Neman Aure Acikin Idda

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Slm Allah yatemaki mallam yakara basira. Mace ne tana idda bata gamaba sai Wani yafito neman aurenta bata bashi izinin zuwa ba amma Suna waya Suna chat. Menene hukuncin neman auren da a ka yishi alhali mace tana cikin idda ko kuma a ka daura auren ba ta gama idda ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahamtullahi Wabarkatuh

Shi dai neman aure a cikin idda ɗaya ne daga cikin abubuwa biyu, ko dai mutum ya fito fili ƙarara yayi, kamar yace da mace idan kingama idda ina sonki zan aureki, ko yaje wajen waliyyinta ya gaya masa cewa zai aureta, to wannan kam haramun ne bai halattaba.

Sannan kuma akwai jirwaye me kamar wanka, wato mutum ya nuna alamun yana so amma bai fito fili ƙarara ya bayyana ba, kamar ta ga haka kawai ya aiko mata da wata kyauta mai tsoka, ko kuma yace mata ni kuwa ina son shawara da ke idan kingama idda, da dai sauran makamancin haka, to irin wannan babu laifi ayi, amma da sharadin ya kasance iddar ta ta ba ta kome ba ce. Amma idan iddar ta kome ce to shima bai halattaba, domin idan mace tana cikin iddar kome hukuncinta na matar aure ne kuma baya halatta anemi matar aure alhali da igiyar auren wani akanta.

Danhaka idan Mutum ya nemi auren mace kafin ta gama idda amma ba a kai ga ɗaura musu auren ba sai da bayan ta gama idda to da yawa daga cikin Malamai sukace auren yayi, amma an aikata haramun a wajen neman auren, danhaka wajibi ne su tuba ga Allah() akan wannan laifi da sukayi.

Amma idan ya kasance an ɗaura auren ne kafin mace ta gama idda amma mijin bai kai ga saduwa da ita ba, to dama asali wannan auren ɓatacce ne, danhaka za a raba wannan aurene har sai taje ta ƙarasa wannan iddar ta ta sannan a zo a sake sabon ɗaurin aure, domin ba ya halatta a ɗaura aure acikin idda kuma ko da wacce irin idda ce mace takeyi saboda faɗin Allah()

وَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ فِيمَا عَرَّضْتُم بِهِ مِنْ خِطْبَةِ النِّسَاءِ أَوْ أَكْنَنتُمْ فِي أَنفُسِكُمْ عَلِمَ اللَّهُ أَنَّكُمْ سَتَذْكُرُونَهُنَّ وَلَٰكِن لَّا تُوَاعِدُوهُنَّ سِرًّا إِلَّا أَن تَقُولُوا قَوْلًا مَّعْرُوفًا وَلَا تَعْزِمُوا عُقْدَةَ النِّكَاحِ حَتَّىٰ يَبْلُغَ الْكِتَابُ أَجَلَهُ وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ يَعْلَمُ مَا فِي أَنفُسِكُمْ فَاحْذَرُوهُ وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ غَفُورٌ حَلِيمٌ

Kuma babu laifi a kanku a cikin abin da kuka gitta da shi daga nman auren matako kuwa kuka ɓoye a cikin zukatanku. Allah Ya san cwa lalle ne ku za ku ambata musu (shi). Kuma amma kada ku yi wa jũna alkawari da shi a ɓoye, face dai ku faɗi magana sananniya. Kuma kada ku ƙulla niyyar daurin auren sai littafin (idda) ya kai ga ajalinsa. Kuma ku sani cwa lalle ne Allah Yana sanin abin da yake cikin zukatanku, saboda haka ku ji tsoronsa. Kuma ku sani cewa Allah Mai gafara ne, Mai haƙuri. (Suratul Bakara aya 235)

Amma idan a ka ɗaura aure a cikin idda kuma mijin ya sadu da Matar to bayan an raba auren dole mace za ta yi idda ne har guda biyu. Idda ta farko za ta ƙarasa cikon iddarta ta mijin farko da ya saketa sannan kuma ta sake yin idda ta miji na biyu.

Amma Mazhabin Malikiyya da wani sashe na Mazhabin Hanabila sukace ai har abada babu aure a tsakinsu tunda ya aureta kuma ya sadu da ita cikin idda. Sai dai mafi yawan Malaman Mazhabin Shafi'iyya da Hanafiyya da kuma Hanabila sukace ya halatta ya sake aurenta bayan ta ƙarasa iddar mijin farko kadai, amma Mazhabin Hanabila sukace a'a kafin ya sake aurenta sharaɗi ne sai bayan ta ƙarasa iddar mijinta na farko da kuma iddarsa, amma maganarda mafi yawan Malamai suka rinjayar itace, ya halatta ya sake aurenta bayan ta ƙarasa iddar mijinta na farko, sukace babu buƙatar wai shima sai ta yi masa idda kafin ya sake aurenta.

Sayyadina Umar yana Ganin duk wanda ya Nema aure a cikin idda. Wajibin Shugaba ne yayi Musu Bulalar Gabaki dayansu. Wanda zai Zama Horo a gare su. Sabida Sun Aika ta Abinda shari'a ta yi Ayalka Akai. Sannan wannan Shugaban zai hana su yin wannan Auren. Ma'ana zai Raba Tsananin su.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments