƙ ata a yau . Rashin tsaro ya dami kowa da kowa, babu yaro babu babba, ya game birane da ƙ auyuka. Saboda haka, a wannan ma ƙ ala mai taken Nazarin Kalmomin Ta addanci a Wasu Wa ƙ o ƙ in Baka, an yi ƙ o ƙ arin fitowa da kalmomin ta addanci da mawa ƙ a ke amfani da su a yayin rera wa ƙ o ƙ insu. Manufa a nan ita ce, fitowa da muhimmiyar rawa da wa ɗ annan kalmomi ke takawa wajen bun ƙ asa harshen Hausa, ta hanyar nuna gwaninta da ƙ warewa da kuma iya sarrafa harshen Hausa da mawa ƙ a da su. Dubarun da aka yi amfani da su wajen gudanar da wannan bincike shi ne, kawo baitocin wa ƙ a daga wa ƙ o ƙ i daban-daban da kaurara kalma mai nuni da ta’addanci da bayanin yanayin ƙ irarta da kawo ajin kalmar da kuma sharhi a kan muhallin da kalmar ta fi dacewa ta zo a tsarin jumla. Ra in da aka yi amfani da shi wajen gudanar da wannan ma ƙ ala shi ne, ra in dangantakar harshe da rikici (Language of Violence) na Smith, Alison G. da wasu (2008). Bugu da ƙ ari, binciken ya fito da sakamako da suka ha ɗ a da; tabbatar da rukunin kalmomin ta’adanci a harshen Hausa da kuma rawar da suke takawa a ɓ agaren ilmin walwalar harshe.

Ke ɓ a ɓɓ un Kalmomi: Kalma, Ta’addanci, Wa ƙ ar Baka

1.0 Gabatarwa

Matsalar tsaro a Arewa maso Yammacin Nijeriya ta shafi kowa, kama daga gwamnatoci da hukumomi da ɗ ai ɗ aikun mutane. Lamarin ya na bu ƙ atar kowa ya taka muhimmiyar rawa rsa domin ganin an kawo ƙ arshen s a. Wannan ya ba da damar shigowar masana harshe da adabi da al’ada wajen amfani da kalmomi daban-daban masu nuna ta’addanci da makamantansa. A wannan bincike an yi ƙ o ƙ arin kawo asalin kalmar ta addanci da ma anar ta addanci da ma anar ƙ irar kalma kamar yadda (Sani, 2011:5) da (Crystal, 2008:340) suka bayyana. Haka ma, mu ƙ ala ta kawo ma anar wa ƙ a da kuma yadda mawa ƙ a suka fito da kalmomin ta addanci a wa ƙ o ƙ insu. Sha anin ta addanci ba sabon abu ba ne, domin ɓ angaren adabi da al’ada sun fito da kalmomi masu yawa da ke nuni da ire-iren wa ɗ annan kalmomi, kama daga wa ƙ oki da karin magana da kirari da sauransu. Wasu kalmomi na aro ne, wasu kuwa an fa ɗ a ɗ a ma’anarsu. A yayin da wasu kuwa an yi masu kwaskwarima ne.

1.1 Dubarun Bincike

Dabarar da aka yi amfani da ita domin samun nasarar aiwatar da wannan binciken sun ha ɗ a da nazartar wasu baitocin wa ƙ ar baka da ke ɗ auke da kalmomin ta’addanci. Bugu da ƙ ari, binciken ya yi nazarin ƙ irar kalmomin ta addanci da azuzuwansu na nahawu. Kasancewar mawa ƙ an baka mutane ne masu hikima da fasaha wajen sarrafa harshen Hausa, suna amfani da kalmomin ta addanci a wa ƙ o ƙ in da suke rerawa. Wa ɗ annan kalmomi suna da bambanci a wajen ƙ irarsu da kuma azuzuwan nahawu. Haka kuma kowace kalma akwai ɓ angaren da ta fi dacewa ta zo a sha’anin tsarin j u mla. Wasu kalmomi ana sumun su har ɗ a ɗɗ u ne, wato a ha ɗ e kalma biyu ko fiye su ba da ma’ana ɗ aya. Wasu kuwa, an yi masu kwaskwarima ne, domin su dace da harshen Hausa. A yayin da wasu kuwa, kalmomi ne na aro, ko dai daga harshen Ingilishi ko na Larabci ko kuma Fulatanci. Wasu kalmomi kuwa an fa ɗ a ɗ a ma’anarsu ne. Dangane da ajin nahawu kuwa, akan sami wasu kalmomi a mabambantan azuzuwa, ko dai ajin suna ko na aikatau ko na sifa ko bayanau da sauransu. Haka kuma, akan sami kalmomi su sami kansu ko dai a yankin suna ko a yankin aikatau, wasu kuwa suna iya kasancewa a kowane ɓ angare. Wannan na faruwa dangane da yadda kalma ta samu kanta a j u mla.

1.2 Ra’in Bincike

R a’in da aka yi amfani da shi wajen gudanar da wannan bincike shi ne , ra’in ‘Dangantakar Harshe da Rikici’ ‘Language of Violence’ na Smith, Alison da wasu (2008), wanda Randall (2010) ya fa ɗ a ɗ a. Wannan ra’i ya yi magana a kan sadarwa tsakanin ‘yan ta’adda da wa ɗ anda ke ya ƙ ar su. Ra’in ya bayyana cewa harshe shi ne kanwa uwar gami ga dukkan al’amurra, domin babu abin da za a aiwatar ba tare da an yi amfani da shi ba. Hakazalika, da harshe ne ake iya gane kowane mutum da halinsa da kuma aikinsa . Ra’in ya nuna cewa, da harshe ake am fani wajen dabarun ya ƙ i domin isar da sa ƙ o da tunkarar abokan gaba. Wa ɗ anda suka yi aiki wajen ɗ abba ƙ a wannan ra in akwai Antonio Sanfilippo da wasu (2013) da Houck (2013) da Corway (2017) da Richard Frank (2021) wa ɗ anda duk sun yi amfani da ra’in. Cullough (2022) ya yi wa ra’in kwaskwarima ta ɓ angaren ta’addanci da ramuwar gayya inda ya dubi ayyukan ta’addancin da ke faruwa a sassa daban-daban na duniya, musamman yankin ƙ asashen Larabawa.

 Bugu da ƙ ari, ana amfani da harshe wajen yayata manufar yan siyasa da malaman addinai da kuma gudanar da tallace-tallace. Bugu da ƙ ari, ra in ya yi ƙ o ƙ arin nazarin sadarwar yan ta adda ta ɓ angarori daban-daban da sukan yi domin cimma bu ƙ atunsu na yau da kullum. Ra’in ya bayyana cewa, masana ba su mayar da hankali a kan abin da ya shafi harshen ta’addanci ba, shi ne dalilin da ya sa aka samar da wannan ra’i. Bugu da ƙ ari, ra in ya yi ƙ o ƙ arin fito da ƙ udurori guda uku da mai nazarin harshen ta addanci ya kamata ya kula da su kamar haka:

a.   La’akari da yanayi da halayyar ‘yan ta’adda a lokacin da suke sadarwa. Wannan dabara tana taimakawa ƙ warai wajen gano ma anar abubuwan da suke furtawa.

b.   Nazarin kalmomi da jumlolin da aka samu daga ‘yan ta’adda, domin fito da ma’anarsu ta asali da kuma sabuwar ma’ana.

c.    Kalmomin da suke furtawa su dace da nazarin da ake a kai, domin shi zai ba i wa mai nazari damar bin diddigin kowace kalma ta fuskar ma’ana.

2.0 Ma’anar Kalma

Ɓ angaren ƙ irar kalma fanni ne shafi ilmin kimiyar harshe, domin shi ke nuna bun ƙ asa da fa ɗ a ɗ a da yalwar da harshe ke samu ta hanyar samar da sababbin kalmomi. Harshen Hausa ya samu sababbin kalmomi ta hanyar ƙ ir ƙ ira da aro da kwaikwaya da kwaskwarima da har ɗ antawa da suka saje da kalmomin da yake da su domin amfanin yau da kullum. Har wa yau, masana sun bayyana ƙ irar kalma kamar haka:

Galadanci da wasu (2005, p. 56) ya bayyana kalma da cewa: ‘taron ba ƙ a ƙ e da wasulla da za a ji suna magana ne a kan wani abu wanda za a iya gani ko aji, ko za a iya tunaninsa. Watau ya ba da ma ana ke nan.’

A nan, kalma ta ƙ unshi ƙ wayar ma ana ko kuma ba ƙ a ƙ e da wasulla da ake iya ji, ko a gani, da ke da wata ma ana ta musamman.

2.1 Ma’anar Ta’addanci

Ta’addanci kalma ce da ta bazu ta yi rassa a Arewa maso Yammacin Nijeriya da ta haifar da ayyuka masu illa da lahani da ke iya haifar da sanadiyar rasa rayuwar mutum da dukiyarsa. Ta’addanci ba sabon abu ba ne a Arewa maso yammacin Nijeriya da ma Arewacin Niyeriya. Saboda haka, masana sun bayar da ma’anar ta’addanci kamar haka:

Abraham (1947, p. 397) ya bayyana ta’addanci kamar haka:

Bad manner that serious misdemeanour.’

Fassarar mai bincike:

‘Ta’addanci yana nufin aikata wani mummunan hali da al’umma suke ƙ yama.

Wannan ma’ana ta yi daidai da abin da wannan ma ƙ ala take bu ƙ atar fitowa da shi, saboda a nan ana son a san mene ne ta addanci? Kafin nazarin ƙ ir ƙ irarrun sunaye da suka samu ta dalilin ayyukan ta addanci.

Ƙ amusun Hausa na Jami’ar Bayaro (2006, p. 415) yana cewa:

Ta’addanci yana nufin mugun aiki, musamman na haddasa ɓ arna kamar lalata abubuwa ko kisa da sauransu, don bambancin siyasa ko addini.

A fahimtar mu ƙ ala, ta addanci shi ne aikata wani aiki da ke da matu ƙ ar illa, wanda yake iya zama sanadiyar rasa rayuwa da dukiyoyin al umma.

2.2 Asalin Kalmar Ta’addanci

Ta’adddanci abu ne da al’umma ba suke ƙ yama, wanda yake haddasa ɓ arna da illata dukiyoyin al’umma. Bugu da ƙ ari, ta addanci yakan haifar da rasa rayukan al umma, musamman a wuraren da ake aiwatar da shi. Dalilin haka ya sa masana suka yi ƙ o ƙ arin lalubo asalin kalmar. Mun yi dace Atuwo (2009, p. 13) ya fito da asalin kalmar ta addanci. Ga bayanin an tsakuro:

Kalmar ta’addanci ta samu asali ne daga kalmar Larabci wato ‘Ta’adda’. Ma’anar wannan kalma ta zahiri ‘ta’adda’ na nufin ƙ etere iyaka ko kuma yin zalunci. Wannan kalmar ta fito a Al ƙ ur ani mai girma a wurare masu yawa da aka yi amfani da nuni da da cin zarafin wani da wuce iyaka. Amma an yi amfani da wannan kalmar a Ba ƙ ara kan zubar da jini da kisa da rauni. Harshen Hausa kan yi aron kalmomi daga wasu harsuna sannan daga baya a yi amfani da su a sassa ko fannonin rayuwa iri-iri, misali, siyasa da addini da mulki da ciniki da ilmi da shari’a da kimiya da ƙ ere- ƙ ere da fasaha. A haka ne kalmar ta addanci ta sami shigowa daga Larabci zuwa Hausa a sashen kalmomin addinin Musulunci .”

Wannan shi ne asalin kalmar ta’addanci ta gama-gari. A nan bincike ya fahinci cewa kalmar ta’addanci ba Bahaushiyar kalma ba ce, an aro ta ne daga harshen Larabci. Sannu a hankali kalmar ta koma Bahaushiya.

2.3 Kalmar Ta’addanci a Hausa

 Harshe yana bun ƙ asa da fa ɗ a ɗ a a dalilin yawan masu magana da shi da kuma yawan kalmomin da yake sarrafawa a yayin zantuka na yau da kullum. Harshen Hausa ya yi zarra, musamman ga ‘yan uwansa, saboda yawan kalmomin da yake da su. Wasu kalmomi an aro su ne daga harsuna daban-daban.. Dangane da asalin kalmar ta’addanci a harshen Hausa an yi dace Atuwo (2009, p. 17-18) ya yi bayani a kai. Ga bayanin an fito da shi :

Asalin kalmar ta’addanci a Hausa na da ala ƙ a da wata almara ta wani bawan Sarkin Kano wai shi Adda. Wani daga cikin talakawan sarki ya yi laifi har sarki ya tunzura, sai ya kira Adda ya ce ya je ya zo da mai laifin, da zuwan Adda sai ya sa takobi duk ya daddatse mai laifi guntu-guntu ya dawo inda sarki ya fa ɗ a masa aikin da ya yi. Duk da yake sarkin ba haka yake nufin Adda ya yi ba a lokacin, amma ya zama darasi ga sarki duk lokacin da ya aiki bawansa domin ya kira wani sai ya ce “To kada ka yi irin ta Adda”. Sannu a hankali kalmar ta ha ɗ e, saboda maimaitawar harafin mallaka (dogo) jinsin mace (ta) da ake yi da sauri tare da kalmar Adda kamar haka: Ta+Adda= Ta’adda. A hankali wa ƙ afi ya shiga tsakani saboda wasalin (a) biyu da suka kusanci junansu .

Daga wannan almara ake hasashen an samu asalin kalmar ta’addanci a harshen Hausa. Wannan ya nuna cewa tun asali kalmar tana nuni da aikata wani abu da jama’a suka ƙ yamata.

2.4 Ma’anar Wa ƙ ar Baka

Mawa ƙ an baka suna da hikima da azanci wajen rera wa ƙ o ƙ i da ke ɗ auke da sa ƙ onni na musamman ga al umma. Lokuta da dama, wa ɗ annan wa ƙ o ƙ i suna fa ɗ akarwa da ilmantarwa bisa wasu al’amurra da suka shigo ga al’umma. Dangane da bun ƙ asar harshe kuwa, akan samu sababbin kalmomi da kuma fa ɗ a ɗ a ma’anar wasu domin su dace da yanayin da ake bu ƙ ata. Masana sun bayyana ra ayoyinsu dangane da wa ƙ ar baka;

Gusau (1993, p. 1) ya bayyana wa ƙ ar baka da cewa; wani fage ne da ake shirya maganganu na hikima da aiwatarwa a rera cikin rauji tsararre, wa ɗ anda za su zaburar da al’umma da kuma hankaltar da su dangane da dabarun tafiyar da rayuwarsu, da za su ba da damar a cimma ganga mai inganci’.

Kurawa da Gummi (2022:165-170) sun bayar da ma’anar wa ƙ a da cewa; wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa ga ɓ a-ga ɓ a bisa ƙ a idojin tsari da daidaitawa a rere cikin sautin murya da amsa-amon kari da ki ɗ a da amshi’.

Saboda haka, wa ƙ ar baka abu ce da ake rerawa cikin hikima da azanci kuma cikin nisha ɗ i domin birge wanda ake rera wa da kuma wanda ke sauraro. A nan, mun kawo baitoci masu ɗ auke da kalmomin ta’addanci da kuma yin sharhi a kansu.

2.5 Kalmomin Ta’addanci A Wa ƙ o ƙ in Baka.

A nan, an yi ƙ o ƙ arin kawo kalmomin ta addanci a wa ƙ o ƙ in baka da bayaninsu ta ƙ irarsu da ajinsu na nahawu da kuma sashen da kowace kalma ta fi dacewa ta zo a cikin jumla. An ciri kalma ɗ aya bayan ɗ aya tare da bayaninta. Saboda haka duk kalmar da aka kaurara a cikin baitocin da tsara, ita ce kalmar ta’addanci, kuma ita ce aka yi bayaninta.

Jagora: Ni saboda ɓ arayi

 Nay yi ganga

 Ba don wani ƙ ato mai na ɗ i ba.

Gambu Mai Wa ƙ ar Ɓ arayi. Bunza (2014)

Kalmar ‘ ɓ arayi’ kalma ce da ake yi wa ɗ ofane . Ana iya samun jinsi da adadi a kalmar. Misali, Kalmar ‘ ɓ arawo’ tana nuna jinsin namiji kuna tilo. Saboda haka, kalmar tana da tushe ‘ ɓ araw’ da kuma abin da ake ƙ ara wa domin samar da jinsin namiji ko mace ko kuma jam i. Kalmar na nufin mutane masu satar kayan jama a. A ɓ angaren azuzuwan kalmomi kuwa, tana cikin ajin suna. Ɓ angaren ginin jumla, an fi amfani da ita a yankin suna, duk da cewa takan zo a yankin aikatau. Ɓ arayi kalma ce ta ta addanci. Saboda Gambu ya nuna cewa, ya barranta kansa da yi wa kowane irin sarki wa ƙ a sai dai ɓ arawo.

Jagora: Ba ni ki ɗ a garkat talaka,

 Komai ku ɗɗ in ɗ an gaton uwa,

 Ban ra’ayinai ba shi nawa,

 Sai in Allah Ya tsare shi,

 Na hi da jin da ɗ in ɓ arayi,

 Gambo Mai Wa ƙ ar Ɓ arayi. . Bunza (2014)

Ɓ arayi kalma ce da ake yi wa ɗ ofane , kuma tana cikin ajin suna. A ɓ angaren ginin jumla, an fi amfani da ita a yankin suna, amma takan zo a yankin aikatau. Ɓ arayi su ne masu satar kayan jama a. Gambu ya nuna cewa a kodayaushe ya fi son ya ji mai ku ɗ i ya koka ya tsiyace a cikin lokaci ɗ aya. Saboda haka ya fi son ya ji an yi ta’asa.

Jagora: Ki ɗ in halaka ko ni da niy yi shi,

 Ba wani da ɗ i naj jiya ba,

 Tun da dag ga macewa sai rasawa,

 Duk da ni da ka yi nai bai bari ba.

  Gambo Mai Wa ƙ ar Ɓ arayi. . Bunza (2014)

Halaka kalma ce ta aro da aka yi wa kwaskwarima. An aro ta ne daga harshen Larabci. Tana cikin ajin suna. Ta fi zuwa a yankin aikatau a tsarin jumlar Hausa. Kalmar na nufin mutuwa ko lalacewa ko ɓ acewa. Saboda haka, ta’addanci ya ƙ unshi tashe-tashen hankulla da hargitsi wanda ke iya kai ga kashe-kashe. Gambo ya nuna ki ɗ ansa babu abin da yake haddasawa sai rasa dukiya da rayuwa. Saboda haka akwai kalmomin ta’addanci a tattare da wan ɗ annan baitoci.

Jagora : Ni dai ga irin mugun nuhina,

 In ishe mai ku ɗɗ i tsugunne,

 In tar da yana naso ga goshi,

 Kamar da kunama sun ka kauru,

 Ya ɗ ibi gumi bai yo gudu ba.

 Gambo Mai Wa ƙ ar Ɓ arayi . Bunza (2014)

Kalmar mugu kalma ce da ake yi wa ɗ ofane. Tushen kalmar ‘mug’ + harafin ‘u’ = ‘mugu’ ,. Tana ajin suna. Mutum mai mummunan hali na cuta. Nuhi kuwa, kalma ce tilo, kalmar sunan aiki ce. Ƙ udura ko yi niyya ko ra ayin abu a rai. Kunama kalma ce tilo, tana ajin suna. Tana zuwa a yankin suna wani lokaci a yankin aikatau. Kauru kalma ce mai kumbura. Tana cikin ajin aikatau. Ta fi zuwa a yankin aikatau. Gambu ba ya son ya ga masu hali cikin nisha ɗ i duk da kasancewarsu su ne manya a cikin al’umma kuma ana bugun gaba da su. Saboda haka wa ɗ annan kalmomi suna da tasiri a cikin sha’anin ta’addanci.

Jagora: Wa ka bi ɗ an Muhamman Dogo,

 Yanzu gwani ya ƙ as ƙ anta shi,

 Don kowa yab buga bai kwana,

 Don ya yi karo da mamman Dogo.

  Garba Ɗ anwasa. . Bunza (2014).

Ƙ as ƙ anta kalma ce da ake yi wa ɗ ofane , a samar da wasu kalmomi daga tushenta ‘ ƙ as ƙ ant ana yi mata ƙ ari daga farko ko kuma daga ƙ arshe domin a samar da wasu kalmomi daga gare ta. Misali, ma ƙ as ƙ anci, ko ƙ as ƙ antacce ko ƙ as ƙ antattu. A yankin jumla tana zuwa a yankin aikatau. A nan mawa ƙ i na ƙ o ƙ arin zuga ɗ an wasa, ya harzu ƙ a har ya kai ga aikata ta addanci. Kalmar ƙ as ƙ anci kalma ce ta ta addanci domin tana iya kai wa ga kisa.

Jagora: Amsad doki gidan kara mina na ga matsiyaci,

 Bari sai gobe da sahe iskan nan ya taso,

 Mai kwasan sansami yana kar-kar-kar,

 Sannan ɗ ebo wuta ga ragga ka hita,

 Yac ce Kassu shawararka ita ce za ni biya.

  Kassu Zurmi. Dunfawa (2013)

Wuta kalma ce tilo, jam’inta shi ne wutace ( Ƙ amusun Hausa, 2006:473), tana cikin ajin suna. Ta fi zuwa a yankin aikatu a jumla. Ragga kalma ce tilo, tana cikin ajin suna. Kalmar tana zuwa a yankin suna, wani lokaci yankin aikatau. Wannan shi ke nuna irin ta asa ko ta addancin wanda ake yi wa wa ƙ a ya aikata a kuma nuna shi ka ɗ ai ke iya aikata irin wannan aiki domin zarumcinsa da kuma buwayar da ya yi. Saboda haka kalmomin suna da tasiri a fagen nazarin ayyukan masu ta’addanci a Arewa maso Yammacin Nijeriya.

Jagora: Sad da yac ciri yu ƙ a yak kihwa mata,

 Tai wani tsalle tah hwa ɗ i jicce,

 Dan nan wani da ɗ i ya ƙ ƙ ume ni,

 Mun bas su da gawa ɗ anya- ɗ anya,

 Mu ga mu da ku ɗɗ i lahiya lau.

 Gambo Mai Wa ƙ ar Ɓ aray. . Bunza (2014)

Ciri kalma ce tilo, kuma aikatau, ta fi zuwa a yankin aikatau. Yu ƙ a kalma ce kumburau, tana cikin ajin suna. Kalmar ta fi zuwa a ɓ angaren yankin suna a jumla. Kihwa kalma ce tilo, tana ajin aikatau. A ɓ angaren jumla kuwa tana zuwa a yankin aikatau. Idan aka kwatanta da wa ƙ ar Kassu da ke tafe da wannan ɗ an wa ƙ a na Gambo za a ga dukkansu suna ɗ auke da bayanin ta’addanci, domin da wanda ya sa wa gari wuta da ɗ imbin jama’a da niyar ƙ one su, da wanda ya soka wa mace mai tsohon ciki wu ƙ a duk Yan ta adda ne. Saboda haka a ɗ ango na farko, nan ne Gambo ya yi amfani da kalmomin ta’addanci.

Jagora: Anka yi mai bukkar tauri,

 Bai hwasa tahowa ba,

 Su ko ba su hwasa kashi nai ba,

 Shaggun ba su hwasa kashi nai ba,

 Shi ko bai hwasa tahowa ba.

 Kassu Zurmi. Dunfawa (2013)

Kashi kalma ce tilo, tana cikin ajin suna, ta fi zuwa a yankin aikatau a tsarin jumla. A nan, ana nufin bin mutum da duka saboda wani dalili. Kalmar ‘kashi’ a nan ta’addanci ce.

Jagora: Ga ni na ha ɗ a ɓ arna na tumaye,

 Tun da ba da ubana za a yi ba.

 Gambo Mai Wa ƙ ar Ɓ arayi

 

Jagora: Ni dai in wuce gawa ɗ anya- ɗ anya,

 Tun da ba ga jikina za a yi ba.

  Gambo Mai Wa ƙ ar Ɓ arayi. . Bunza (2014)

Ɓ arna kalma ce tilo, tana ajin suna. Kalmar tana zuwa a yankin suna wani lokaci a yankin aikatau. Ɓ arna na nufin fa ɗ a tsakanin dangi. Kalmar gawa kalma ce da ake yi wa ɗ ofane, ɗ anya- ɗ anyakuwa, kalma ce har ɗ a ɗɗ iya, tana cikin ajin amsa-kama. A yankin jumla tana zuwa a yankin aikatau. A nan Gambo ya nuna halin rashin tausayi wanda ke sa ɓ arawo sata har ta kai ga ta’addancin kisa.

3.0 Sakamakon Bincike

A ƙ arshen bincike na ilmi, ya zama tilas a fito da sakamakon da aka gano domin cimma burin bincike ko akasin haka. Saboda haka, a wannan bincike an gano abubuwa kamar haka:

1.      Tabbatar da samuwar kalmomin ta’addanci a wa ƙ o ƙ in baka, wa ɗ anda mawa ƙ a ke rerawa a wa ƙ o ƙ insu na yau da kullum.

2.       Har wa yau, bincike ya gano cewa, samuwar wa ɗ annan kalmomi na da nasaba da irin munanan ayyukan da ake aikatawa ko kuma mugun nufi ga al’umma musamman masu arziki. Daga nan ne mawa ƙ a ke amfani da wannan dama domin harzu ƙ a ɓ arayi su aikata aikin da jama’a suke ƙ yama.

3.      Bincike ya fito da azuzuwan kalmomin ta’addanci da ke cikin baitocin wa ƙ o ƙ in da aka kawo tare da yanayin ƙ iararsu. Haka ma, an kawo wurin da kalmomin suka fi dacewa su zo a tsarin jumlar Hausa.

4.      Bincike ya tabbatar da fa ɗ a ɗ ar harshen Hausa da samuwar sababbin kalmomi da fa ɗ a ɗ a ma’ana a cikin harshen.

4.0. Na ɗ ewa

Mawa ƙ a musamman na baka, suna taka muhimmiyar rawa wajen ha ɓ aka harshen Hausa. Wannan na faruwa ne ta hanyar fito da basira da zala ƙ a da hikimar da Allah ya ba su. Sukan samar da sababbin kalmomi ɗ ori da wa ɗ anda ake da su a cikin rumbun kalmomin harshe. A wannan takarda an fito da kalmomin ta’addanci da mawa ƙ a ke amfani da su a yayin rera wa ƙ o ƙ insu. Bugu da ƙ ari, takarda ta fahimci wa ɗ annan kalmomi suna da tasiri matu ƙ a a ɓ angaren ilmin walwalar harshe ta hanyar fito da ma’anarsu da yanayin ƙ irarsu da kuma ajin nahawun kowace kalma.

Manazarta

Abraham R. C . ( 1947 ) . Dictionary of Hausa Langauge. London: Hodder and Soughton.

Abubakar, A. (2000). An Introductory Hausa Morphology. Maiduguri: University of Maiduguri Press.

Dunfawa, A. A. (2013). Maka ɗ i a Mahangar Manazarta: Jerin Takardun da Aka Gabatar a Taron Ƙ ara wa Juna Sani Kan Tubar Muhammadu Gambo mai Kalangu. Kano: Gidan Dabino Publishers. ISBN:978-8082-02-5

Atuwo, A. A . ( 2009 ). Ta’addanci a Idon Bahaushe: Ya ɗ uwarsa da Tasirinsa a Wasu Ƙ agaggun Rubutattun Labaran Hausa. Kundin Digiri na Uku. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Usmanu Danfodiyo University, Sakkwato.

Bunza, A. M. (2014). In Ba Ka San Gari Ba Saurari Daka: Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambu. Kano: Al’umma Printing Press. ISBN: 978-33308-0-2

Bashir, A. ( 2012 ). ‘ The Morphosyntax of Diminutive in Hausa’. Unpublished B.A. Dissertation, Department of Nigerian Languages and Linguistics, Bayero University Kano .

CNHN, ( 2006 ). Ƙ amushin Hausa Na Jami’ar Bayero Kano. Cibiyar Nazarin Harsunan Nigeria.

Crystal, D. (2008). A Dictionary of Linguistics and Phonetics Seven Edition. U. S. A. Blackwell Puplishing. ISBN: 978-1-405-15296-9

Galadanci, M. K. M. (1976). An Introduction to Hausa Grammar. Zaria: Longman. Nigeria.

Galadanci, M. K. M. da Wasu (1990). Hausa Don Ƙ ananan Makarantun Sakandare 1. Ikeja, Lagos: Longman Nigeria Plc.

Gusau, S. M. (1993). Jagoran Nazarin Wa ƙ ar Baka. Kaduna: FISBAS Media Service Limited.

Kurawa, H. M. da Gummi, M. F. (2022). Gudummuwar Adabin Baka a Farfajiyar Tsaro: Duba Cikin Fasahar Maka ɗ an Bakan Zamfara. Tasambo Journal of Language, Literature and Culture. Volume 1, Issue 1. ISSN: 2757-6730 (Print)ISSN:2782/8182(Online).Pp165/170.DOI:https./dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.01i01.017.

Smith, et, al. (2008). The Language of Violence: Distinguishing Terrorist from Non-terrorist Groups by Thematic Analysis. London: 34-41 Mortimer Street. Routledge Publisher. DOI: 10.1080/17467580802590449

Post a Comment

0 Comments