Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Yi Bakance, Amma Ta Kasa Cikawa, Yaya Za Ta Yi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam wata mace ce ta yi bakance za ta yi azumin Annabi Dawud, wato yau ta yi azumi gobe ta sha, amma kuma yanzu ta yi aure ta kasa, ya ya kamata ta yi ? shin akwai mafita?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To ɗan'uwa Bakance makaruhi ne, haramun ne a wajan wasu malaman, saboda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yana cewa: "Bakance ba ya zuwa da alkairi" kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1639. Saidai ya wajaba a cika bakance idan aka yi.

Wasu daga cikin malaman hadisi sun ta fi akan cewa idan mutum ya yi bakance ya kasa cikawa zai iya yin kaffarar rantsuwa, saboda hadisin da aka rawaito daga Muslim a lamba ta: 1645 a sahihinsa, wanda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yake cewa: "Kaffarar bakance irin kaffarar rantsuwa ce".

Duba Alminhaaj na Nawawy 4/269

A bisa abin da ya gabata za ki iya yin kaffarar rantsuwa wato: ciyar da miskinai goma, ko tufatar da su, ko kuma 'yanta kuyanga, idan babu hali, sai ayi azumi uku, kamar yadda yazo a suratul Ma'idah aya ta 89 .

لَا يُؤَاخِذُكُمُ اللَّهُ بِاللَّغْوِ فِي أَيْمَانِكُمْ وَلَٰكِن يُؤَاخِذُكُم بِمَا عَقَّدتُّمُ الْأَيْمَانَ فَكَفَّارَتُهُ إِطْعَامُ عَشَرَةِ مَسَاكِينَ مِنْ أَوْسَطِ مَا تُطْعِمُونَ أَهْلِيكُمْ أَوْ كِسْوَتُهُمْ أَوْ تَحْرِيرُ رَقَبَةٍ فَمَن لَّمْ يَجِدْ فَصِيَامُ ثَلَاثَةِ أَيَّامٍ ذَٰلِكَ كَفَّارَةُ أَيْمَانِكُمْ إِذَا حَلَفْتُمْ وَاحْفَظُوا أَيْمَانَكُمْ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ اللَّهُ لَكُمْ آيَاتِهِ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ

Allah ba Ya kama ku saboda yasassa a cikin rantsuwoyinku, kuma amma Yana kama ku da abin da kuka ƙudurta rantsuwoyi (a kansa). To, kaffararsa ita ce ciyar da miskĩni goma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyalanku, ko kuwa tufatar da su, ko kuwa 'yantawar wuya. Sa'an nan wanda bai samu ba, sai azumin kwana uku. wannan ne kaffarar rantsuwoyinku, idan kun rantse. Kuma ku kiyaye rantsuwoyinku. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ayoyinsa, tsammaninku kuna godewa. (Suratul Má'ida aya ta 89)

Allah shi ne mafi sani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments