Ticker

Shin Baiko Aure Ne?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam an yi min baiko da wani mutum, to shi ne zai yi tafiya sai ya biyo ta gidanmu wai yana so ya sadu dani, yayi ta kawo min kabli-da-ba'adi, akan cewa, ai mun riga munyi aure, ni dai gaskiya malam na qi yarda saboda ina da shakka akai, shi ne nake neman fatawa ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To 'yar'uwa tabbas akwai malaman da suka yi fatawa a Nigeria cewa: baiko aure ne, saidai zance mafi inganci shi ne baiko ba aure ba ne saboda hujjoji kamar haka

1. Abin da aka sani shi ne kuɗin da ake bayarwa yayin baiko ba'a bada su da nufin sadaki, duk da cewa wasu suna dunqulewa su bayar gaba ɗaya, kin ga kuwa inhaka ne, to ai dukkan ayyukan ba sa ingatuwa sai da niyya, kamar yadda ya zo a hadisni da dukkan malaman hadisi suka rawaito.

2. Bayan an yi baiko mutum zai iya cewa ya fasa, a dawo masa da kuɗinsa, kin ga wannan yana nuna ba aure ba ne.

3. Hakan zai iya buɗe hanyoyin ɓarna, don dukkan wani ashararu zai iya kai kuɗi a yi masa baiko da wacce yake so ya yi lalata da ita, addinin musulunci kuma ya haramta duk abin da yake kaiwa zuwa ɓarna.

4. Yana daga cikin sharuɗan auren a wajan wasu malaman samun shaidu, kin ga kuwa wani lokacin wanda zai kai kuɗin da za a yi baiko, zai iya zama mutum ɗaya, kin ga akwai nakasu ke nan.

5. Abin da muka sani a kasar Hausa, sai bayan an yi baiko, ake sanya ranar ɗaurin aure, kin ga wannann yana nuna cewa, baiko daban, aure daban.

6. Sannan duk mun yarda cewa baiko ba ya wajabta gado tsakanin waɗanda akayiwa, idan ɗaya daga cikinsu ya mutu kin ga wannan yana nuna cewa ba aure ba ne, domin ma'aurata suna gadon junansu.

Allah shi ne mafi sani.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments