Tsawon Takaba

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀��𝐀

    As-Salaam Alaikum. Kwanakin takaba wata huɗu ne da kwana goma. To ana nufin kwanaki 90 ke nan, ko kuwa watanni huɗu na miladiyya da kwana 10?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

    Abin da Allaah Ta’aala ya faɗa a kan hakan shi ne

    وَالَّذِينَ يُتَوَفَّوْنَ مِنْكُمْ وَيَذَرُونَ أَزْوَاجًا يَتَرَبَّصْنَ بِأَنْفُسِهِنَّ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَعَشْرًا

    Kuma waɗanda suke mutuwa kuma suke barin matan aure, matan suna haƙurin zama da kawunansu na tsawon watanni huɗu da kwanaki goma. (Surah Al-Baqarah: 234).

    Kuma Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

    « لاَ يَحِلُّ لاِمْرَأَةٍ تُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ أَنْ تُحِدَّ عَلَى مَيِّتٍ فَوْقَ ثَلاَثٍ ، إِلاَّ عَلَى زَوْجٍ ، فَإِنَّهَا تُحِدُّ عَلَيْهِ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَعَشْرًا »

    Bai halatta ga macen da ta yi imani da Allaah da Ranar Lahira ta yi takaba a kan rasuwar wani mamaci ba sama da kwanaki uku. Sai dai a kan mutuwar miji, a nan kam tana yin takaba na tsawon watanni huɗu ne da kwanaki goma. (Sahih Al-Bukhaariy: 1280).

    Daga waɗannan nassoshin da makamantansu muna iya fahimtar cewa

    1. Lissafin kwanakin idda da takaba ana yi ne da lissafin watannin musulunci, kamar dai na watannin kaffarar azumi.

    2. Ba a amfani da lissafin watannin bature, domin a cikin watanin bature akwai mai kwana talatin da ɗaya. Akwai kuma mai kwanaki ashirin da takwas ma a wani karon.

    3. Idan daga farkon wata ne aka fara takabar sai ta lissafa watanni huɗun kawai, ba tare da kallon ko watan ya cika ko bai cika talatin ba.

    4. Idan kuwa daga tsakiyar wata ne ta fara takabar sai ta yi lissafin kwanaki talatin sau huɗu kawai, wato ɗari da ashirin (30x4=120) ke nan.

    5. Sai kuma ta ƙara da kwanaki goma, kamar yadda nassoshin suka ambata. Ya zama kwanaki ɗari da talatin (120+10=130) ke nan daidai.

    6. Sannan tana fara lissafin ne daga ranar da mijin ya rasu ko da kuwa ba ta sani ba, a marinjayiyar magana a wurin malamai.

    7. Ibn Hazm (Rahimahul Laah) shi ne yake ganin mace tana fara idda ko takaba ne daga ranar da labarin sakin aurenta ko mutuwar mijinta ya isa gare ta. (Tamaamul Minnah: 3/227).

    Don haka matar da mijinta ya rasu ran 18/10/2022 ba za ta gama takaba ba sai a ran 26/2/2023, in shaa’al Laah.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

    Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buqatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta wadannan Links...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Fb6qgYPXfEeHb8CD1SWAkK

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄��𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.